← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 93

Sashe 79

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Mimi na gefe ta na jin su tana yar dariya, ba ta ce komai ba, Yaya Halima ta ce"Duk fa wannan muzurin saboda matarsa ne, kada mu kara kwana a barshi a gauro."
GabaÉ—aya suka saka dariya Bintu har suna tafawa da Yaya Amina.
Mimi ta harare ta kafin ta ce" Har da ke ko? Zan gaya masa."
Bintu ta tsuke baki tana faÉ—in" Ni ban ce komai ba, ba ruwana."
Suna cikin mganan ne Auwalu ya leko ya ce su fito su Yaya Zuwaira daman suna tsakar gida Maeesha ne kawai tare da su, Mariya da Walida yan zumuɗi suna kofar gida wajen mota su Auwalu suka fiffita da kayan a ka saka a booth, sannan a ka tsara tafiyan Aji shi ya saka Mimi a gaban mota ita da Mariya tunda ba ta da jiki, Yaya Jummai ta kaɗa baki tana faɗin"To ai da baya ta dawo,  ko ka saka Bintu madadin Mariya."
Kai tsaye ya ce"A'a Bintu za ta matse ta, kuma ni ina so ku kula da ita ne, juna biyu gare ta fa"

  Kunya kamar Mimi ta nutse kanta ta sunkuyar Yaya Auwalu ne a ka bari da faɗin" ƙwarai kuwa, ku kula da matar yallaɓai dakyau."
Gaje ce ta ce" Kada ka damu Baban inna  zamu kular maka da matarka da abin da ke cikinta in sha Allahu."
Suna ta masa dariya shi kuma ya haɗe rai, Mimi ko kunya ta rufe ta wai har ya na ma direba warning cewa kada ya yi gudu ya bi a sannu matarsa juna biyu gare ta har yana cewa"Ita ce komai nawa, ka bi su a hankali don Allah ban da gudu.". Direba na dariya yace"In sha Allahu Yallaɓai "
Inna Meri ma har kofar gida ta rakosu,  tana musu fatan Allah ya tsare, baya mutum huɗu Gaje da Jummai da Zuwaira, sai Maeesha. Kujeran tsakiya kuma Yaya Amina da Yaya Halima sai Bintu, sai Walida da a ka gyara ma inji sauran kujeran za'a biya Tudun wada a ɗauki mutum ɗaya daga gidansu Hibba.

  Suna ɗaga musu hannu tare da fatan su isa lafiya, Tudun suka biya su ka ɗauko Zaliha ɗiyar ƙanwar Maman Hibba ne sai bayan sun dau hanyar kano Nafisan Nasir ta kira Mimi ta ce ba ta san sun shirya tafiya ba, Nasir ya barta da ta zo. Sai mimin ta bata hakurin itama ta sha'afa ne ba ta mata magana ba, amman wai Nasir ɗin ya yi ma Aji mgana shi kuma wannan tuni ya manta ma.

  Direban ya ji mganar Oga Aji bai yi gudu ba amman sun isa wajajen uku ne na rana. Shi kan shi Aji ya yi mamakin saurin su haka yace ma Mimi da suka yi waya. Murna wajen Hibba da Mu'azzam ba'a mgana, suka rasa ina za su saka su saboda murna sun iske wasu daga cikin ƙanen Hibba da yayenta sun riga su zuwa tun jiya suke. A ka rasa ina za'a saka su kawo wannan miko wannan Sun rasa bakin godiya ga zuwa ga abun alheri Mu'azzam sai da ya yi ƙwallah domin Yayan nasa ya gana mishi komai bayan kudin da ya tura masa ya biya kuɗin mota sannan ga ɗawaniyar kayan suna da kuɗi, ya kira shi zai masa godiya ya kashe wayarsa. Ba su zauna ba da yamma a ka fara aikin suna raguna biyu a ka yanka ma Maryama da safiyar suna. Sannan sun dafa shinkafa sun yi alale da Zoɓo an kuma soya kayan ciki bayan haka kuma ga nama ya siya ɗanyen an yi girki da shi, a ranar Mimi ba ta samu fita ba sai washegari ranar lahadi Bintu da Walida tare da mariya suka rakata gidan Dr ta fara zuwa baya nan ma yana asibiti sai dai Jawahir nan suka yi sallar la'asar sannan suka wuce soron ɗinki, Inna Zainaba sai da ta mata tsiyan ta ɗauka za ta kwana ne amman sai ta ce washegari za su koma gabaɗaya, suna can har dare sannan a ka saka direba ya dawo da su gida.

  A ranar daman su Yaya Amina suka soya Nama a ka diɓar musu na su a daran. Na Inna daban haka na Baba sai sauran kuma a ka haɗa su gabaɗaya. Amman na Baban inna roba guda cike da nama in ji ɗan'uwansa, misalin sha biyun rana direban yazo amman sai da suka yi azahar suka ci abinci shima yaci sannan suka ɗauki hanya nan suka bar ƴan'uwan Hibba su sai jibi za su koma anman ƙanwar mamanta na nan sai ta yi arba'in.
Sai mangariba suka iso gida, gidan Inna su ka yada zango, nan suka raba naman kowa ya É—auka na shi, sannan Mu'azzam ya ba su kwalin omo da sabulu yace su raba gabaÉ—aya.

