Sashe 71
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Rukayya mamaki ya kamata sai kawai ta ɗaga waya ta kira Jaheed tana gaya masa abin da ya faru da kuma tambayan ko wani abu ya faru ne jiya? Bai gaya mata sai kawai ya ce"Ban sani ba, a waje na sauketa jiya nan." Da sauri Rukky tace"An ya? Ina zargin da wani abu. Mimi ba ta kwana a gida ba, Bari na sake kiranta."
Da sauri ya ce" A'a Ruƙayya kyaleta. Shi aure daman ya gaji haka tunda ba ta faɗa miki ba to ba ta son ki sani ne, ki yi musu addu'an Allah ya daidaita su kawai."
Shi ya hana Rukky sake kiran Mimi amman abun ya dameta tana tunanin me ne ya faru haka,? Jaheed kuma bai ba ta damar da za ta gane ya san wani abu ba, yana ma faɗa mata Jirgin karfe uku zai bi zuwa lagos su haɗu a asibitin da a ka yi ma ƙanwarta aiki su yi sallama.
 Shi kuma Aji daga ma'aikan su Mimi bulayi ya fara yi a gari duk in da ya yi tunanin Mimi na can ba ta je ba, to ta na ina? Ko dai tana gidan Bintu ne? Ya kira wayar Bintu ta ɗauka suka gaisa sai ya ji hayaniya sai yake tambayanta ta na ina ne? Sai ta ce masa tana gidan su Bashir Hajiyarsa ba lafiya tunda ya ji haka ya san ba ta je bam Bayan Bintu har su Yaya Amina ya kira nan ma shuru suna ta tunanin yau Aji na jin zumunci duk ya kira su sun gaisa bai taɓa kawo tunanin tana wajen Inna ba ganin ba shi da mafita ne ya sa ya yanke shawaran zuwa gaban Inna ya faɗi ya gaya mata duk abin da ya aikata ta taimake shi kada ya rasa Mimi in ya rasa ta ya shiga uku.
Yana tafe a Mota kamar mara lafiya duk ya faÉ—a saboda bai ci komai ba tun jiya da rana.
 A kofar gida ya bar motar, ya shiga gidan shima yana layi kamar zai faɗi, a tsakar gida ya ga Inna ta na shanya zogalanta ya yi sallama ta amsa masa a ciki ko kallonsa ba ta yi ba, tun bayan kallo ɗayan da ta yi masa bayan ya shigo ba ta kara ba.
"Ina kwana Inna.."
 Haka ya faɗa yana kokarin zama kan damdalin ƙofar ɗakin, kamar ba ta jisa ba haka ta yi masa banza sai ya ƙara gaisheta sai ya ga kamar ma ba ta san yana wajen ba Da ace ba ta amsa sallar masa ba sai ya ce ba ta san da zuwan sa ba, amman ta amsa kuma ta kallesa, tabbas wani abu na faruwa, Kafin ma ya samu bakin ƙara mgana ya ga Inna Meri ta wuce su zuwa cikin falon ta barsa nan kamar ma ba ta gansa ba, baki sake ya bi ta da kallo kafin a ranshi ya ce" Me kuma na yi?
Ko dai Mimin nan ta zo? tuna haka ya sa dai gabansa ya faɗi da sauri ya tashi ya bi Inna cikin falon lokaci ɗaya yana faɗin" Inna wai baki..."
 Sauran mganar ta sa ta maƙale ne a fatar bakinsa, ganin Mimi zaune a saman kujeran falon inna, sun kuma haɗa ido ta ganshi ya ganta, kafin ma ya samu zarafin mgana Inna Meri da ta fito daga kitchen ta kalleta lokaci ɗaya tana faɗin" Binta shiga ciki."
Ba musu Mimi ta mike tana tafiya a sannu sannu ta shige É—akin Walida ta rufo kofa.
Amman an ce tsakanin miji da mata sai Allah sai ta tsaya jikin kofar kawai har ga Allah ta ji tausayinsa ganin rana É—aya duk ya faÉ—a, jikinta a sanyaye ta karisa gefen gado ta zauna ta yi tagumi.
Inna Meri kuma Mimi na shiga ciki ta koma saman kujera ta zauna har t na jawo Radionta tana kunnawa kamar ma ba ta san da wanzuwarsa a falon ba.
 Ƙafafunsa suka yi sanyin da suka kasa ɗaukansa ba shi da mafita Inna ba za ta saurareshi ba. Gwara ya bi ta hanyar Mimin kila ya samu ragowa tunda ta na son sh. Salau salau haka ya wuce zai nufi hanyar ɗakin da Mimi ta shiga. Cikin mamakin rashin kunyar sa Inna ta bi sa da kallo,gani ta yi zai shiga tana zaune bai ji kunya ba.
Sai kawai ta juya tana faÉ—in" Kai.."
Haka ta faÉ—a sai ya juyo yana kallon Inna cikin rashin madafa
 Inna ta nuna masa hannu kafin ta ce" Ina kuma za ka je?
Haka ta faɗa tana hararanshi kansa a ƙasa ya ce" Zan zan je wajen Mimi ne Inna."
Wani sakaran kallo Inna ta yi masa kafin ta ce"To mara kunya, sai yanzu ka san da ita ? Ba cewa ka yi ta bar maka gidanka tun da tana cin amanar ka ba miye za ka zo kana wani sanyin jiki? Fita ka ba ni waje kafin na tashi na yi maka dukan mahaukaciya wlh."
