Sashe 54
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
 A can gidan Inna Meri ma kamar tana sake sabon biki, makota sai zuwa suke yi daga can anguwan Arawa. Har da su Gaje domin Bintu ce ta shiga da gayya ta sanar da su Mimi za ta tare a sabon gida, ita kuma ta biya gidan Jummai ta gaya mata ta kuma san za ta gayama Zuwaira,. Sai ga shi har da Maeesha ta zo tunda ta dawo daga wankan gidan, Zuwaira ma ta zo Magajiyar ce kawai ba ta zo ba Mariya daman tun jiya tana gidan Har da matan Auwalu da ta daina adawa itama tunda mijinta ai yana gaya mata irin taimakon da Yayan Inna Meri suke yi ma rayuwarsa. An ci abinci shinkafa da alala lemuka da ruwa kam duk na gora ne aka yi ta sha ana guzuri. Daman sun ce za su je gidan su Mimi bikon ta daga nan sai su ƙarisa gidan gabaɗayansu suka yi gungu suka tafi, Inna kaɗai suka bari a gida da Dije matar mallan Hashimu sai yara har da su Gaje sun tafi Maeesha kuma daman ganin kwakwaf ne ya kawota kuma ta ga irin daular da Inna ke ciki saura kuma in ta je gidan su Mimi ta sha kallo.
 Sai da suka yi azahar wajen uku saura sannan suka hau adaidaita suka tafi, ba su ko jira kowa ba Hibba ta kira Mu'azzam ya ce suna gidan Makama kafin ma su kariso sun yi nisa shi ya sa kawai ta ce bari su tafi, Suna shirin tafiya ne sai ga Nafisa matar Nasir da Fati matar Ahmad sun zo gidan yi ma Inna murna. Dalilin su ya sa ma suka kai har biyu a gidan Inna sannan suka tafi, sai dai Mimi ta gansu kwatsam tunda ba su gaya mata za su zo ba, Bintu ce uwar faɗin sun zo ɗaukan Amaryansu ne.
Rukky ta ce"Kwa dai jira dai mu miƙa ta can gidan ko?
Hibba ta ce"Ai ta mu ce tuntuni, saboda haka a bamu matar mu mu mikata gidan ta da kan mu."
Ana ta raha ana dariya an kawo musu abinci su ka ce sun koshi amman irin su Jummai sai da suka ci, suna ta mamakin girman gidan sai ma su ka ji an ce nan É—in gidan kakkaninta ne Gidan iyayenta na Abuja su Gaje sun sha kallo irin su Maeesha sai zaran ido ba baki ai tuni ta raina kanta.
Mimi ta yi ma Rukky raÉ—a kunne da cewa" Ga kishiyar can"
Ta na nuna mata Nafisa da ido wacce ke ba ma yarinyarta nono, Rukky ta ga ba ta da aibu kwata kwata ga ta doguwar mace sai dai kawai abun namiji amman mai mace har Nafisa ai ba shi ba sake kallon wata ua mace sai dai su daman maza haka Allah ya hallice su.
 Duk saurin da a ka yi sai da suka kai la'asar a gidan Hajiya tun da sai bayan oa'asar ɗin su Mu'azzam suka zo da motociin, Ahmad ne ya tuka motar Aji a motar Mu'azzam a ka ɗauki Amarya da yake akwai motocin gidan Daddy wajen guda uku shi ya sa kowa ya samu har da su Hibba kuwa, Kuma daman su Anty sun yi gaba tun ɗazu sun kai Yaddiko ta ga gidan daga can za ta wuce gida ba ta jin daɗi tana ta fama da kafa, Sun iske su sun ƙara gyara gidan ma sha Allah ya na faman ta shin kamshi.
 Guɗa kawai ke tashi Bintu ne da wannan aikin, Khadi da Mama suka riƙe Mimi ta yi addu'an sosai sanman suka shigar da ita tana nannaɗe cikin lafayanta ja. Gida fa ya yi kyau turbakallah masha Allah, Walima a ka ce za'ayi Mama ce ta gayyato wata malamar Islamiya an kawo Mimi ba daɗewa ta zo. Bayan ita sai ga yan wajen aikin su Mimi Rukky ta fita bakin hanya ta shigo da su ta bakin Aisha Farida ta ce aiko daga yanayin anguwan za ka san ta masu abin ne Sai da suka ga gidan Mimi suka ruɗe, suna tambayan kuma gidan Sabo ne?
Rukky ta ce"kwarai dal ma kuwa, kowata biyu ba'a yi da fara gina shi ba a ka gama sh." Haka suka riƙa zagayen gidan suna buga sqntin an raba cake da nama a babban falon gidan aka taru malama ta yi nasiha sannan tare da addu'o'in sabon gida na awa ɗaya sannan a ka tashi kowa na saka albarka, Maeesha dai ban da yaƙe ba ta komai gassadan ma ta kasa samun muhalli domin daga gidan har kayan gidan kowa yasan na alfarma ne. Ta kuma ƙara yardan ma kanta Mimi ba sa'ar karawarta ba ne.
