Sashe 62
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
 Yinin ranar yana gida bai fita ko'ina ba sai dai waya kawai.Sai bayan mangariba ya fita ya je gidan Inna suka gaisa, ta yi masa mganar zuwa Kwami nan ya ke gaya mata cewa sai dai bayan sallah tafiya Abuja ta kama shi daman kuma ya yi ma Mimi alƙwari za su tafi tare ita sai ta sauka a gida Inna tace hakan ma ba laifi, yana gida har a ka yi sallar isha'i kuma sai da ya ci yuwo da miyar kuɓewa, da su ka yi waya da Mimi ya gaya mata ga shi ya na cin tuwo sai ta ce itama don Allah ya ce ma Inna za ta ci, kai tsaye ya ce"Ni ɗan aiken ki ne? Ba zan iya daukan tuwo ba."
Ta san halin shi ya sa ta kira wayar Inna ta gaya mata tana son tuwo nan da nan inna ta ce a saka mata a Kula Baban Inna ya wuce mata da shi, ya na zaune kai tsaye ya ce"Ni kuma Inna? Daga nan ba gida zan je ba fa."
Inna ta harareshi kafin ta ce"Ko ba gida za ka je ba sai ka É—auka ba na son iyayin banza."
Shuru ya yi bai kara mgana ba har Walida ta zubo tuwo da miya a kula sai yake mata mganar yaushe za ta gama Traning É—in ta?
Kai tsaye ta ce"Wata mai kamawa yayanmu., Amman mai shagon ya ce zai rikeni na riƙa zama masa kafin lokacin zana jamb ɗin ya yi." Da sauri ya ce"A'a ba za ki zauna ba, ki dawo gida ki cigaba da taya Inna zama."
Inna ba ta yi mgana ba daman itama tunda ta gaya mata ta ce ba ta amince kuma daman tasan shima Baban inna bazai amince ba.
Inna ce ta ga Walidan ta ɓata rai sai ta ce"Nima na ce mata ta yi hakuri ita mace ce, ko wannan ɗin ma da ta yi saboda Kun matsa ne. Ni da har shawaran ta fara zuwa can anguwan da muka taso wajen Bahijja yar wajen Dije ta fara koyon ɗinki kada ta yi ta zama ba ta wani abun."
 Mansoor ya mike lokaci ɗaya yana faɗin" To gwara ma can ɗin, ki yi mata mgana Inna abin da a ke bukata sai a sanar da ni."
Shike nan ma har ya zartar da Hukunci Dole Walida ta yi shuru, amman ita har ga Allah ba ta son koyon É—inki yana da wahala, Inna kuma Daman shawara ce nata abin da Baban Inna ya ce shike nan ballantana Baba da duk abin da ya zartar sai ya ce mata ya yi, gwara Mariya auranta za ta yi, itama ta na da samarim amman kuma tunda ta ce karatu za ta yi ba ta da ikon sauya wata mgana daga baya.
Tana ji ta na gani Baban Inna ya bar gida bayan inna ta ce za ta kira Dijen su yi mgana ko ita Walidan ta je ta samu Bahijja su yi mgana.
 Abu kamar wasa ƙaramar mgana ta zama Baba Inna ta kira Dije ta ce ai bakomai an zama ɗaya, ta ce Walida ta fara zuwa gidan Bahijja ita a Tunferre take zaune kuma babbar Tela ce gidanta cike da yaran mata har da matan aure ma ba'a bar su a baya ba, Walida ba ta da ra'ayi amman tunda mai gayya mai aiki ya zartar shikenan
Kuma duk abin da ake bukata Aji ya ba ma walida kuɗi ta siya, kenan ba ta da iko da ta ce ba za ta je ba, an gama mgana da cewa da zaran an yayeta a computer Traning za ta fara zuwa, da ta gayama mariya abin da Yaya Mansoor ya ce itama ta ce ta na so za ta yi kafin auran ta ya zo, tunda wani Lokacin Walida na biyawa ta gidan Magajiya ta yi laushi kamar ba ita ba wani ookacin har cewa ta ke yi, Walida ta gai da Inna amman kunya ya hana ta zuwa gidan innar da kanta.
 Mariya Auwalu ta yi ma mganar itama tana son koyon ɗinki tunda ga Walida ma za ta fara zuwa da ta ce za ta yi ma Yaya Mu'azzam magana sai ya ce ta bari shi zai ba ta kuɗin abin da za ta bukata, ba zai zama lalle sai komai Mu'azzam ko Mansoor sun yi musu ba, suma ya kamata su riƙa taimakawa da wani abun, Saddiqu dai lagos ɗin ta gagare shi ya koma yana zaman shago, gida duk ya lalace ga dai ɗakin nan Inna ta bar musu amman ba kowa ciki sai tara tarkace Maeesha ke yi, can ma bangaren da Maeeshan ta tashi shima Mariya ce ke tara tarkacenta a ciki, tabbas dai Inna ita ce gida ko shiga da fitan jama'a babu kamar baya.
