Sashe 24
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A lokacin da saƙonta ya shigo kamar tasan yana kwance ne yana kisima hukuncin da zai yanke Mata in ta bari suka haɗu, tsabar ma takaici ko abinci bai ci a daran kuma in ya je gidan Inna ba bashi za ta yi ba domin tun bayan barin Mimi gidan inna ta daina masa tayin abincin ko ya ce zai ci sai ta ce ya kare ko da ga shi nan ko yana gani shi ya sa yake rufa ma kansa a siri ko ya gani bai nuna yana bukata. Barcin sa rabi da rabi ne a baya ne da yasan Mimi na ƙarƙashinsa ya ke samun Ishasshen barci amman tunda ya fahimci kamar ta yi masa nisa ya daina samun barci cikin natsuwa. Shi fa a ransa sai da ya ga laifin Hajiya ta ya ya za a su bar matar aure tana yawo ba tare da sanin Mijinta ba shi fa tafiyarta Abuja ta fi masa raɗadi fiye da yadda take yi masa wannan renin wayau.
Da farko ya yi alkwarin ba zai ƙara kiran ta ba amman ba shi da mafita saboda ya kasa sukuni ko da bai kirata ba yana bibiye da dukkkan wani motsinta. Haka kawai saboda ita zai hau facebook da WhaApps ya duba ta, a Facebook duka Account ɗin ta guda biyu na Fatima Kabir Dabo(Mimin karamchi) da kuma na wanda ta buɗe a ɓoye na MIAJ, duk ya san dasu kuma yana vibiyanta amman ba ta taɓa sani ba, to abubuwa da dama ma ba ta sani ba wani abun gwara ka bar shi a rufe saboda Sanin shi a lokacin ba shi da wani amfani.
Yini yake duba ta sai ya ga ba ta saka komai ba kamar ma tun bayan auransu motsin Account É—inta ya dakata.
Sannan ya duba bangaren hidan tibin da take aiki, daman tun kwanaki ya ga ma kallata gidan Tibin suna ta cigiyarta sai suka ba da sanarwan ta na nan lafiya ta ɗauki hutu ne ma'ana Anaual leave ɗin ta, ƙaramin tsaki ya ja shi fa ya tsani aikin nan domin shi bai ga wani amfanin shi a Al'umma ba, Kuma zai bude data yana ganin tarin Groups da aka saka shi yawanci duk na ƙwallo ne tunda babu wani Team na nan Gombe da ba'a saka shi a ciki ba, akwai wani ma da tunda aka saka shi an tara saƙo sama da dubu bai taɓa buɗewa ba, kuma ko a Private ka yi masa mgana in ka ci sa'a ya buɗe ya karanta ba zai maida maka amsa ba sai dai in ta kama ya kira ka. Saboda gani yake ɓata lokaci ne ya tsayawa yana typing.
Shi ya sa duk yadda su Nasir suke caccakan sa a group ɗin su na Brother's bai ko shiga ba, Ko mu'azzam ba ya chart da shi sai dai in ya ga ya yi masa mgana ya sauka ya kira shi, yawanci ma shima yasan hali yafi tura mishi hotuna ko wani abu mai muhimmanci,group ɗin su na jami'a ko tuni ya fice,an sake maida shi ya sake fita har sau uku, daga nan suka ƙyaleshi.
Har ta goup ɗin su na Gombe United kowa na da amfani ban da shi hatta Coach na su yana mgana da sauran bayanai amman shi sai dai a waya ko ya je Camp ɗin ya tara su yi magana shi ya zauna ne wai ya ga yana rubutu ya ke ganin shi a ɓata lokaci ko kuma wai ya kunna voice note shi fa har mamakin ma su yi masa vioce yake yi, wani mai tsawon ma shi ai ba shi da wannan lokacin, wani lokaci yana buɗewa yake kashewa ba ya da lokacin saurara shi ya sa ga wanda yasan tayuwar Aji gwara ya kira shi a waya amman domin ya yi magana ta chart kamar ya zama aikin banza ne
Gabatowar wasan da suka shirya ne ya sa ya rage Tunani da damuwar Mimi sai da aka buga wasa aka ta shi lafiya sannan ya dawo natsuwarsa, kuma shi abin da ke ba shi mamaki Inna ƙiri ƙiri ta nuna ta fi son Mimi a kansa tsakani ga Allah shi fa Ɗanta ne, Ita fa Iyayenta ba su juya mata baya ba sai shi? Haka zai je Inna Meri ta yi kamar ba ta gan shi ba da ya Kira Mu'azzam ya yi masa ƙorafin abin da inna ke yi masa kai tsaye ya ce"Ni fa ba ruwana tunda ka ce kowa ya cire bakin shi a ciki."
Cikin haɗe rai Aji ya ce"A maganar Mimi ba, maganar Inna fa dole za ka yi min amfani ka kira ta ka nuna mata ni fa Ɗan ta ne ai bai kamata tana banzarta da ni ba, ita kanta Mimin da take min haka saboda Ita iyayenta ai ba su nuna son fi sona da ita ba, Itama Inna ta gane mana kowa fa nashi ya sani."
Mu'azzam na ta faman danne dariyansa, amman sai da ta fito Aji ya ji sa.