 Ana gama walima ba wanda ya tsaya har su Khadi sun tafi.Su Hibba kawai a ka bari a gidan su Gaje ma sun tafi tare da su Maeesha, daga Nafisan Nasir sai Fatin Ahmad ma ta koma gida ta yi girki. Su aka bari da ƙara gyaran gidan Rukky kuma na tare da Mimi nan suka yi sallar mangariba bayan sun gama gyara Ko'ina sannan suka yi shirin tafiya, da wuri suka ce za su kawo Ango shi ya sa su Yaya Amina suka tasa su Mariya har da Bintu zuwa gida Hibba kawai a ka bari saboda mijinta da ita da Nafisa da Rukky, suna ƙara ɗan gyara gidan Mimi ta yi wanka ta sauya kaya anguwan ga su da ruwa ita Mimi Bahol gare ta ma ba ta da wata matsala. Ana idar da sallar Isha'i Angawayen suka shigo su biyar Ango dai ya yi shigar wata deep blue ɗin shadda tana yarari da maiko ga hula bakar dara da takalmi sau ciki sauran kuma kowa dai ya saka manyan kaya, Mu'azzam ne ɗauke da ledojin kaza, Sai kuma sun shigo da katan katan ɗin ruwa sai kayan tea da buredi siyayya fa da yawa, Rukky na yi ma Ajin tsiyan wato dai in ya fara cin amarci ko Kofar gida ba zai fita ba.
 Yana shafa keyarsa ya ce"Ashe kin gane.".
Sai ya bar su Nasir da yi masa tsiyan bai isa ba sai ya fito. Falo Mimi ta fito suka haɗu suka yi musu yan nasihohi daman a auran farko ba su aiwatar da wannan al'adan ba, Saboda Nafisa na wajen ya sa Nasir bai yi rawan kafa akan Rukky ba. Dukkansu sun kame kansu, Aji ya duba agogon fatan hannunshi ya ga tara har ta gota kawai sai ya kalli Mu'azzam kafin ya ce" Lokacin ku ya kare fa, kwashi abokan ka da matanku ku je na gode sai Allah ya kai mu."
Suka saka masa dariya gabaɗaya Nasir na masa raɗa a kunne shi kuma ya daki Kafaɗansa yana yar fariya, da za su tafi ko Rakiya bai yi mu su ba iyakarsa ƙofar falo suna fita ya rufe kofa.
Makama a ka bari da kai Rukky gida roƙonsa Nasir ya yi, shi kuma ya ɗauki matarsa, Ahmad kuma ya bi Mu'azzam da Hibba za su sauke shi a gida. Hankula sun kwanta tunda Mimi dai ta tare a gidan Aji a karo na biyu.
 Ajin na jin buɗe get da alamun fitan su ya sauke ajiyar zuciya ya ƙarisa kusa da Mimi ya ɗago ta daga zaunen da take cikin mayafinta tana tashin kamshi, kai tsaye ya rumgumeta cikin natsuwa suka yi luf a jikin juna suna shaƙan kamshin turaren Juna, sun ɗauki wajem minti goma a haka sannan ya ɗago ta ya yaye mata mayafinta suna kallon juna cikin wani irin murya ya kira sunanta
"Fatima.."
Da wani salo ya kirata da ya sa ta ji ta ƙara narkewa cikin sanyin murya ta ce"Na'am.."
Kallonta kawai ya ke kamar ya ga ta sauya masa sai da ta shafa fuskarsa tana faÉ—in"Kallon fa? Na sauya maka ne?
Numfashi ya fesar ta baki kafin ya ce"Eh mana, kin ƙara kyau, duk da daman ke ɗin mai kyau ce."
Mirmishi ta sakar masa kafin ta ce"Ajin Mimi ma ya yi kyau sosai."
Riƙo ta ya yi lokaci ɗaya yana sagala hannunsa ta wajen kugunta kafin ya ce"Kin yi sallar Isha'i?
Sai ta gyaɗa masa kai kafin ya cigaba da faɗin" Wannan tarewar ta sha bambam da auranmu na baya, wannan da niyar ingattaciyar zamantakewa ne a tsakanin mu saboda haka mu je ki yi alwala nima na yi domin mu yi sallar da Annabi ya umarce mu da yi a daran farko tare da roƙa mana Zuru'a mai albarka da zaman lafiya."
Tana Mirmishi ta É—aga masa kai kafin ta ce"To mijina."
Ya kalleta ta kalle shi sai kawai ya sumbaci goshinta suna rike da juna har zuwa cikin Bedroom É—in, tare suka shiga tiolet É—in daman diukkansu suna da alwala sun dai sake sabunta ta ne, sannan suka fito a tare ya shimfaÉ—a musu sabuwar sallayar da ya gani nan saman gado, yana gaba tana bin shi a baya sai da suka yi raka'a Takwas sannan suka zauna ya É—aga hannuwansa sama itama ta É—aga yana ta yi musu addu'an zaman lafiya sannan daga karshe yace Allah ya tsare su daga dukkan wani sharri. Daga karshen karshen ya ce Allaha ya jikan Iyayensu su kuma ya sa su tafi a sa'a cikin aminci.