  An raba amman Mimi ba ta amsa ba, Naman ma cewa ta yi su haɗa ma Inna sabulun kuma ta ba ma Jummai omon kuma ta ba ma Yaya Zuwaira su sun fita bukata.
Yaji jegon ma an ba su wanda ƴan'uwanta su ka mata sun raba gabaɗaya. Zuwa bayan isha'i kowa ya yi gidanshi inna ta diɓar ma Magajiya naman da Yaji ta ba Mariya ta kai mata, Gaje ma har na Harira an ɗiba mata ita daman Inna an san rabar da shi za ta yi kila ma ko a bakinta sai an yi da gaske za ta ɗanɗana.

  Mimi dai nan ta jira Aji ya zo ya ɗaukota da daddare suka tafi gidansu, daman a daddafe ya yi kwana biyun nan. Washegari ma ba ta samu zuwa wajen aiki ba sai ranar laraba ta koma.Miyan ma da ta yi masa ko sau ɗaya bai yi amfani da ita ba. Ya dai ci cake da samosa, itama ya ce domin ya na so ne yasa ya soya ya ci, da tace ina ya ke cin abinci ya ce gidan Inna da ta gama za ta kira shi ya je ya cika cikinsa, ina zai iya wani Dafa shinkafa bayan ta gama sangarta shi..
In da Allah ya so ta da rahama ba ta yi mugun laulayin da zai hana ta aikace aikacen da kuma biya ma mijinta bukata ba ko amai ba sosai take yi ba bar ta dai da cin goro sai kayan kwalama suma ba kasafai ba. Cikin fari ne amman Alhandulillah ta same shi da sauki fiye da tunaninta, fatan ta Allah yasa yadda ta samu laulayi da sauki ta samu haihuwan ma cikin sauƙi.

******

*BAYAN WATTANI BIYU..*

Har Hibba ta yi arba'in ta zo gombe ta yi sati ta kawo ma Inna takwaranta wacce suke kira Ammi. Mu'azzam ya zo ya É—auke ta suka koma gida, cikin Mimi kuma watannin shi shida ne, har ta fara zuwa awo a wani asibitin kuÉ—i a cikin gari tana kuma cigaba da zuwa aikinta.
Cikin ya bi jikinta tunda tana da tsawo sai da ya saka ta buɗe daga kasanta saman ta kuma mamanta sun yi manya kumatunta ya kumbura sannan hancinta ya ƙara girma tuni dai halittar ya sauya. Hajiya ce ta gaya mata cikin jikinta ya bi shi ya sa ba'a ganin girmansa, shi kuma Aji ya ce ta zauna a haka ta fi masa kyau a koda yaushe ya kalleta ya na jin farincikin yau ita ce ke ɗauke da cikinsa wannan ma abun alfahari ne.

  Zaman su suke yi lafiya cike da kauna sai ɗan abun da ba'a rasa ba. Tun da daman shi zamantakewa zo mu zauna ne zo mu saɓa ne, sai dai suna ƙokarin Fahimtar juna domin samun daidaito. Shi yanzu babban Blburin shi shi ne ya samu ya biya ma Inna ta je makka ta sauke farali, ga shi Contart ɗin shi saura shekara biyu ya ƙare a Gombe United amman bai yi tunanin yi ma kansa wani tanadi anan gaba, ya samu kuɗi tunda a wata ɗaya sun je kano da kaduna sun buga wasa bayan albashinsa akwai allowense. Sannan kuma mganar Contrart din Captain din Team an saba daga waje akan ɗauko wani a ba shi horo amman wannan karon sai ya samu Coach ɗin su da maganar ga Musa pele a cikin su yake yana da ƙokari tunda shi ne kamar matsayin Assitancen ɗin Aji, yace me zai hana shi a ba shi horon.?

  A lokacin kallonsa Coach ɗin na su ya yi kafin ya ce"In contart din mu ya ƙare, ka shirya in da za ka koma ne?
Sai Aji ya ce"Tukunna dai Coach."
Sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Ba na so ka bar mu, kuma ina son cigaban ka ina inan ina yi maka wani ƙokari in ya tabbata zan neme ka, in kuma bai tabbata ba sai dai mu ƙara singing ɗin contart ɗin da kai amman ba zan bari Gombe United ta yi rashin zaƙwaƙuru irin ka ba."
Ya daɗe daman ya na jin Coach na yawan faɗin ya na masa jokari bai taɓa maida kansa ba, ballantana ya yi tunanin makomarsa anan gaba, shi kam me ya ke nema? Komai ya samu sai dai godiyar Ubangiji kawai mutum ne shi da ba shi da hange hange, saukaƙƙiyar rayuwa ce a gabansa ya yi ma iyalansa sannan ya farantama Iyayensa..
Chapter 79 · 0% Book details