← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 93

Sashe 44

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

*BAYAN KWANA BIYU.*

Tun bayan sharuÉ—É—an da Mimi ta saka tsakaninta da Aji ya zama duk ya takura, ya fahimci Mimi so take yi ta maida shi kamar wani sharukhan É—in Kasar India, to da girmansa da komai ace sai ya koma yana soyayya kamar wani yaro? Ya tabbata yanzu matasa na sun daina wannan soyayyar domin duk yaudara ce, masu yin ta ma yanzu mayaudaran sun fi yawa.
Ko bai kirata ba sai ta kira shi ta ce bai turo mata kalaman soyayya ba. Sai ya ce zai tura mata ya rasa shi ina ma zai samu kalaman Soyayya ya manta da wannan tun a zamanin baya.

Dole dai ƙanwar naƙi ya shiga Playstore ya ɗauko Application na lalaman soyayya In hausa da turanci, bai ma tsayawa karantawa da safe sai ya yi mata copying da forwarding ya tura mata haka da rana in ya tuna haka da daddare ma, amman duk da haka sai da ta gane domin ce masa ta yi.
" Kalaman na ka ba emotion a ciki Aji, kamar dai wai da gasken ba ka sona."
Ya rasa da wani yare zai mata wannan bayanin da fahimta ba ruwan ina son ki da wasu kalamai, kawai dai ta ga soyayya aikace ina ruwanta da wani wai sai ya riƙa yi mata kalamai?. Da ya ga ba za ta gane ba sai ya ƙyaleta da ta matsa masa sai ya ce"Mimi ni fa ban iya duk wannan karyan ba, to ƙarya mana soyayya yanzu ai duk ta zama shirme ki buga ma misali da kan mu, ina son ki kina sona muka yi aure amman ki duba yadda matsaloli suka zagayen mu da ya saka sai da kika yi Yaji, to duk ina wannan son da muke ma juna? Zaman aure zaman haƙuri ne kawai da sadaukarwa, ina son ki zan iya zama dake har abada sauyin fuska ko wani nakasu ba za su shafi soyayyata ba ko da Sauyin hallaya ne sai dai zan yi koƙarin cewa ki gyara amman wani ina sonki na yi kewarki duk magana ce ta fatar baki ya kamata ki gane wanman Fatima."

A waya ne ya ke gaya mata haka sai da ta tura masa baki kamar ya na ganinta kafin ta ce" Wai na yi yaji? Haka fa ka ke cewa yaji"
Kai tsaye ya ce" To ba yajin kuke cewa ba? Ko barkonu zan ce."
Haushi ya sa ta kashe wayarta ta barshi ya na ta mirmishi, ya san ba za ta hakura ba da daddare da ya zo kwanciya ya kira ta nan ta É—auka tana ta kumbure kumbure t sai ya nuna kamar bai gane ba sai ya ce"Gobe zan zo taÉ—i me za ki tanadar min?
Ita kuma sai tace"Gobe zan koma aiki."
Ɗan bata rai ya yi kafin ya ce"Tunda ba acan za ki kwana ba da sauƙi, zan zo bayan sallar Isha'i tunda sai na shiga na gaida inna."
Ganin kamar bai gane tana fushi da shi ba ne ya sa ta ce"Ina fushi da kai. Amman sai na ga kamar ka basar ba ka gane ba"
Ya na shafa kasan gemunsa ya ce" Au wai fushi kike yi? To wannan fushin na ki ba na komai ba ne sai na shagwaɓa kuma lallashin ki ai sai ina kusa, ki anada fushin har sai na zo kin ji ko matas?
Har gobe dai Aji ba zai sauya ba in an yi gabas shi sai ya yi yamma. Dole ta saki ranta suka cigaba da waya sai da ta fara hamma sai ya ce ta je ta kwanta saboda fita aiki gobe.

"Sai da safe Mijina, I love u."

Mirmishi ya yi mata kamar ta na ganin shi kafin ya ce"Sai da safe Matas, ki yi shigar nutumci gobe, kada ki manta ke matar aure ce matar auran ma matar Mansoor Aji."
Tana yar dariya ta ce"Yes Sir.."
"I love u."
Haka ya faÉ—a da sauri ta zaro ido kafin ta yi mgana ya yi saurin katse wayar ya barta da shauki. Ranar barcinta cikin natsuwa ta yi shi, har ta na makara sai shi ne ya ta she ta da asuba kamar ya sani ya ce ya ji a jikinsa barci ya kwasheta ta kasa tashi.
A gurguje ta yi sallar asuba da azakar sannan ta yi wanka ta shirya ta yi shigar lafaya ta yi kyau sosai tunda daman can ita mai kyau ce.

