Sashe 78
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Haka ya faɗa yana tsare ta da Idanuwansa sai kawai ta saka masa dariya kafin ta ce"Da izinin mijina mana, ka manta ranar na ce maka Rukky za ta rakani anguwa? Ka ce sai na dawo kada na yi dare? To ai kasuwan ne anguwan"
Sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Na ji kin yi naki, ni me ya kamata na yi?
Sai da maida ledar in da ta É—auko sannan ta zauna gefensa kafin ta ce" To me ya kama ta ka yi? Tunda ni na siya waÉ—anan kayan me zai hana kai sai ka É—ora mata da KuÉ—i?
Kai tsaye kuma ta cigaba da cewe" KuÉ—in zai fi, tunda ka ga ni na siya kayan sai mu É—ora da kuÉ—in zai fi."
Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Shike nan amman kamar nawa ki kke ganin zan É—ora na kuÉ—in?
Kai tsaye ta ce"Â Duk abin da Allah ya hore maka Merapyaarr"
Sai ya gyaÉ—a kai kafin yace bari da safe in Allah ya kaimu.
 A daran bai mata mganar satin da ta ce za ta yi ba sai da safe tunda tun asuba ta tashi tana aiki. Daman tun a daran jiya ta yi masa miya saboda tasan shi ba ya son aiki.
Sannan ta saka an yi masa snak cake da cincin da samosa ya riƙa shan Tea da shi kafin ta dawo duk kuma ta kaisa kitchen ta nuna masa, har tana cewa ya riƙa dafa farar shinkafa ko taliya ya na ci da miya.
Kallonta ya yi a karkace kafin ya ce"Wai wata za ki yi ne a can?
Mimi ba ta ba ma tambayansa muhimmanci ba ta ce"Ka manta, na ce maka zan yi sati É—aya."
 Bai ƙara mgana ba. Sai da suka karya har Mimi ta yi wanka tunda Bintu ta kira ta ce suna gidan Inna ita a ke jira mai motar ya ce karfe tara na safe za su tafi, Aji ya riga ya biya kuɗin motan na zuwa da na dawowa.
Sai da suka zo sallama duk da shi zai kaita gidan Inna a motarsa, ya rumgumeta yana shafa cikinta da ya fara tasawa lokaci É—aya kafin ya ce"My jan.."
"Uhm Merapayaar."
"Bai kamata ki je ki yi sati ba. Saboda kina da juna biyu ni ya kamata na riƙa kula da lafiyarki, don Allah ki yi kwana biyu ki biyo su Yaya Halima ku dawo"
Da sigar lallashi ta faÉ—a, da yasa ta yi shuru ta lafe a jikinsa.
Ganin ta yi shuru yasa ya ƙara sausauta murya kafin ya ce" Na saba dake, ba zan ji daɗin zama ni kaɗai ba, ba ki tausayina? Wa zai rika ba ni abinci yana min hira? Ki bari daga baya ko bayan kin haihu ne sai ki je ki gaishesu. Ni sai ma mu tafi tare na rakaki amman na roke ƙi da Allaj ki dawo tare da su Yaya Halima.".
Nan ma shuru ba amsa, Idanuwanta ya ciko da kwallah. Domin har ta faÉ—a ma Mommy za ta je soron É—inki, sannan kuma yanzu sai ta ce ba za ta samu zuwa ba?
Ganin yadda ta nuna ne ya sa sai ya raba ta da jikinsa lokaci É—aya yana faÉ—in"Amman kin kin ga da takura ba zan hana ki ba, ki yi satin sai ki dawo daga baya."
Sai kawai ya juya zai fita daga ɗakin da sauri ta riƙo hannunsa kafin ta rumgumeshi ta baya lokaci ɗaya tana faɗin" Umarni kawai za ka ba ni ba alfarmana za ka roƙa ba, ai zaman ka nake yi, Kada ka damu zan dawo in sha Allahu tare da su."
 Kamar zai yi kuka ya juyo yana faɗin "Kwana biyun za ki yi ko? Sai ta gyaɗa masa kai, rungumeta ya yi cikin farinciki lokaci ɗaya yana faɗin" Allah ya miki albarka My Jan, na yi miki izinin ko Walida ko Bintu su raka ki ki je ki gaishe su kin ji ko? Sai ta gyaɗa masa kai, Ita da kanta ta yi ɗage ta sumbaci kumatunsa. Shi kuma ya yi saurin damƙe kanta ya rankwafa yana sumbatar bakinsa, ita kuma sai ta zagaye hannayenta daga bayansa ta rumgumosa sun daɗe a haka kamar ka da su rabu gani ta yi zai ɓata mata kwalliyarta yasa ta ƙwace jikinta lokaci ɗaya tana faɗin" Suna jira na fa."
Ƙara riƙota ya yi lokaci ɗaya yana faɗin"Minti biyar to."
 Dole ta kyaleshi ya rumgumeta kawai ya na shakan kamshinta. Sannan ya sake ta lokaci ɗaya yana riƙe mata hannu ɗayan hannun kuma ya rike akwatinta, sai ta karɓa Lokaci ɗaya tana cewa"Sai na sauya shiri."
Shi taya ta ta rage wasu kayan, kayan sunan ma da za ta kai ma Hibba duk a ciki ta tusa kafin su fito har Yaya Amina sai da ta kira shima Kuma Mansoor Auwal na ta kiran shi Mu'azzan tun asuba ya kira baki ya ƙi rufuwa yan'uwansa suna hanya.
