← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 93

Sashe 49

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dukkansu suka kalli juna kafin bahaushen ciki ya kalli Mimi lokaci É—aya yana faÉ—in" Captain kike nufi?.
Sai ta gyaÉ—a musu kai lokaci É—aya tana faÉ—in" Yana ciki ko?
Sai ya ce"Eh bai daÉ—e da shiga ba, amman ya san da zuwan ki?
Sai Mimi ta girgiza kanta lokaci É—aya tana É—aukan wayanta a hannunta.

"Bai sani ba, ina ta kiran shi bai É—auka ba."
Tana faɗa tana rubuta masa saƙo.

"Ina bakin get É—in Camp É—inku.."

Haka kawai ta rubuta masa. Dai dai lokacin taji wani cikinsu na faÉ—in" Bari mu kira wayar É—akin sa, wa za'a ce masa? Tun da akwai telephones a cikin Camp wajen guda uku da na reception da na É—akin Aji da na meeting room É—in su.

"Mimi.."

Sunanta ta faÉ—a musu. Sai ta jira a cikin mota ta na ji suna mgana a Telephone amman ba ta jin me su ke faÉ—a ba.Ta ga dai É—aya daga cikinsu ya zo ta gefen tagar motarta dake ke buÉ—e yana faÉ—in" Ki shiga ciki Hajiya.".
Sai ta amsa masa da kai dai dai lokacin dayan ya buɗe mata get ɗin ta shiga ciki saboda ba ta san yanayin wajen ba sai ta rasa ina za ta yi fakin. Dole ta tsaya a bakin ginin wajen da aka sake rubuta GOMBE UNITED CAMP. Ta Fara waige waige kenan kamar suna jiranta sai kawai a ka kawo wuta wajen ya gauraye da haske, sai kawai ta fito daga cikin motar da wayarta a hannunta sai dai wajen tsit sai kukan tsuntsuye haka ta rika juya ido tana bin cikin wajen da kallo. Kai wajen fa ya haɗu dole Aji ya riƙa zuwa nan domin za ka ssmu cikakken natsuwa.

Ba ta san daga ina ya fito ba kamar dai Kila ta bayanta ne ta ji dai mgana kawai a saman kanta.

"Me ya sa kika zo nan?

Da sauri ta juya yana tsaye daga bayanta yana sanye da riga da wando saukakku, fuskar nan tasa a haɗe kamar bai taɓa dariya ba, tana ganinsa ta sauke Ajiyar zuciya sai kawai ta buɗe mota ta ɗauko kwandon abincin lokaci ɗaya tana faɗin" Ga abin da na kawo maka."
Ta faɗa tana ƙarisawa gabanshi. Juyawa ya yi kawai ya fara tafiya yana mai faɗin" Me yasa ba ki ba ma saurayin na ki ya cinye ba?
Ba ta yi fushi ba haka ta bi bayan shi da sauri tana faÉ—in" Aji mana. ka Saurare ni ne mana, Yayana ne fa"

Bai juyo ba ya ce" Yayanki guda É—aya na sani. Dr Sulaiman bayan shi ban san kina da wani Yaya ba."

"Cousin Brother É—ina ne. Jaheed ne Son É—in Daddy."
Cak ya tsaya. Har ta kusa cin masa kafa fuskarta ta daki bayansa yana juyowa ya ga
ga kwandon hannunta na neman faɗuwa da sauri ya saka hannu ya karɓa lokaci ɗaya yana faɗin "Oh muharraminki ne da zai riƙa taɓa jikin da ni kaɗai ne nake da ikon taɓa shi? Ko kuma ya dace ki tsaya da shi ba mayafi a jikin ki duka suran ki ya bayyana wanda ni kaɗai ne shari'a ta ba ni damar ganin ki a haka. Wato shi kin yarda ya ganki a haka ya kuma taɓa jikin ki ni kuma da shari'a ta ba ni wannan damar ba ki taɓa yarda wani abu ya shiga tsakanin mu ba ko? Me ki ka mai da kan ki ne Fatima? So kike yi ki kasheni lokaci nq bai yi ba ko? Kin san yadda zuciya take yin kuna? Kin san cewa hoton ku ya kasa ɓacewa daga tunanina? To in ma ya na tunanin zan rabu dake ne ya aura to ki gaya masa ya farka daga wannan nafarkin nasa domin ba zai taɓa zama gaskiya ba, ke ko mutuwa na yi ki ka sake aure Allah ya isa ban yafe ba."
Haka ya faɗa cikin fusata Idanuwansa sun kada sun yi jajir, Mimi ta zaro ido tana kallon shi jin mamakin kalamansa a ina yasan cewa Jaheed na sonta.? Kuma wai Allah yas a ko bayan ransa in ta ƙara aure.