Shi kuma Baba tunda bayan abin da ya fqru ya daina ɓata bakin shi, ya bar Magajiya da Ƴaƴanta duniya ta koya musu hankali daman an ce indan an ciza a hura Saboda gudun ranar nadama kuma ga dukkan alamu nadamar ta fara shigar su.
*****
 Ana sallah saura kwana shidda Mimi da Aji suka tafi a Abuja jirgi suka bi, ana gobe taron da Mansoor zai hallata. Har gida ya rakani Mimi sai da Mommy ma ta saka baki ya tsaya ya sauka nan ya yi sallah ya ci abimci kwana kuma ya ce ba zai kwana ba, Mimi ta san halin yan kayanta shi ya sa ba ta matsa masa ba, hotel ya kama ya kwana washegari kuma a ka yi taron a Eagless Squeare, An san da zuwan shi tunda ya na wakiltan Gombe United ne ya haɗu da shugabbanin Kungiyoyin kwallon kafa ta jihohin Nageria waɗanda ya sani, da ma waɗanda ma bai sani ba su sun san shi, ya haɗu da su Ahmad Musa shima sun gaisa sannan ya nuna masa sani da cewa yana kallon wassanin shi sannan hatta shuggaban Super Eegless ɗin sun yi mgana da Aji abin da bai sani ba Coach ɗin su ya daɗe yana kai mganarsa sama tare da video ɗin wasannin Aji fatan sa kafin Contart ɗin sa ya ƙare Allah ya ɗaga sa zuwa sama amman baya taɓa bari Ajin ya sani tunda yasan in ya sani zai ce shi baya bukata.
 Kwana biyu a ka yi ana taron na ƙara ma juna sani ne kan abib da ya shafi ƙwallon Kafa ne, bai ƙara neman Mimi ba sai da suka gama taron gabaɗaya sannan ya memeta. Ranar da ya je gidan sun daɗe suna hira nan ya yi sallar mangariba da isha'i ya ci na rana da sare sai dare ya tafi washegari Mimi ta matsa masa sai da suka fita zaga gari, su ne wajajen shakatawa da kuma wajajen siyan kayan ƙwalama sun yi hotuna da Vedio sai dare ya maida ta gida. Washegari suka juya Gombe,sun koma saboda sallah saura kwana biyu ne. Tun yana Abujan sun yi mgana kan ragunan layya da zai siya. Daman duk salla Aji ke yi ma Inna layya Mu'azzam kuma sai ya yi ma Baba.
 Akwai daman wani anan anguwansu mai safaran Rlraguna daga taraba daman wajensa suke siya, Mu'azzam ya turo kuɗin raguna biyu ya ce ɗaya na Baba ɗaya kuma Baba Sani tunda shi ne Babba in kuma shi ya yi layya naman gida biyu za'a raba Baba Danlami ya ja na shi, shi kuma sai ya siya guda biyu na shi ɗaya na Inna guda ɗaya, Mimi ma za ta yi amman ita Daddy ne yake siya mata ita da Hajiya.
Ana gobe sallah a ka raba ma kowa ragon shi su Baba Sani suna ta godiya, Auwalu kuma ya siya ma Magajiya É—an bunsuru ya ce ta yanka ta yi ta murna tana saka masa albarka, abin da ba ta yi a baya amman yanzu ta fahimci yadda duniya take.
Ana goben sallah a daran sai ga wata ɗiyar kanin Maman inna, suna matsayin yar mace da yar namiji ne, amman ubansu ɗaya ne da babanta. Lokacin da suka rasa mahaifinsu mahaifiyarsu ta kwashe yayanta sai bayan sun girma me suka nemi dangi, kuma shima ba'a nan sokoto ya ke zaune ba ya na tureta ne cikin garin Sokoto, Ita ce ta sauka a gidan wanzamai tunda wayar Baba Ɗanjuma ta kira.
 An faɗa mata tana da wata uwa a garin Gombe shi Baban nata dake kwance ya na jinya ya ba ta lambar Baba Ɗanjuma da ita kaɗai gare shi ba shi da lambar Inna. Da ta fara biyawa ta can babban gidansu na Argugun ne ta samu tabbacin Inna Meri na aure a garim Gombe ne duk da ta kwana biyu ba ta je ba, shi ne ta shirya ta zo gombe sai ga ta a gidan Wamzamai ta sauka ɗakin Magajiya.
Inna ta san Tanimu ne kaɗai ya rage mata acikin ƴan'uwanta duk sauran sun rasu amman shi ba shi da zumumci sau ɗaya ta taɓa zuwa cqn Tureta, ko argungun sai ya fi shekara goma bai je ba.shi ya sa itama ta manta da shi kawai. Ta san yana da ƴaƴa amman ba za ta san su da adadin su ba..