Sashe 18
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Maeesha ta faɗa cikin hargowa shi ko kamar bai ji ta ba ya shige ɗakin Inna wacce ke salla ta kosa ta Idar kada Baban inna ya ƙara jawo mata wata masifar, Maeesha bakin ciki ya rufe ta sai kawai ta saka kuka tana faɗin an takura mata ita da gidan Mijinta ba ta da halin sararawa Walida na gefe tana yar eariya daman matar nan ta gama cika mata ciki da iskancin ta a cikin gidan nan saboda ita Bintu ta daina zuwa gidan in ta ga abun magana sai ta yi mgana Kuma tana mgana sai a fara hayaniya Ita kuma Inna yar zaman Lafiya ce ita ta ce in fitina ke kawo ta itama ta zauni gidanta.
Maeesha ta yi ta kumfar baki tana tunanin Magajiya za ta fito amman shuru ita kuma Walida sai ta tafa hannu kafin ta ce"Sorry fa, ko shi Yaya Saddiqun ba zai iya da Yayanmu ba ballantana ke karamar alhaki."
Da haka itama ta nufeta gadan gadan kamar za ta murje mata hannu ya sa da sauri ta mike tsaye Walida ta shige É—akin Inna tana faÉ—in" Ashe karyan tsiya kike yi."
Fuu Maeesha ta koma É—aki tana kuka ta kira Saddiqu tana gaya masa karya da gaskiya har ta na faÉ—in Aji ya saka yakalmi ya taka ta kuma da gangan.
Shi kuma cikin Kumfar baki ya ce mata ai ya Kusa dawowa zai yi sharia da wanda ya taɓa masa mata daman ai ya na jin hauahin warning ɗin da ya saka Auwalu ya kira shi ya yi masa to wai shi da me ya ke takama ne?
A ɗakin Inna ko ta na sallame sallah cikin ɓacin rai ta kalli Mansoor kafin ta ce"Ba na son fitina. Ba na so ina zaune lafiya ba za ka jawomin wata fitinar ba, in kai ba ka san darajan matar ka ba, wasu sun sani kuma da gaskiyanta gidan mijinta ne a barta ta yi abin da ta ga dama mana."
Lokacin ya na wasa da Junoir ne wanda tun shogiwarsa a she bai yi barci ba ya naÉ—e masa. Sai ya kasa mgana domin kamar gori ne Inna ta yi masa.
Walida ce ta tura baki kafin ta ce"Shikenan Inna sai a barta ta rika mana abin da ta ga dama."
A fusace Inna ta ce"Sai me? Ai wuri ta samu É—an da ka haifa ma bai ji mganarka ba sai wani can ne za ka damu kanka domin ka yi masa mgana bai ji ba."
Yadda Inna Meri ke mgana ne ya sa ya san ranta ya ɓaci kai tsaye ya ce"Ki yi hakuri inna." Sai kawai ya miƙe ya na faɗin"Inna ki ba ni Junior na tafi da shi wajena ya kwana."
Wani kallo mai kama da harara Inna ta sakar masa kafin ta kalli Walida lokaci ɗaya tana faɗin"Ke karɓe shi, "
Walida ta yi shuru kafin ta karisa za ta karɓeshi shi kuma ya makale masa sai ta Juya tana faɗin" Inna ko za ki bari ya tafi da shi ne, duba fa ki gani baya son zuwa."
Inna ba ta sake mgana ba ta miƙe ta warce Junoir a hannun Babban Inna yaron ko ya fashe da kuka Inna ta mikama Walida shi tana faɗin ta kai shi ciki ya kwanta.
Ta kalli Manaoor da ya yi kasaƙe kawai yana na kallon Inna komawa ta yi ta zauna lokaci ɗaya tana faɗin" Mu kwana lafiya."
Takaici ya kume shi cikin É—an jin haushi ya ce"Inna É—an ÆŠan uwane fa?
Inna kai tsaye ta ce"E fa! Amman ai ba É—anka ba ne ko ? In ka ji haushi ka haifi naka sai ka rika kwana da su."
Har ya dawo gidansa in ya tuna kalaman Inna sai ya ji kamar ya yi kuka wai shi Inna ke yi ma gorin Mata da haihuwa, takaici ya sa a daran ya Kira Mu'azzam y na gayamasa shi kuma ya nuna bai ji daÉ—i ba.
Sai kawai Aji ya ce" Amman ba komai, ta kwantar da hankalinta sai ta gaji da ɗaukan Ƴaƴa na"
Mu'azzan sai ya ji ya ba shi tausayi ya kuma san Inna ta yi masa hakane Saboda ya ji haushi ya gyara abin da ya ɓata kuma kamar hakan ya yi tasiri daga baya shima ya zauna yana tunanin shekaru sun tura ya kamata ace shima yanzu ya wuce wannan matsayin tunda har Inna ta fara masa gorin mata da haihuwa to nan gaba bai kuma san wa zai masa gori ba, ya fi su fa bukatar matarsa akwai abubuwan da suka faru ne suke danne wannan bukatar ta shi amman cikin ikon Allah da shawarwarin Nasir tun kwanaki ya fara yaƙi da abin d ke ransa kuma Alhandulillah yana jin abun na raguwa.