Sai kawai ya yi kafci kafin ya ce" Au dariya na baka? Ya yi maka kyau."
Daga nan ya kashe wayarsa, Mu'azzam ya biyo bayan kiran aka yi banza da shi ba'a É—auka ba.
Dole ya Kira inna Meri domin yi ma fan'uwansa biko, ya kuma maida mata abin da Mansoor ɗin ya ce kowa fa na shi ya Sani inna, ki yi masa hakuri in sha Allahu zai daidaita komai. Sai da ta gama jinsa sarai kafin ta ce"Mu'azzamu in kana son kanka da arziƙi a wajena kada ka ƙara kirana kan mganar ɗan'uwanka, ni na ce na yafe masa amman na tsame hannuna a kan rayuwarsa ya yi duk yadda ya ga dama."
Mu'azzam ya ce"Inna to ai baki haƙuran ba kenan, cewar da ki ke yi kin tsame a hannun ki a kansa kamar baki ne fa ki ka yi masa"
Inna Meri ta ce"Ban yi masa baki ba, kuma na yafe masa saboda ɓacin raina ma kaɗai bala'I ne wajensa, amman ba zan ƙara bari Baban inna ya ɓatamin rai ba, tunda shi haka ya ke ba ya jin mgana sannan abin da ya ga dama shi yake yi to ba sai ya je ya yi ta yi ba, ai yanzu ba mai ce masa don me, ni ce kuma na tsame bakina da hannuna a kan sa."
Mu'azzam na so ya ƙara mgana. Amman Inna Meri ta ƙi sauraran shi cewa ta yi in mganar da ya kirata su yi kenan za ta kashe wayarta dole ya bar maganar.
Sai washegari ya samu Aji ya É—auki wayarsa shi kuma ya gaya masa yadda suka yi da Inna numfashi ya furzar kafin ya ce" Ai shike nan."
Mu'azzam ya ce"Mafi masalaha ka je ka Dawo da Anty Mami in har kana son Inna ta Daina fushi da kai."
Cikin jin haushi ya ce"Wai ba na je ba. Tayi tafiyarta wai Abuja domin ta raina ni, da aurena a kanta amman iyayenta sun barta tana yawon tafiye tafiye."
Yadda ya faÉ—i mganar ne ya sa Mu'azzam ya yi shuru yana danne dariya kada ta fito abin a ya shafe sa.
"Gaskiya ba ta kyauta ba. To ka kira ta a waya mana?
"To taba É—auka ne? Wani irin kira ne ban yi mata ba ta É—aga kirana ba."
Mu'azzam ya yi tsai kafin ya ce"Topha! To ko za ka shirya ka je can Abujan ne ka same ta? Kasan mata fa yan Lallashi ne in ta ga ka Bbta za ta sauko sai ta Saurare ka."
Kai tsaye ya ce"Amman ba ka da hankali Mu'azzam ni ne zan bi ta har Abujan? Lalle to ta shekara a can."
Mu'azzam na shafa kansa daga can bangaren ya ce"Ba za a yi haka ba. Ya kamata ka samo mafita saboda Inna."
"To ai daman saboda ita ne ya sa ka ga ina bin ta amman ni har Mimi ta isa ina kiran ta a waya tana min wulaƙanci?
Sai ya yi kafci kuma shi kaɗai irin abun ya nan ya gama ɓata masa rai. Shi ko Mu'azzam wayar ya matsar gefe yana ta dariya shi kaɗai sai ji ya yi Aji na faɗin"Ni na ce ba zan kara kiranta ba amman kai in za ka kirata ne ba zan hana ka ba tunda ka matsa"
Mu'azzam ya yi ta dariya bayan sun gama waya da daddare ne lokacin Hibba na tiolet ta na wanka tun tana ciki ta ke jiyo dariyan Mijinta sanda ta fito ta iske shi ya na Dariya shi kaÉ—ai cikin mamaki ta ce"Me ka samu ne kake ta dariyan nishaÉ—i?
Yana dariya yana tuna amsar da ya bama Yayan na shi da cewa" Nima fa ba ta ɗaukan wayata. Sannan daga baya ma ina jin rufe ni ta yi ko na kira ta ba na samun ta, Ai ina ganin wannan faɗan ya fi karfin ƙanin miji sai dai mijin da kansa."
Kawai sai Aji ya ce"Kai dai ka sani."
Da haka ya katse wayarsa ya bar Mu'azzam na Kwasan dariya shi kaÉ—ai.
"Ina nan ina dariyan Yaya Mansoor, ina tunanin mu kusa mu ji shi a garin Abuja ya je biko."
Hibba ta ƙariso gefensa da sauri tana faɗin" Ba ni in sha, me ya faru?.
Nan ya labartamata abin da Yayan na shi ya gaya masa yaje gidan Hajiya Mimi ta tafi abuja sannan ya na kiran wayanta ba ta É—auka.
Hibba ta saka dariyan ƙeta kafin ta ce"Kai na gode ma Mimi, ai sannu sannu ba ta hana zuwa sai dai a ɗaɗe ba'a je ba."
Mu'azzam ya ce"Ina tsausayin shi ni nasan duk ya damu amman ba ya son ya nuna ace ya damu da ita, kuma muna nan dake zai kirani ya ce zai je Abuja amman saboda Inna ne."