Sashe 88
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna cikin ɗakin nan ko karyawa ba su yi ba. Sai da Dr ya sake dawowa ya lallashe su amman ba su ji ba gwara Mimi ta sha tea sannan ta ci dankalin da Asmauu ta soya ko saboda goyo. Sannan ta saki fuska har ta je ta gaida Hajiya da Mommy da duk idanuwanta sun kumbura saboda kuka Hajiya ta kalli Mimi kafin tabce"Binta ka da na ji ko na gani kin biye ma sakarkarun yayyenki kin saɓa ma Murja, kin ji ko?.
Sai ta gyaÉ—a mata Hajiya sai faÉ—a take yi Inna Zainaba na wajen ta ce"Hajiya kyalesu sai dai su mutu aure kamar an yi an gama."
Mommy daman a jiyan ta ce ita ta fasa Inna Zainanba ta dira kanta da faɗa da cewa"Sai zauna ki koma baya kina bin ƴaƴa sai abunda suka ce aure fa ba mai tada shi na ce duk wanda ya ji haushi kada ya ƙara neman ki."
Khadi da Madiha suka fara shirin tafiya, Sai dai misalin goma sha ɗaya safe suka ji Inna Zainaba na sakin guɗan an daura auran Mommy da wani, gabaɗaya sai hankalinsu ya ƙara ta shi, ba yadda sulaiman bai yi da su su tsaya kada su tafi ba suka ƙi ba da asuba kafin ya wuce tunda shi ma jirgin karfe bakwai ya bi ya koma kano ya samu ɗaurin auran Mommy.
ita madiha ta samu jirgi amman Khadi motar haya ta bi zuwa Kaduna kuma ko sallama ba su yi ma Mommy ba ballantana Hajiya, Mommy ta damu Inna Zainaba ta ce kada ma ta saka a ranta su je, ma ji ma gani in sun isa su sauya ma tuwo suna. Mimi ce kaɗai a gidan itama sun yi da Aji zai zo bai kuma zo ba sai bayan azahar shima da labarin Mommy ta tare shi sai ya washe baki yana riƙe da Ummi lokaci ɗaya yana faɗin"Ma sha Allahu abun alheri madallah. Na yi ma Mommy murna Allah ya ba su zaman lafiya."
Kawai sai ta saka masa,kukan me ya sa zai yi murna saboda Momny ta yi aure? Ba ya kishin Abi ne me ya sa Mommy za ta ƙara aure? Cikin Mamaki ya kalli Mimi kafin ya ce"Ban gane ba? Saboda addini ya ba ta wannan damar gwara da ta yi auranta sai mutumcinta ya fi fitowa a idanuwan waɗanda suka santa, sannan kuma kwanciyar hankalinku ne ku tuna yau tana da miji kuma sannan kun kara samun wani abu a karo na biyu."
Kawai sai Mimi ta saki baki ta kasa mgana, Aji ba zai gane ba ne shi ya sa ba ta ma samu damar gaya masa abunda ya faru da su khadi ba sai da ya shiga suka gaisa da Hajiya ita ke gaya masa har ta na cewa" Ga ta nan duk da itama ba ta ce komai ba amman zuciyarta ba daÉ—i ka sake yi mata faÉ—a don Allah kada su saka ma Murja hawan jini."
Aji ya kalli Mimi da ke gefen sa kafin ya ce"Haba Hajiya, suma É—in yarinta ne amman in su san ciwon kansu ai ba za su yi haka ba, sannan su mata tunanin su a karkace yake, shi Dr da yake namiji ne ai ya fahimta kada ki damu Mommy auran da ki ka yi masalaha ne ga rayuwarki da ta su gabaÉ—aya ba za kuma su fahimta ba sai nan gaba kaÉ—an."
Inna Zainaba ta ce" Ka ji maaganar masu hankali, itama sai ɓata rai take yi tunda ƴan'uwan sun yi fushi sun tafi."
Kuma da gaske nan ko fara'a Mimi ba ta yi Mommy ma duk ranta a jagule ga shi sai kiranta a ke yi masu yi mata murna, tunda acan kano aka ɗaura auran shi kan shi Alƙali bai je ba. Sai dai waliyyansa kuma da kan shi ya faɗa mata an ce babban ɗanta ne ya ƙarbi sadakinta wato Dr Sulaiman farinciki ya cika Mommy har sai da ta yi kuka a ranta ta yi ma Sulaiman fatan ya gama da duniya lafiya shi da iyalansa yadda ya ke faranta mata shima Allah ya faranta masa haka. Aji bai tsaya wani lallashin Mimi ba saboda ya ga kamar abun na su har da iskanci, bai nuna ma ya gane ta na jin haushi ba bai daɗe ba ya tafi sun rabu akan itama gobe za ta koma, cikin zolaya ya ce" Ki tsaya mana ko zuwa laraba ku gaisa da sabon Abin naku mana."
Hararansa ta yi sai ya yi shuru ya na dariya , har ya ci abinci ta tafi raka shi tana kumbure kumbure shine ma ya sa ta saki fuska tunda cakulkuli ya riƙa yi mata tana dariya.