Duk iya yadda ya so ya share Mimi sai ta neme shi amman ba ta neme shi ba Sai ya ji ya kasa hakuri ana neman cin wajen wata ɗaya sai ya fara jin tsoro kada fa ya yi sakacin da zai ƙara jefa rayuwarsa cikin yarari a karo na biyu.
Ba shi da wani abokin shawara sai Mu'azzam Shi ya kira ya na ce masa" Mu'azzam kana ganin na bi Mimi Abuja ba matsala.?
Mu'azzam na mirmishi ya ce"Me zai hana? Ba wata matsala, ka kirata in ba ta É—auka ba ka tura mata sakon za ka zo sai ku zauna ku yi mgana." Kamar wani yaro sai ya ce ma Mu'azzam Toh, Sai yayan na shi ya ba shi tausayi yasan yadda ya tsani garin nan amman ga shi yau zai koma kuma a kan dalilan nan guda É—aya wanda saboda shi ya je a karon farko a wannan karon ma saboda shi zai koma.
"Don Allah Yaya Mansoor kada ka ce za ka mata yi faɗa, ka lallasheta tunda dai kai ne mai laifi."
"Uhm!
Kawai ya ce daga nan bai ƙara mgana ba Saboda a lokacin yana tunanin ya je ko kuma kar ya je, amman ya bi shawaran Mu'azzam ya ƙara Sauke kai ya kira Mimi amman matar nan ba ta ɗauka ba sai ya tura mata sakon ta tura mishi adireshin gidansu zai zo su yi mgana.
Lokacin da ta ga sakon shi matuka ta sha mamaki, wani gidan y ke nufi? gidan da ya ce Allah ya yi masa tsari ya ƙara takawa, ba ta yi gaggawan tura masa sai da ta kira Rukky ta sanar da ita, ita kuma tana dariya ta ce" Na fahimci ba ma zai yi mana wahalan kamuwa ba, tura masa kada ki sake ki gaya masa wani abu."
Kai tsayen ta tura mishi yadda zai gane, An yi wajen kwana biyu ba ta kara ji daga gare shi har Rukky ta kira ta na gayamata ta ji Aji shuru Rukky ta ce zai zo fa ki kwantar da hankalin ki, shi ko tunanin tafiyar ne amman haka nan dai ya sauke girman kansa da wannan rikon da ya yi a ranshi a ransa ya kudurta ba zai shiga gidan ba sai dai ya tsaya daga haraba..
Bayan Mu'azzam ba wanda yasan zai je Abuja Jirgi ya bi zuwa can ranar wata Asabar da safe domin ko da sha É—aya ta yi sun sauka a garin Abuja, a direshin ya nuna ma mai Taxi É—in sai ga su har kofar gidan Marigayi Major Kabir Dabo dake anguwan Gwamrinpa.
Tsawon shekaru goma anguwar ba ta sauya masa a i do ba. Sannan gidan kan shi bai sauya masa, sama da mintina talatin ya na bakin get ɗin gidan yana kokuwa da yanayinsa domin ji ya ke kamar a wancan lokacin ne da suka sauka shi da Mu'azzam kawai sai komai yake dawo masa daki daki kamar a lokacin yake faruwa ya yi tunanin ba zai shiga gidan ba, in fa ana son a samu masalaha har gobe ba zai daina ganin baƙin wannan gidan da mutanen dake cikin sa ba.
Wayarsa ya É—auka ya kira Mimi abin mamaki wannan karon Mimi ta É—aga wayarsa.
"Hello, na iso gani a kofar gida amman ki fito ba zan shigo ba."
Cikin yanayin maganarta tacce"Ni kuma ba zan iya fitowa ba, in ka na so in saurare ka sai ka shigo cikin gida."
A ransa sai ya ji daÉ—i da ya ji muryanta amman kuma yana tsoron wani abu da sauri ya ce" Kada ki sake ki shirya wani abu, domin na ga alaman kin sakani cikin dangin ku bangaren abokan wasan ki."
Dariya ta saki mai kayatarwa kafin ta ce"Kar ka damu, yi ma megadi mgana ka ce kai baƙo na ne."
Daga haka ta katse wayar ba karamin jarumta ya yi ba. Har sai da ya kai zuciyarsa nesa sannan ya iya tun karan get É—in ya buga megadi ya leko sai ya ga yau kam ba Soja, wani dattaijo ya gani bayan sun gaisa ya ce masa ya zo wajen Mimi ne sai ya buÉ—e masa kofa ya shiga amman sai ya ce ya jirasa bari ya shiga ya sanar musu.