Ba ta samun zarafin mgana ba ya kuma juya kawai ya fara tafiya zuwa wajen motar ta lokaci É—aya yana faÉ—in"Ki koma gida dare ya yi"
Tura baki ta yi kafin ta ce"Ni a'a sai ka ce ka haƙura." Banza da ita ya yi har suka karisa wajen motar ta ya buɗe baya y sakaa mata kwandon abincin lokaci ɗaya yana faɗin" "Ba na son gaddama, ki shiga mota."
Yadda ya yi mganar ya sa ta san ba wasa Idanuwanta suka tara kwallah a sanyaye ta ce"Ka yi hakuri ba abin da kake tunani ba ne.' Wani kallo ya yi mata da yasa ta buÉ—e bangaren direba ta shiga ta zauna kafin ta kalle shi a marairaice tana faÉ—in" To ka yi hakuri ka É—auki abincin"
Kansa ya kauda da sauri kamar za ta yi kuka ta ce"Ni na girka fa da kaina don Allh kada ka ce a'a ka ji."
Sai ya ɗan kalleta da sauri ta ƙara shagwabewa kafin tac e"Don Allah na ce fa"
Tana gani ya sauke numfashi sannan ya buÉ—e bayan motar ya É—auko kwandon abincin dai dai karisowam wani matashi ya na tafiya ne da alama dai ya fito shan iska ne sai Aji ya kira sunan shi.

Da sauri ya ƙariso Cikin ladabi yana faɗin" Barka da dare Captain"
Kwandon kawai ya mika masa lokaci É—aya yana faÉ—in" Ka saka min a cikin É—akina."
Da sauri ya amsa amman yana leƙen Mimi a mota akwai haskem wuta ya gane ta tabbas Matar Captain ce ma'aikaciyar gidan tibi ya na tafe yana faman waige ya ƙosa ya je ya kai sakon ya shiga group chart ɗin su ya kai ma su Zinder labarin yau matar Captain ta kawo masa ziyara a cikin Camp. Shi ko sai da ya ga kabiru da suke ma laƙabi da pele ya wuce sannan ya zagaya ta bangaren Mimi kai tsaye ya ce"Fito.."
Ba musu ta fito, shi kuma ya shiga mazaunin direba ya zauna lokaci É—aya yana faÉ—in" Sai na ce ki zagaya ki zauna?
Da gudu Mimi ta zagaya tana mirmishi ta shiga bangaren mai zaman banza ta zauna

"Seat belt"

Da Sauri ta saka nata, shi daman ya zura na shi sannan ya ta da motar tunda daman key din na jiki. Tun da ta fahimci gida zai kaita ta ke ta faman mirmishi a sannu sannu har zuwa bakin get shi ya leka ya yi mgana da Security suna ganin shi ne suka buɗe mishi get suka fita suma suna gulmar kila madam ɗinsa ce domin tunda suka fara aiki a wannan wajen ba su taɓa ganin mace ta zo wajensa ba sai dai maza, suna tafe a hanya amman ba wanda ya yi ma wani mgana Mimi ce ta ga kamar ya na fushi da ita har lokacin ta kara narke murya tana ba shi hakiri kanzil bai ce mata ba har ya kai ta gida har cikin haraban gidan sai da ya yi parking Sannan suka fito a tare.
Key ɗin motar ya mika mata ookaci ɗaya ya na faɗin" Kada ki ƙara cewa za ki tuka mota da daddare, in kika haɗu da miyagu fa?
Kanta na kasa ta ce" To ba kai ba ne ka tafi kaba fushi da ni ba"
Kamar za ta yi kuka. Kallonta ya yi kafin ya tura mata key din motarta ta saka hannu ta karba sannan ya juya kawai ya wuce ta bi shi da kallo, da sauri ta bi shi tana faÉ—in" Kana da kuÉ—i a hannunka ne?
Juyowa ya yi ya kalleta kafin ya nuna mata hqnnu cikin kaushinsa yana faÉ—in" Ki koma ciki gida Fatima."
Yadda ya yi mganar ya sa dole ta juya tana tafiya a sannu har falon Hajiya amman sai da ta laɓe tana lekensa su ka yi mgana da Megadi sannan ya fita ya bar gidan.

Sannan ta sauke ajiyar zuciya tana juyowa ta ga Hajiya zaune taba gyanyadi ta kuma san zaman jiranta take yi. Sai ta yi mirmishi sannan ta ƙarisa wajenta tana tashinta Hajiya ta farka sai ta ga Mimi da sauri ta ce"Binta kin dawo?
Sai ta riƙe Hannun Hajiya ta miƙar da ita tsaye lokaci ɗaya tana faɗin" Na dawo Hajiya, ki kwantar da Hankali Aji ne ya dawo da ni gida."
Hajiya ta jinjina kai ba ta yi mgana ba. Sai Mimi ta riketa har zuwa cikin É—akinta ta kwantar da ita kan gado Hajiya na faÉ—in, ki samu wani abi ki ci Binta kin yi azumi ba ki ci komai ba."
Sai ta amsa mata. Nan ta bar Hajiya ta koma ɗakinta ta cire kaya ta yi wanka da sallar Isha'i sannan ta fita falo zuwa Kitchen ta diɓo abinci da kayan marmari Baaba Uwani ta jima da shiga ciki, sai da ta gama cika cikinta ta sha zobon da ta yi sannan ta koma ɗaki ta ɗauki waya ta kira Aji amnan bai ɗauka ba, so take ta ji ya koma gida lafiya?
Chapter 49 · 0% Book details