← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 93

Sashe 91

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari tun safe suka tafi asibitin da ta ke zuwa, suka samu likitan da mganar Ummi da lafiyan Mimi nan da nan ya ba su shawara ya ce bakomai. Za ta cigaba da shayar da Ummi har sai cikinta ya kai wattani biyar sai ta yaye ta tunda dai akwai rufin asiri Ummi ba za ta wani samu matsala in dai za ta samu abinci mai rai da lafiya da zai gina mata jiki ita da Mimin gabaɗaya, nan ta ke Aji ya ce ya yi alƙawarin sai in da karfin sa ya kare sun baro asibitin bayan ya rubuta ma Mimi maganganun karin jini saboda cikin jikinta tare dan ƴan dokokin daza ta kiyaye kaɗan ba ma su yawa ba, suna hanyar komawa gida Mimi ta roƙi Aji da Allah da Annabi kada ya yi tallar ta na da ciki kamar yadda ya yi da ita a cikin Ummi ganin ta damu ya sa ya ce ba zai gaya ba amman in har aka tambaye shi zai faɗi gaskiyansa ta ce ta ji kuma ta amince.

Har ya koma Abuja yana lallaɓa Mimi ganin duk ta damu,amman har ya koma sai a hankali ba ta wani saki ba fahimtar haka yasa ya ce in ta samu sarari ta ziyarci Hajiya da gidan yaddiko da duk in da take son zuwa kila ko shiga mutane zai rage mata damuwa kamar ko ya sani fita mutanen da ta yi yasa sai damuwanta ta ragu sannan iya bakin ƙokarinta Mimi ta ɓoye cikin jikinta. Ita ce har gidan Nasir da Makama su rana ɗaya ta je musu ranar lahadi tunda ba ta da shiga wajen aiki ranar, kuma in ta dawo daga wajen aiki ta kan sauka gidan Hajiya ko Inna, ko sun gane tana da ciki ko ba su gane ba Oho ba dai wanda ya yi mata wata mgana, amman abin da ba ta sani ba daga Hajiya har Inna Meri sun fahimci Bintar ciki gare ta. Sannan yaddiko ma ta gane lokacin da ta je gaisheta sai da ta ce"Ai yanzu kya yaye wannan katuwar yarinya ko kina so ko bakya so."
Ita ba ta gane ba, saboda Yaddiko ta sha mata tsiyan girman jikin Ummi ya yi yawa ya kamata ta yayeta in ta shekara ko da wattani ne ita kuma ta ce sai ta kai wa'adi, ko da ta yi mata mganar har a cikin ranta ba ta kawo ta fahimci wani abu ba ne.
Ita a tunaninta ba wanda ya sani sai dai in ya fito a ganshi.

Cikin ta na shiga wata biyar ta cire Ummi a Nono, saboda ma kada kowa ya fahimci wani abu ta kasa kaita gidan kowa da sunan ya ye,sai babanta ne da ya dawo ya kwashi kayanta ya kai ma Inna da ya dawo ta tambayesa me Inna ta ce? Kai tsaye ya ce"Ta tambayeni dalilin yaye Ummi ni kuma nace ciki gare ki."
Ai sai Mimi ta saka masa kuka kamar ya daketa ya fara fahimtar wannan cikin mai son rigima ne mgana kaÉ—an ko a waya ne sai ta fashe masa da kuka, tunda ya fahimci yanayinta sai ya koma lallashinta har suka rabu lafiya.

Cikin uan'uwa Mimi ba wanda ya san tana da ciki sai yan Gombe ne da ya fito suka gani, Ita Mommy ta zo garin ta ga Mimi da ciki a gaba ta kama baki, suma yan'uwan Aji haka suka ganta da shi abun Allah kuma lokaci ɗaya ita da Bintu suna da tsohon ciki sannan itama Mariya na da ciki irin wanda ana zuwa a ke tutuɓe da shi a kofar ɗaki, kuma shima wannan cikin tun da wuri suka gama siyan komai Bintu ta rigata haihuwa An yi suna da kwana uku Mimi ta haihu, ta na fara jin naguda ta haɗa kayan haihuwa zuwa asibitin da take awon ta sannan ta kira inna ta faɗa mata sannan ta kira Hajiya kafin ma su zo ta na ɗakin haihuwa , wannan haihuwar dai ta ɗan sha wahala sai la'asar ta sauka wannan karon Namiji ta haifa baki mai kama da uban sak.

Kwana ɗaya ta yi a asibitin suka maida ta gida, Aji sai dai ya ga hoton Baby boy da Mimi ta ɗauki hoto ta tura masa, Ya yi farinciki sannan ya yi godiya ga Allah jin Mimin tana lafiya tun da aka faɗa masa namiji a ka haifa Ya raɗa masa suna IBRAHIM, ita kuma Mimi ta na murnan a saka mata sunan Abi sai da ya dawo ta ji yana faɗin ya yi ma Jariri huɗuba da Ibrahiim,abun na ranta ya sa sai da ta furta masa shi kuma ya ce ai haihuwa yanzu suka fara ta yi kokari nan da wattani kaɗan ta kara samun ciki sai ta haifi Baban nata, Murgaɗa masa baki ta yi ba tare da ta yi masa mgana ba ganin kamar da gayya yake mata mganar, su khadi sai dai suka zo suna suna mai cike da mamakin daman Mimi ciki ne da ita? Shi ne ba su taɓa sani ba Mommy ce kuma da Hajiya su kuma ba su yi mganar da kowa ba, ko Rukky a bakin Aisha Ta Karamchi ta ji Mimi na da ciki ta kirata tana mata tsiya ta samu zuwa suna tunda daman wannan shi ne karon farkonta na zuwa ganin gida.

