← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 93

Sashe 45

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan komawrarta gida ba daÉ—ewa ta haihu samu mace kuma Saddiqu ya ce sunan Magajiya zai saka ma Æ´arsa, asalin sunan Magajiya Mardiya ne da farko ita Maeeshan ta É—auka Magajiyan ne sunan har ta fara bala'in ba mai sakan ma Æ´arta suna Magajiya sai daga baya ta ji sunan ashe Mardiya ne sai ta koma ta yi laushi, An yi suna na karya da garari duk abin d Saddiqu ya ce ba shi da shi sai Maeesha ta ce bashi ne aka ci zai biya daga baya, Ita kanta Magajiya sai da ta raina kanta ta kuma gane amfanin Meri da uaÆ´anta a tare da su da ace suna gidan komai na sha'in taron suna da kuÉ—i ba zai yi mata wahala ba, itama ta yi taron suna a nan gidan amman dakyar aka samu a ka yi fate, Auwalu ne ma ta samu dubu goma a wajensa zuwaira biyar amman Jummai tana nema itama. KuÉ—in da za ta haÉ—a ma a siya zannuwan suna ba ta da shi sai da ta ci bashin Atamfa da rigar yarinyar sai Inna Meri itama ta yo turmi, sai da Bintu ta hana ta amman ta ce ba ruwansu ta kuma matsa musu suma sai da suka leka sunan nan gidan Wanzamai daga nan suja wuce gidan su Maeshan.

Har Gaje na yi musu tsiyan tunda Inna ta bar gidan suka daina ganinsu, Yaya Amina ce ma ke ba da hakuri amman Bintu cewa ta yi" To me za mu zo mu yi muku? Tunda daman wacce muke zayan domin ta kun kore ta daga gidan? Ai ita ce mu , mune ita dole ko ku daina ganin mu ai ga gidan nan mun bar ma masu gidan sai su haɗa duka su yi ta zama har ranar busa ƙaho."
Saboda su Zuwaira ta yi mganar su ma dai ba su tanka ba. Sai ga shi ko Kunya Zuwaira ta ja Yaya Amina gefe ta na mata mganar, In sun zo da abun suna don Allah su kawo a haÉ—a anan ana haÉ—a na dangin uba ne daga bangaren su, sai Yaya Amina ta ce bari ta yi ma su Halima magana.
Aiko dai Halima ce kaɗai ta ba da 5k, Daman ita Yaya Amina rigar ƴarinya ne da kuma pampers, Bintu kuma da Yaya Amina ta yi mgana sai ta ce ita kam ba ta da shi kuma ba za ta matsa ma kanta ba ashe sai yanzu aka san su ma ƴanuwan Saddiqun ne ƙiri ƙiri kuma su san tana da shi amman ta ce ba ta da shi dole suka ƙyaketa sana'ar saida ruwa take yi da zoɓo amman Bintu kafiya gare ta abin da ba ta yi nyya ba, ba mai sakata dole.

Sai ga shi tafiya ma can gidan mai jegon Jummai ta ce su jira zuwa la'asar su tafi gabaÉ—ayansu sai a tafi da kayan gabaÉ—aya shi ya sa suka jira, Inna Meri daman ba ta zo ba tana gida tare da yara. Su ne sai wajen biyar da wani abu suka isa gidan su Maeesha suka iske a na ta shan DJ.
Mai jego ta ci gayu har da mai kwalliya ta ɗauko da mai hoto sannan sun yi abinci mai rai da lafiya har da Alala da zoɓo an tarbesu dai sama sama sai da ma suka buɗe kayan da suka kawo ne sannan suka ga ana ta duban juna ana taɓe baki, Atamfa biyu ce cotoon ɗaya ɗayar roba ce sai rigar ƴarinyar guda uku da sabulan wanka da Pampers ɗin Yaya Amina, kuɗin kuma ba su san ina a ka siya fallayan zannuwan guda biyu wai Mejego sai ta yi goyo da shi, Gaje ce ke kora wannan bayanin Amman ko alama ba su ji daɗin wannan kayan ba ko godiya nan in da suka sauke kayan nan aka bar su kamar sun kawo kashi Binta na ta dariya ƙasa ƙasa ga shi kuma Walida abokiyar gulmarta tana wajen koyon Computer, Mariya dai daman a gidan ta kwana tun jiya ta na can waje cikin ƴan rawa anman ta zo ta gaishe da su Yaya Amina har ta na zolayanta da Amarya tunda an saka ranar auranta Shekara.