Shi ya rike mata akwatin har jakarta sannan ya saka mata mayafinta a saman kanta ya rike mata hannu ya kai ta har mota, sannan shima ya zagaya ya shiga a hanya suka tsaya ya cire kuÉ—i 50k yace ta haÉ—a ta kai ma Hibba ta amsa lokaci É—aya tana faÉ—in. "Mungode Baban Maryam Allah yasa ka ma nema albarka."
Yana mirmishi ya ce"Amin Amin Ummu Maryam."
Suka haɗa ido suka yi ma juna mirmishi, ya rike mata hannu da hannunsa guda ɗaya, ɗayan kuma ya na tuki dashi, kewarta yake yi tun kafin ta tafi, ganin yadda ya matse mata hannu yasa ta rike hannayensa da hannunta guda biyu ta jimke kafin ta kallesa cikin shagwaɓa Ta ce.
"Ina sonka, ina matukar kaunar ka.."
 Wani kayattacen mirmishi ya saki kafin ya ce" Kin san dai na fi ki son ki ko? Ina sonki, ke ce komai nawa Fatima."
Sai suka ƙurama juna ido, ganin kamar hankalinsa na kanta yasa da sauri ta ce"Tuki kake yi, ka kula Merapayaar"
Sai ya maida hankalinsa kan hanya Allah yasa ma titin ba motoci sosai. Suna tafe amman suna ƙanƙame da hannuwan juna
"Ki kula da kanki, kin ɗauko magungunan ki? Sai ta gyaɗa masa kai kafin ta yi mgana ya yi saurin cewa"Ka da ki ci wani abun da cikin ki ba ya so, ina son cikin nan Mimi nima na ƙosa ki haifamin wata Maryama ɗin" mirmishi ta yi masa kafin ta ce" In sha Allahu kada ka damu."
Sai ya jinjina kansa, sun shigo anguwan Tunfere kenan ta ji yana faÉ—in" Na ma gayama Mu'azzam ya kula da ke, kina da juna biyu."
Mimi ta kalleshi cikin jin kunya ta ce"Kai, wai kai baka jin kunyar gayama mutane ina da juna biyu?
Suna tsayawa ƙofar gidan Inna dai dai lokacin da ya kalleta yana faɗin" To miye a ciki? Ai ba abun kunya ba ne na ga abin farinciki ne kowa kuma na son matarsa ta samu ciki."
 Mimi ta ce"Duk da haka dai ba a faɗa sai dai a gan shi ya fito, haka fa da muka je gaida Daddy ka faɗa masa wai ina da juna biyu."
Dariya ya yi mai sauti kafin ya ce"Kin ji ki da wata mgana? Abun kunya ne? Na ga dai abun alhafari ne, kuma ke ba ki san masu shege ma suna nuna ma duniya ba? Ballantana ni da ɗan sunna zan haifa"
Dai dai yana buÉ—e mota ya fito sannan ya zo ya buÉ—e mata ya rike hannunta ta fito daidai lokacin da ta ce"Amman ai da kunya tun da kowa ya san abin da muka yi a ka samu cikin ko?
Aji ya kalli Mimi ganin har ta na wani ɓata fuska. Dariya ta kamashi ya kama yi tun da Mimi take da Aji a sanin da ta yi masa a baya da yanzu ba ta taɓa ganin shi yana dariya haka ba.
"Shekaran ki nawa wai? Ai daman kowa ya san sai da muka haÉ—u a ka samar da saduwa sannan kika samu ciki, tunda ba a ruwa za ki sha ba."
 Haka yake faɗa yana mata dariya, kamar za ta yi kuka ta dake shi a kirji shi kuma ya na riketa yana dariya dai dai lokacin sai ga mai motar tare da Auwalu da Gaje a ciki ita ce za ta je. Sai matar Auwalun da Maeesha da Mariya, da Jummai da Zuwaira kowa cikin shirinta, Auwalu ne ya sauko suka gaisa yana gaya masa yaron mai motar ne zai kai su kanon shi yana gida baya jin daɗi, Aji ya kalli direban kafin ya ce"Ka tabbata ya iya mota? matata ciki gare ta ban shirya ɗaukan wannan kaddaran ba yanzu."
Ai Mmi na jin haka ta ja jikinta zuwa wajen su Yaya zuwaira tana gaishesu domin in ta cigaba da tsayawa saita ji abin da zai saka ta ba za ta ƙara kallon Yaya Auwaln ba.
 Tare suka shiga gidan suka iske su Yaya Amina tun ɗazu suna nan suna jiran su, nan a ka gaggaisa sannan sai ga su Auwalun sun shigo gidan tare da Mansoor suka gaida Inna sun shirya daman motan kawai suke jira, Yaya Halima ce ta kalli Aji kafin ta ce"Na ji ana zencen kwana biyu na ce mu fa huɗu za mu yi."
Kai tsaye ya ce"A'a kwana biyu za ku yi gaskiya." Haɗe rai ya yi kada ma ta kara mgana, Ita daman zolayanshi take yi, Bintu ce ta ce a hankali ita sati mijinta ya barta ta yi. Hararanta Mansoor ya yi kafin ya ce" Duk wacce ta ga kwana biyu ya yi mata kaɗan za ta iya ƙarawa amman litini da safe mota za ta koma wanda ya ga zai dawo shike nan.
Haka ya faÉ—a lokaci É—aya yana ficewa Bintu ta tura baki ta ce" An ya in Anty Mimi ta haihu za mu je mu yi sati muna suna kuwa?
Yaya Amina ta ce" Kina da koƙari, in ma ya bari an yi sunan kenan tsab zai ce ba taron suna in dai Baban Inna ne."