Shima a sunan Ibrahim wanda za'a riƙa ma alkunya da Babangida, an yi abubuwa sosai kamar na sunan Ummi ma sha Allah, a haihuwan Babangida Aji ya siyama Mimi danƙareriyar sarka gold mai tsada a matsayin tukwaicinta. Sannan ya ce itama mota za ta biyo baya da yardan Allah. Mimi ta ji daɗin wannan kyautar sosai haka ta riƙa nuna ma mutane cikin jin daɗi. Haka dai mimi ta cigaba da jegonta wannan karon Baba uwani ne ta zauna da ita na sati biyu sai ta koma gidan Hajiya ita kuma daman ta iya ta cigaba da Kula da kanta da ƴayanta. Miji kuma sai dai su yi mgana ta waya Aji na neman ya ɓace ma ganinta saboda yanzu duniya ce ta san shi ba jiha ko ƙasa ba.

Mimi na kula da yayanta gefe É—aya kuma ta na kula da kasuwancin ta da yanzu sai habaka yake yi, Aji kuma na can Abuja sai ya samu lokaci zai zo ya ganta amman fa komai na bukatar rayuwa ya tanadar musu ba abunda take nema ta rasa kuÉ—in ta kuma suna account É—in ta. Ba abunda ta ke siya in ba kyauta za ta yi ba,ko ta ga wani abun ta ke so za ta siya ko za ta siya ma yayanta.
Rayuwrta take yi cikin kwanciyar hankali tun tana damuwa na rashin Aji a kusa da su ne har ta fara sabawa tunda ga ƴanuwa lulluɓe da su, ta gama arba'in ɗin Babangida Mariya ta haihu suka sha suna, Ta samu namiji an saka sunan baban mijinta Ahmad, Walida kuma tana kano sai sun samu hutu ta kan zo gida, Inna kuma daman ta saba zama ita kaɗai in kuma tafiya ta kamata ta rufe gida ta je ta yi zumuncinta, ko kuma wani lokacin yaran su Bintu na gidan suna ɗeɓeta mata kewa. Amman Ummi kan sai dai in tare da Mimin suka je gidan Aji ba mutum ba ne da kan bar yaransa su je wani waje hutu ba, ko da gidan Inna kwana in ya wuce ɗaya zuwa biyu sanda ta fi sati ma lokacin da ta yaye sati biyu ta yi da kansa bayan ya dawo ya je ya ɗaukota zuwa gida. Shi ba shi da ra'ayin irin haka ba wai domin yana da wani dalili ba ne.

******

*BAYAN SHEKARU SHIDDA*

Bayan shuɗewar wasu shekaru kamar shidda. A ya yinda Mimi da Aji suke da shekaru goma da aure ƴaƴan su biyar Tunda Mimi haihuwan kusa kusa take yi bayan Babangida ta kara samun mace sai taci sunan Mommy, suna kiran ta da Batul,sannan ta kara yin mace mai sunanta sunan Hajiya kuma wato Fatima suna kiranta Fati ba sa mata alkunya, sai ƙaramin su mai sunan Mu'azzam shima ba sa masa alkunya, duka cikin shekaru goma Mimi ta haifi waɗanan Zzaratan ƴayan nata, tare da gwarzon mijinta Best Nigerian player Mansoor ibrahim Aji wanda ya shahara ya samu ɗaukaka ba iya kasar mu ta Nageria ba, ya kutsa kasaahen ketare sun buga wasa manyan kasaahen duniya ma sun kutsa sun buga cikin kwararun manyan yan wasan kwallon kafa, kama daga manyan manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasashen ketare sun yi wasa da su. Sannan sun ta kawo masa hari domin hayarsa ya koma turai buga wasa ya ce har Abada shi sunan shi Aji Ajin kasar ne shi ba Ajin turawa ba, shiyasa an kasa siyan shi ballantana ya bar kasar sa ya koma wata ƙasa.

Sun buga easa tun daga Nation Cup da sauran manyan mamyan wasanin FIFA, a yanzu a kungiyar kwallon kafa ta ƙasa mai suna Super Ealges ba kamar ɗan wasa irin Mansoor Aji, tunda sannanun duk sun yi ritaya su Ahmad Musa, shi ne kuma ke rike da muƙamin Captain da ya samu wannan matsayin saboda shin ɗin Dodo ne a Filin wasa sannan ƙwararra ne wanda ya samu kyakyaawan ƙwarewa. A yanzu a Nageria Mansoor Ibrahim Aji ne fitattacen ɗan wasan kwallon kafa da ke kan gaba da kowa cikin shekaru kusan ashirin da ya kwashe ya na buga ƙwallo ya na da shekaru arba'in da huɗu a yanzu amman sai kace ɗan shekara talatin ne saboda hutu da jin daɗi da kuɗin da suka zauna masa, Mansoor Aji ya na da kuɗi da bai san iyaka ba, kwallo yake yi kuma ita ta raa masa. Duniya ce ta san shi ta dalilin kwallo ya taka kasaahen da bai taɓa tunani ba sannan ya buga wasanni da ƴan kwallon da a baya sai dai ya gansu a hoto.
Chapter 91 · 0% Book details