Ko Jaririyar ba'a ba su sun ɗauka ba sai da Yaya Halima ta yi mgana sannan Maeeshan ta kawo musu. Su kuma aka fi ma sakar ma fuska tunda an gan su sharr ba wahala a jikinsu barin ma Bintu da take ta wani shan ƙamshi ko gaishe da mejegon ma ba ta yi ba, ana ta gulma dai a gidan ana raɗan su waye su Bintu? Maeesha ta ce ƴayan Inna Meri ce ta bangare da ta koma matar da ta zo ta yi ma Jinjira wanka ta mata gashi, Domin Inna Meri ranar da ta zo barka har Maeesha sai da ta ji kunyar abin da ta aika mata nuna komai ba komai ta yi ba ta zage ana ta hidima da ita a lokacin yarinyar tana kuka ashe xibiya ce ba a yi gashi ta kume nan fa ta ce a saka ruwan zafi ta zauna tana ta ga shin cibiya sai ga Yarinyar ta yi shuru tana raba ido washegari kuma ta dawo ta kara yi mata ta shafa mata wani mgani a daran cibiyan ta faɗi. Sannan tunda aiki a ka yi ma Maeesha sai ta ba su shawaran kada ta yi wanka ganyen yanzu sai zuwa gaba amman a riƙa yi mata da towel kada jikinta ya ɗanyan ce amman ta ce a riƙa ba ta abinci sosai kuni da ruwan shayi tana sha saboda shi zai taimake ta. Uwar Aishan ta ji daɗi domin ita ce yar fari ba sanin haka ta yi ba.

Kafin su bar gidan nan sun ga abu har hoto ma suna gani ana yin hotuna ba wanda ya gayyace su, Bintu ce ma da shegen neman mgana ta shiga hotunan bayan ta ɗauki Jaririyar ta rike su Zuwaira dai sai rakuɓewa a gefe kamar wasu almajira shi ya sa ana kiran sallar mangariba suka yi musu sallama daga gidan suka rabu, Yayan Inna Meri can suka koma gidan ta saboda ɗauko yaran su Zuwaira kuma suka yi gidan Wanzamai suna ta ƙananun mganganun wulakancin da aka yi musu suka koma ma da Magajiya abin da ya faru, To me za ta ce? Baba Danjuma ma ko sisi bai ba da ba ya ce ba shi da shi yanzu ta fahimci in ta cika ma matsa masa sai ya hau masifa yana maganganu, Kamar kada Inna Meri ta bar gidan shik enan ta koma ta yi sanyi kamar ba ita ba.

Saddiqu daman ya gaya mata duk kuɗinsa sun kare wajen aikin nan da aka yi ma Aisha, Duk abin da ma za ta yi na suna ya ce ta ci ba shi abinci ma da sauran su duk iyayenta ne za su yi da kuɗin su. kudin aikin ma sai da ya Kira Mu'azzam ya taimaka masa da 100k tunda an ce za'a yi aikin amman ba shi da ko dubu 20 dole dai ƙanwar naki ƴaƴan Inna Merin da suka ci ma mutumci sune su ke tallafe da su, Shi kuma Baba Danjuma ya koma gefe kawai ya saka ma Magajiya ido daga ita har ƴayanta ya ga in da hassada za ta kai su.
Shi har Allah Allah yake yi kwanakin girkin Inna su shiga in ya tafi can ya fi samun kwanciyar hankali da natsuwa, in ko yana wajen magajiya ko fara'a ba ya y. Saboda Magajiya tun da ya aureta bai taɓa samun kwanciyar hankali da ita ba ko da yaushe masifa da bala'i.

****

Ana azumi saura kwana huÉ—u Mansoor ya koma gidan Hajiya Wajen Mimi, ya iske Yaddiko ta zo duba Hajiya da ta ganshi sai da ta ce ma Hajiya" Sun daidai ta kenan?
Hajiya ta ce"Eh, tace bayan sallah za ta koma in sha Allahu." Yaddiko ta ce ya fi mata tunanin kashe auran da take yi,Hajiya tace daman ba da gaske ba ne duk shegentaka ne.

Yau bai wani jima sosai ba. Ya dai kawo mata zanen da mai zane ya yi na tsarin gidan ta ce komai ya yi yana faɗa mata har an fara saka doundiom in sha Allahu za'a gama cikin wata ɗaya da wani abu tunda akwai kayan aiki, abincin ma da ta yi masa sai dai ta kwashe masa ya tafi da shi saboda ana jiransa ne za su yi meeting a Camp, Ita daman Mimi da Rukky kaɗai take shawara kuma itama ta ce duka tsarin Mimi ya yi dai gwwra dai yasan yanzu mai daraja zai ɗauka, bayan Rukkyan kuma ba ta gaya ma kowa ga abib da ke faruwa ba Hajiya dai ta yi mgana da Mommy ta kira ta itama ta gaya mata sai bayan Sallah Saboda ginin gida haka ma ta gaya ma Daddy da ya zo gidan sai ya ce ai Mansoor ɗin ya kira shi sun yi magana, sannan ya ƙara da cewa"Ki yi hakuri Mimi kin ji ko? Kin ga ribar hakuri ga shi yanzu gidanki ke kaɗai yake ƙokarin samar miki, shi ya sa akace komai mai wucewa ne"
Chapter 45 · 0% Book details