Yana kuma tafiya ta koma yadda take, Mommy ba ta yi gayya ba amman ta gayyaci abokan aikinta sun zo mata murna tunda da É—aurin auren da tariyan duk É—aya ne ita a gidanta za ta zauna shi ne zai rika zuwa wajenta in ranar girkinta ya shiga, bai zo a daran ba sai washegari da safe da ta ce ya zo su gaisa da Hajiya da Mimi za su koma Gombe. Gaskiya a ido mutum ne mai kamala da dattako ba yaro ba ne domin zai iya yin sa'an Abin ma, sun gaisa cikin girmamawa da Hajiya, Mimi kuma tana gaisheshi ya kama sunanta da cewa"Mimi auta ko? Yau dai navga auta."
Ya faɗa ya na mirmishi ya miƙa hannu ya karɓi Ummi yana faɗin"Ga kuma Ummi maryama ko?
Sai Mimi ta gyaÉ—a masa kai a ranta tana faÉ—in su Mommy manya, ta sha kwaliyarta suna ta yi ma juna wani kallo.
Ba ta gama mamaki ba sai da ta ji ya na tambayan su Madiha tunda Mommny ta gaya ma sa dukkansu sun zo.
Da sauri ta ce Madiha za ta koma saboda yara ita kuma Khadi saboda aikinta sai ya ce bakomai wata rana ai za su haÉ—u Dr dai yana kano sun haÉ—u tunda shi ya ba da auran Mommyn tashi ya faÉ—a har ya na kashe ma Mommy ido, Mimi ta ji kamar ta make shi saboda haushi.
10k ya saka ma Ummi a jikinta sannan ta yi masa sallama ta bar falon zuciyanta na ɗaci saboda haka ta matsama Hajiya suka koma Gombe a ranar domin ba za ta iya zaman ganin wannan bakincikin ba Aji ma ya yi da ita ta zauna da Mommy ko na sati ne sai su koma tare amman ta ki sai ta fake da aiki shi kuma ya san dalili amman sai ya ƙyaleta. Kuma da ta dawo ko a zencen ba ta taɓa faɗan cewa Mommy ce ta yi aure ba.
Ko Inna ba ta gaya mawa ba ta kuma san Aji ba shi da surutu daman dai Mu'azzam ne, Rukky dai ta samu labari ta bangaren Jaheed da ta kira ta ta na tambayanta ashe kuma Mommy ta yi aure sai kawai ta ce"Uhm" daga nan ta sauya mganar har Rukky dai ta gano Mimi ba ta son mganar. sannan da kanta ta kira su khadi ta na gaya musu abin da ya faru sanda Alƙali ya zo tana gaya musu Mommy ta ba shi labarin kowa ya san shi ya sunan sunan shi.
Madiha bakin ciki kamar ta mutu sai ta ce" Wai mommy yarinya ce? Ji fa wannan aikin da take yi mtswww.."
Ta yi tsaki duk suka ƙara saka Mimi a tafiyarsu na ba su amince da auran ba shi ya sa ko da ta dawo ko sau ɗaya ba ta kira Mommyn ba sai ita ce ta kirata tana cewa ba ta kira ta ba kada bakin Mimi sai ta ce"Ina zan kira na takura miki Mommy, na baki lokaci ne ki ci amarcin ki.'
Mommy sai ta kasa mgana jiki a sanyaye ta ce"Ke ma kin kasa fahimtata ko Fatima.?
Da Sauri Mimi ta ce"Na fahimta kina son aure kuma kin yi, Allah ya ba da zaman lafiya. Daga nan ta kashe wayarta daga ranar ba ta ƙara nemanta ba, itama Mommy sai ta ba ma zuciyarta haƙuri ta tsaya ganin in da suka dosa. Matar alƙali da yayansa sun karɓeta sosai sai ita ce ke da yayan da ke yi mata barazana in ka cire Sulaiman Asma'u sai murna take yi ta samu Abba amman ban da su Madiha da suke kishin Abi sannan suna ganin kamar abun kunya ne.
Hibba ta saamu labarin auran da Mommy ta yi ta bakin Jawahir tunda sanadin Mimin suna zumunci ta je gidan shi ne ana hira labari ya kawo ta faÉ—a mata, tana komawa kuma ta faÉ—ama mijinta shi kuma sai ya xe bai ji ba, bayan ya kira yayanshi ya tambayeshi sai ya ce eh da gaske ne. Ke Hibba sai ki ka ga Mimi a chart sai kika ce mata" Matar Yaya ashe kuma Mommy ta yi aure? Allah ya sanya alheri."
Sai ta tura emojin dariya har da na rawa, wannan abun Mimi ta gani sai ranta ya ɓaci kawai sai ta yi ma Hibba vioce da cewa miye take mata dariya saboda Mommy ta yi aure? Abun dariya ne ya faru da za ta riƙa mata dariya? Tun Hibba na ganin wasa har Mimi ta maida mgana faɗa ta kira Hibba a waya tana gaya mata mganganu marasa daɗi har tana faɗin in abun dariya ne to ta bari in nata Baban ya rasu mamanta ta sake wani auren za ta yi mata dariya ta ji in da daɗi. Ran Hibba ya ɓaci sukavyi ta gayama juna mgana ita da Mimi a ka rabu ba daɗi har da su blocking ɗin juna.