Ido ya zaro ya na kallon Inna, wai ta yi masa dukan nahaukaciya. Ganin yadda ranta ya baci yasa jiki ba kwari ya yi kamar zai bar falon sai kuma ya dawo ya duka a gabanta muryansa na rawa ya ce"Don Allah Inma ki yi hakuri wlh sharrin sheÉ—an ne."
Banza Inna ta yi masa har tana ƙara volume ɗin radion ta, tana jin sa yana ta ban hakuri yana ta kuma faɗin sharrin sheɗan ne.
 Haushi ya kamata kamar ta watsa masa mari, ba ta san lokacin da ta kashe radion hannunta ba a fusace ta ce"Rufe min baki, in ƙara jin kace sharrin sheɗan ne ka ga ni in ban watsa maka marin ɓarin makauniya ba." Haka ta faɗa ta na hararanshi. Kallon Inna ya yi cikin mamaki kafin ya ce"Inna kin ce za ki dakeni yanzu kuma kin ce za ki mareni? Baban inna ne fa?
Inna ta ce"Eh Mansoor ba ɗan ibrahim na gane ka, ka wuce dukan ne? Ka ƙara cewa sharrin sheɗan ne ka gani in ba wanke fuskar ka da mari ba."
Sai Aji ya yi gum kansa na ƙasa. Domin ya san in kuma ya sske ya sake mgama tabbas Inna za ta iya wanke sa da mari.
"Ki yi hakuri inna, na tuba.."
 Haka ya ke ta faɗa, Inna sai da ta ga dama sannan ta kalleshi kafin ta ce"Sheɗan din ne ya sake ka da sauri haka? Ƙaryan banza Ka raina ma kanka wayau, waye sheɗan din in ba kai ba, in ba sheɗan ba waye zai aikata abin da ka aikata, kana zargin matar auran ka Mansoor? Kai kam wani irin jaki ne?
Baki ya buÉ—e yana maimaita kalmar jaki a ransa a she a fili ne a fusace Inna Meri ta ce"Eh mana jaki mana, wani mutum ne mai tunani zai aikata abin da ka aikata? Ka kore ta ba ka tsaya ka ji bayanin ta ba. Yanzu da ta je wajen iyayenta ta sanar da su fa? Wallahi da sun daina ganin ka da daraja, sai ta yi wayon zuwa wajena ni kuma wlh zan bi mata kadin abib da ka yi mata ne. Tun da har kana zarginta ya tabbata auran ku ba zai zauna lafiya ba gwara ka sake ta na maida ta hannun Iyayenta ka fin ka aikata abin da za ka hanani shiga mutane."
 Haka ta faɗa tana kallonsa cikin ɓacin rai. Cikin zaro ido ya ce"Saki kuma Inna?
"Eh haka na ce"
Ta faÉ—a tana haÉ—e rai. Sai kawai ya yi zaman dirshan gaban Inna lokaci É—aya yana faÉ—In" Ki yi min rai Inna don girman Allah ki yi hakuri."
"Rai ai na Ubangiji ne, ba ka yi tunanin haka za ta faru ba ka aikata abin da ka aikata?
Da sauri ya ce"Inna kishi ne, kinsan ina da kishi, kuma ina takiran wayarta ba ta ɗauka ba sannan na ga sun dawo tare ya na riƙe da ita, kuma Inna tsohon saurayinta ne fa me kike tunani?
Inna tac e"Ba komai sai alheri, zuciyarka ce ba ta da kyau kishi halas ne ga matar ka amman naka ya yi yawa ya zama na jahilci da daƙikanci tunda kake zargin matarka da cin Amanarka? Kai ba ka da lura ne? Ina tunaninka yake? Na sha gaya maka in ka ciza ka hura Mansoor, in rai ya ɓaci hankali ke nemosa. Hadisi ne fa Annabi(SAW) yace ma wani sahabinsa Kada ya yi fushi har sau uku sannan a matsayin ka na musulmi mumini in ranka ya baci sai ka lallashi zuciyarka ka yi hakuri ka jira in ka huce sai ka yanke hukunci amman yanke hukunci cikin fushin shi ke haifar da dana sani Mansoor."
 Duk abin sa Inna ta faɗa gaskiya ne, Kai tsaye ya ce"Inna sheɗan ne, amman wallahi gar ga Allah ba na zargin Mimi ki yi hakuri."
A kufule Inna ta ce"In sheɗan ne me ya sa ba za ka nemi tsari da shi ba? In ka ji zuciyarka na zafi ka kira sunan Allah mana ka nemi tsari daga sharrin sheɗan din mana ka gani in abubuwa ba su yi maka sauki ba."
Shi dai sai hakuri ya ke ba ta amman Inna ta fusata ta ce tunda yana zarginta shike nan ya ba ta takardan sakin Binta ta fahimci bai san darajan mace ba.
Daga karshe ma banza da shi ta yi yana mgana shi kaɗai, ta shi ma ta yi ta shigewarta ɗaki, sai kuma ta dawo falon kada barinta falon ya sa ya shiga wajen Binta so take yi sai ya gane kuranshi wanda nan gaba ba zai ƙara gigin aikata haka ba..
Yana zaune in da ta barshi sai ta shige Kitchen ta barsa gajiya ya yi da zaman ya É—auko wayarsa ya kira Mu'azzam kamar an saka masa batir ya shiga gaya masa duk abin da ya faru.
Mu'azzam ya saka salati ya saukewa kafin ya ce"Haba Yaya Mansoor me ya sa ka yi haka? Gaskiya ba ka kyauta ba."
Shi dai Mansoor faÉ—i ya ke yi Mu'azzam ya taimaka masa ya kira Inna ya ba ta hakuri sai ya ce bari ya kirata.