← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 93

Sashe 3

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Idon su ya rufe ba wanda yasan Bintu ta zo gidan sai da ta kwaɓe hijabi ta ci ɗamara ta sha gaban Inna tana nuna Magajiya da yatsan hannunta lokaci ɗaya tana faɗin" Ya ishe ki fa magajiya kul ɗin ki, Innar mu ta fi karfin reni daga gareki, yayanmu ya fi karfin ku kirashi yana hango wani abu me zai hanga? Me kuke da shi? Miye a wamnan gidan ban da tsiya? Na rantse da zatin Allah ban ga wani abun arzikin dake gidan da Yayanmu zai nace sai ya zauna ba sai dai can wani ra'ayi na shi ,kuma  dukkan nan kunsan ya fi karfin zaman a wannan a kurkin ɗakin da kuke rigima a kan shi."
Ta faÉ—a cikin bacin rai, Magajiya sai ta saki baki ta na kallon Bintu, haka ma su Baba Sani Baba ÆŠanjuma kuma sai ya yi mirmishi a kallah dai yasan yanzu za su saurara.

  Baba Sani ya nuna kansu yana faɗin" ke ke, wai mu kike kira matsiyata don uban ki? mu sa'annin ki ne?
Magajiya ta saki shewa tana faÉ—in" Lalle, to in har ana da arzikin a tashi a bar ma masu gado gida ehe."
Saddiqu ya harzuka ya faɗo tsakiyar wajen kamar zai kai ma Bintu duka Inna Meri ta tare gabanshi tana faɗin" Kul kar ka  sake ta taɓa ta, matar aure ce kuma sannan ƴaƴanta na kallon ka."
Sai Baba ɗanlami ya fara Kumffar bakin ta na kare mata amman tana gani tana yi musu rashin kunya. Saddiqu kuma yana haƙilon sai ya yi kasa kasa da Bintu ita kuma ta na bayan Inna ta na faɗin Uban da ya fasa wlh in ya taɓa ta sai ya yi kwanan cell.

  Inna Meri ta kalleta kamar ta make ta tana faɗin" Rufe min baki me ya sa baki da kunya ne?
Bintu ta tura baki tana faÉ—in" Inna to ba ki ji abin da yake cewa ba ne, ni zai da ka? To wallahi kar ya fasa."
Inna Meri ta ja Bintu ta turata cikin É—aki har su Hibba ta ce su shige da yaran kar wacce ta sake fitowa, itama sai Baba Danjuma ya riketa ya na neman tura ta cikin É—akin yana yi mata magiyan ta yi shuru lokacin fa har su gaje sun jiyo hayaniya sun shigo gidan.

  Amman Inna ta kafe ta ce ita ba faɗa za ta yi ba mgana za ta faɗa musu sai ya sake ta.
Kallonsu ta yi dukkansu kafin ta ce" Ku kwantar da hankulanku zaman Binta a gidan nan tun jiya ya ƙare, ga ɗaki nan ku yi yadda kuke so da shi.Ɗan yau ne ka haife shi ba ka haifi halin shi ba, in da ace Baban Inna mai jin mgana ne wallahi da yau ba ta zo ba, amman ku yi hakuri ga ɗaki nan in kuma nan ma bai isa ba, ni ma kuna son na tashi na bar ma shi Saddiqun shashen ne gabaɗaya sai in ta shi, miye a ciki? Ai ba wani damuwa tunda gidan ubansa ne, ni kuma matar babanshi nake  kuma ya fini iko da gidan gabaɗaya"

  Da sauri Baba Ɗanjuma ya ce" Ki fita ki bar musu shashen? To ban animce ba, ba ke ba ko Manaoor ba in da zai je."
Inna Meri ta ce"Magana ai ta kare kuma, ga É—aki nan zan kira Hajiya su zo su kwashe kayan su, abin duk bai kai na faÉ—a ba."
Sai mamaki ya kamasu Baba ÆŠanjuma cikin mamaki ya ce"Ban gane ba, ina ita Bintar?
"Ta na gidan su tun jiya.?
"Me ya faru?
Inna ta kalle shi lokaci É—aya kafin ta yi mirmishi tace" Ina ga sun rabu ne."
GabaÉ—aya su Baba Sani suka zaro ido, ita Inna Meri É—aki ta shige da sassarfa Baba ÆŠanjuma ya bi bayanta cikin mamaki.
A ka bar su Magajiya a tsakar gida suna ta magana ƙasa ƙasa.
Magajiya ko har dariyan mugunta ta saka da karfi ta ce"To daman ina wannan auran zai yi karfo? An gama karyan arziki ya auro wacce ta fi karfin shi, ai daman hausawa sun ce kwarya ta bi kwarya in ta hau akushi sai ta fashe fasss."

Ita dai tunda an ba da ɗaki ta yi wucewarta shashenta tana waƙe waƙe  Ta bar su Baba Sani na mganganun su, Gaje ta bi bayanta Harira dai duk ba ta ji daɗin abin da ya Faru ba,.Haka suka fito suna ta dariyan cewa Daman ai tun farko ya kai kansa in da aka fi karfinsa , Saddiqu ma sai dariyan mugunta yake yi domin ya ce ya na jin haushin Mansoor ya yi ta nuna yafi kowa sa'an rayuwa.