Motar ta tun shekaranjiya ta kira Bakanikenta ya zo ya tafi da ita da yake ta daÉ—e ba ta yi amfani da motar ta, ya yi ma ta juye da service sannan jiya ya dawo mata da shi tana so ma ta sauya mota da kuÉ—in gadon ta, amman kuma ba ta so Aji ya ga kamar ta na nuna masa kuÉ—i amman tuni Khadi ta sauya ta ta motar. Sannan an riga an gama ginin masallatan nan da bohol É—in ruwa a wasu anguwannin dake cikin garin kano sai dai fatan Allah ya kai ladan Kabarin Abi, bayan ta shirya ta É—auki kanta hoto ta tura ma Aji sannan ta fita zuwa É—akin Hajiya su ka gaisa Hajiya ta ga sai faman nishaÉ—i take yi cikin zolaya ta ce"Binta dai za'ayi kome ko? Daman ance kome ai ya fi sabon aure daÉ—i ko?

Mimi ta rufe fuska tana dariya kafin ta ce"Kai Hajiya ta"
Hajiya na Æ´ar dariya ta ce"Ai na gano ki, tunda Mansoor ya zo ranar nan kike cikin nishaÉ—i, to gaya min yaushe ne komen na mu.?
Mimi ta zauna kusa da ita lokaci É—aya tana sagala hannunta saman KafaÉ—an Hajiya tana faÉ—in" Saboda ginin da za'ayi ya ce sai bayan sallah lokacin duk na gama sauran shirye shiryena."
Hajiya na Mirmishi ta ce"Ya yi kyau, To gidan shi da aka ce ya gina fa?
Mimi ta ce"Ban gaya miki ba? Ai Inna Meri ta koma gidan da zama"
Nan Mimi ta ba ta labarin da Hibba ta gaya mata ta ƙara da cewa" To shi ne ya ce yana da fili gwara a gina kawai."
Hajiya ta jinjina kai kafin ta ce"Ma sha Allah, na ji daÉ—in haka Allah ya sa albarka, ke kuma da ku ke mganar tsayawa wasu shirye shiryr? Me za ki shirya? Na ga dai komai kina da shi?
Mimi ta mike tana dariya kafin ta ce"Ke fa kika ce kome ya fi sabon aure daÉ—i ko?
To ai sabon biki zan yi da zai tabbatar da Komen da zan yi ya fi sabon aurana na farko."
Kafin Hajiya ta samu bakin mgana Mimi ta fice da sauri tana faÉ—in" Sai na dawo Hajiya za mu yi mgana."
Hajiya ta bi ta da Allah ya tsare tana Cigaba da jan casbahanta lokaci É—aya tana wani mirmishin jin daÉ—i. Farincikinta ta ga Binta ta koma É—akinta ta yi zamanta cikin Salama.

****

KARAMCHI TV

Ma'aikatan Karamchi kowa ya yi murna da dawowar Mimi, bakinta ita kuma ya ƙi rufuwa sai gaisawa take yi da mutanen arziƙi, wani farinciki na ratsata sun gaisa da Salim Bunza ya na zolayanta da cewa"Tunda kin dawo nima ya kamata na ɗauki hutuna nima."
Cikin Magiya ta ce"Ka rufamin asiri mana Bunza, in ka tafi yanzu ai sai aiki ya nemi kashe ma mijina mata."
Sai kawai ya yi mata dariya Na Misau na gefe ya ce" ƙila ma sai ya haɗa mana da zanga zanga."
Suna ta raha da nishaÉ—i. Ta je Office É—in Manaja suka gaisa shima sai da ya yi mata tsiya" Na É—auka wannan rigimammen mijin naki ya hana ki dawowa aiki damu ne gabaÉ—aya.?
Mimi na dariya ta ce"Ko ɗaya yallaɓai kawai dai ba na gari ne har Umra na je na dawo kuma matar Yayana ta haihu na tsaya sai da aka yi suna na dawo, nan ɗin sai da na zauna na huta tukunna."
Ya na jinjina kai ya ce"To ai shinke nan muna yi miki barka da dawowa."
Daga nan suka tattauna abin da ya shafi aiki kafin ta haɗu da editor ita ta karanta labaran safe na ranar oaraba. Jama'ar gari na ta nurnan ganinta domin wasu har sun gaji da tambayan Ina Mimi take a tunaninsu ta daina aiki da gidan talabijin na karamci ne ne sai kuma kwatsan a ka ganta ta yi kiba ta yi bul ɓul, kamar ba ita ba har wasu ma su kallon tashar suka ce kamar tana da shigar ƴaron ciki.

A cikin waɗanda suka kalli labaranta na safiyar ranar har da Inna Meri da Walida da kuma Maeesha dake can gidansu tana jego, Tuni ta ji kishi ya kama tana ganin Mimi, ta tabbatar da kome za ta yi ba za ta kama kafar ta ba. Sannan ta ji a bakin matar Auwalu cewa ba sakinta ya yi ba, kenan auran su na nan za ta iya dawowa a kowani lokaci kila ma a katon gida na alfarma kamar yadda Inna ta koma katon gida na alfarma duk da ba ta je gidan ba amman ta ji labarin tsaruwan gidan a bakin Mariya ta kuma ji labarim komai sabo ne, ita a ganinta ita ya dace ta riƙa samun wannan abubuwan ba wasu ba. Sannan ita ya kamata ta zama a bar kwaten ce ba wata can ba.
Chapter 44 · 0% Book details