  A can ɗaki kuwa Baba Danjuma ya tsare Inna Meri sai da ta maida masa abin da duk ya faru a daran jiya.
Cikin tashin hankali y ace"Innalillahi! Ban san duk haka ya faru ba, jiya na gaji sai na kwanta da wuri amman Meri me ya sa kika barta ta tafi?
Inna Meri ta bar gaban Baba Ɗanjuma sai ta koma gaban tibin dake ɗakin tana neman Sigan da za ta saka ma Kuni lokaci ɗaya tana  faɗin"me ya sa kuke tunanin zan hana ta tafiya? Shi wanda ya ijiyeta da kanshi muna ji ya ce ta tafi ɗin zai fi, ni kuma a wa da zan ce kar ta tafi,? wallahi  na ɗauki Binta a matsayin ƴata kamar Bintu ko itace Bashir ya yi mata wannan wulaƙanci sai na dawo da ƴata gabana sannan na saka ya sake ta tunda ba a zaman aure dole ko domin alfarma."

  Baba Ɗanjuma da ya fahimci ranta ya ɓaci sai ya ce"Yanzu Shi Baban Inna yana ina?
Inna Meri ta yi masa banza ta duka tana saka ma kuninta siga,  sai ya shiga ƙwalama Walida kira sai ga ta fito ita da Bintu su yake tambaya Mansoor walida ta ce tun jiya da ya fita bai dawo ba sannan Yaya Mu'azzam ya ce yana ta kiransa bai same shi ba.
Baba Danjuma ya fice yana faÉ—in bari ya neme shi ya gani ko zai same shi.
Ya na fita Bintu ta ce" Yaya Mansoor bai  kyauta ba, ga shi yanzu saboda shi  an zo Anci mutumcin Inna"
Nan suka zauna suna mai da yadda akayi Inna ba ta saka musu baki ba tana dai ta hidima da yara abin ta, Bintu ce ta kira Yaya Amina da Yaya Halima ta ce su zo gida su dai sun ce in Inna ba za ta saka baki ba su za su saka, in ta kama sai su je su ba ma Mimin hakuri da kansu, tunda Hibba nata kiran wayarta ba ta É—auka ba,daga baya ma sai su ka ji wayar a kashe.

******

*MANSOOR.!*

Tun a daran jiya da ya bar gidan ya isa camp ɗin su domin a tunanin shi anan zai samu natsuwa. Sai dai Ina! wannan natsuwar da ya ke fata ya kasa samun shi, gaɓadaya ji ya yi kamar ya na cikin nadama wata zuciyarsa tana faɗa masa abin da ya aikata ma Mimi bai kyauta ba? A ƙasan ran shi ya ke jin radaɗin maganganun da ya gaggayamata sannan a cikin kunnuwansa ya ke jin sautin kukan ta, me ya sa? me ya aikata? Menene laifin Mimi da ya riƙeta a cikin ransa? In har zai yi adalci da ita da shi duk suna matsayi ɗaya ne a lokacin.

  Amman sai wata zuciyarsa ke faɗa masa abin da ya aikata shi ne dai dai domin duk abin da ya faru Babanta ne sila, kuma ya san duk barazana ce ba za ta iya tafiya ko ina ba saboda ta na son shi, bai taɓa tunanin da gaske Mimi za ta iya tafiya ba in da ace yasan za ta suɓuce masa da bai tafi ba da ya tsaya ya bata hakuri.
Ko ya yi tunanin kamar ya tashi ya koma gidan ya ba ta hakuri amman sai zuciyarsa mara kyan ta hana shi, sai yake ganin kamar shi za ta ba ma hakuri domin shi aka fi Saɓamawa da wannan tunanin ya sa ya kasa dawowa amman barcinsa rabi da rabi ne gabaɗaya sai yake jin sa kamar wani mai laifi, yana ji kamar ba shi da gaskiya sannan yana jinsan kamar wanda ya ɗauki wani irin nauyi mai girma a saman kansa.

  Uwa uba ga kallon da Inna ta yi masa a jiya nan yasan ba shi da bakin kare kan shi, sai kuma ya yi tunanin bai kyauta ba ya fara nadama sai wannan baƙar zuciyar tasa ta rinjayeshi ya ji kamar abin da ya aikata daidai ne, amman kwana ya yi da ya runtse ido sai ya ga Mimi ta na wannan kukan.
Da asuba ya kashe wayarsa saboda wata  zuciyarsa na zuga shi akan ya ɗaga waya ya kira wayar Mimi ya ji lafiyanta ita kuma wacce baƙar zuciyar nasa na nuna masa shi ne akan dai dai. Saboda kar ta  rinjayesa ya kira ne ya sa ya kashe wayar gaɓadaya.

  Ranar morning traning gare su sai dai ya wakilta Zinder ya tsaya da su, ya ce ba ya jin daɗi ɗakinsa dake cikin camp ya koma ya kwanta saman ƙaramin gadon yana faman tunani ya yi juyi ya fi sau goma amman Mimi ce a cikin ransa! Ko ya koma gidan ne ya ga halin da take ciki? Ko kuma ya kira ta a waya ne? Haka yake ta wannan tunanin sai ya ji kamar ya amince ya ta shi ya je ya ganta sai wata zuciyar ta ce"Me kake shirin aikatawa? Ai ba ka yi mata laifi ba duk abin daka faɗamata gaskiya ka faɗa."
"A'a na na yi mata ƙarya, na yi mata karyan cewa ba na sonta ahalin duk duniya duk wata macen bayan uwata da ƴan'uwana su biyo bayan Mimi a zuciyarsa duk saboda ita ne ya koma haka saboda tsananin kishinta da yake yi ne ya sa a tsawon shekarun zuciyarsa ta kasa zama cikin salama a baya yana da tabbacin in da ace Mimi wani ta aura ba shi ba, to ko bai mutu ba sai ya Ta ggayara.
Chapter 3 · 0% Book details