← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 93

Sashe 20

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amman tunda ta tura masa saƙon wai ta samu wani. Ya ji kasa sukuni maganar ta ƙi barinsa ya zauna Lafiya barcin sa ma ragagge ne. Baƙin kishi gare shi shi fa a tsarin rayuwarsa in har ya riga matarsa mutuwa Allah zai bar wasiyyan in ta sake aure bai yafe mata ba, ba zai iya ɗaukan wannan kwamacalan ba a ce in da ya shiga ya yi nomansa wani ya shiga ya ba za ta shi hajar ba zai iya ɗaukan haka ba. Ballantana yana raye a duniya nan Mimi ta je tana kula wani, ya fara tunanin waye ta ke nufi? Ko dai wannan sakaran ɗan'uwan nata ne? domin ai ya san labarin shi a bakin Makama In ko hakane lalle daga Mimi har iyayenta zai ɗaga musu hankali. Sannan ko da ya ce ba zai ƙara nemanta ba ya kasa, ya sake kiranta amman wayarta a kashe amman bai haƙura ba, karin abun ma ko barci yake yi sai ya riƙa mafarkin ya ga Mimi da wani ta na ta masa dariya, a kwanaki nan barcinsa duk babu salama da sukuni a cikin sa.

Duk yadda ya so ya nuna bai damu ba ya kasa damuwar har ta fara bayyana a saman fuskarsa baya samun cikakken barci haka za ka ganshi zuru zuru,  duk kauce kaucen sa na kada a fahimci Mimi ta ci nasara a kanshi ya kasa. Duk kuma tunaninsa na ya share ta shima ya kasa tuni zuciyarsa ke rinjayansa ya bi ta can kano, wata kuma zuciyar na hana shi, amman kuma wata na tunkuɗa shi saboda samun natsuwar shi, Ga shi har a Lokacin Inna sama sama take yi masa ya bata hakuri bai san adadi ba sai ta ce ita bai mata komai ba, ya yi mata maganar Mimi ya ce ta kwantar da hankalinta za ta dawo kai tsaye ta ce masa wannan kuma abin da ya shafi rayuwarsa ne ita nufinta ta fita a ciki, In ya neman masu mai faɗa ne ya nemi dangin ubansa ita kan ta gaji da bin bayansa ba shi kaɗai ta haifa ba. Har Baba Ɗanjuma ya gaji da yi mata mgana ta kafe ta ce ita wlh ta yafe masa ɓacin ran da ya saka ta amman kuma ta ƙi ta koma masa kamar baya.

Yana ma dai zuwan gidan ne domin ya zame masa dole amman ba ya jin daÉ—in gidan kwata kwata. Sai dai saboda Junior in ya je gidan da ya gansa zai É—ane shi yana murnan ganinsa in ko ya ce zai fita da shi Inna ta fara faÉ—a kenan ta ce in nesa zai yi ka da ya fita da shi, Shi dai ai na shi ban hakuri ne sai dai ya je ya yi yawo da shi cikin Camp É—in su, Ko kuma ya yi yawo da shi acikin mota ya na siya masa kayan kwalama da kuma kayan wasa.

Ya so cikin satin da zai shiga ya je Kano duk da baya samun wayar Mimin amman hakan bai samu ba  baya samun shima lokacin kansa, wani girma ne Allah ya ba shi a sanadin wannan kwallon kafa. Matasa matasa dake Gombe da zagayenta suna yawan zuwa wajen sa neman karin bayani ko wani taimako,  duk da shima ya dan ƙwallo ba ra'ayinsa ba ne sannan ba burin shi ba ne, amman tunda abin da Allah ya zaɓa masa kenan sai ya rumgume shi hannun biyu, tunda shine komai na shi yanzu komai zai zama ko ya zama a wannan rayuwa sanadin wannan sana'ar ne a farko bai wani ɗaukesa da wani irin Muhimmanci ba amman daga baya sai ya rike abun ya san Allah ne ya yi masa kyakyawan zaɓi ta hanyar da bai za ta ko tsammani ba.

Har satin ya ƙare. Bai samu yanke shawara ba, a satin kuma da ya shiga suna da traninng saboda watan gaba suna da buga wasa, to duk ba ya samun zama sannan Baba ma ya kira shi kan maganar Walida da Mariya ya ce zai shigo gidan su yi mgana.
Abin da ya sa ma ya yi musu shuru ba su ci Jamb ba, ya na tunanin su jira wata shekara su sake rubutawa, sai su tafi jami'ar Gombe kamar yadda ya yi ra'ayi duk da ya san Baba aure yake so su yi saboda tsarin gidan wanzamai kenan ba'a dogon karatu a gida.
Suna mgana da Mu'azzam shi dai ya damu ya zo kanon nan ya yi bikon Mimin sai ya riƙa nuna masa zai yi tunanin har a lokacin bai gama gaya masa ga abunda ya yanke ma ransa ba., daga baya kuma sai ya ce ko ya na son zuwa ba shi da mafita tunda wayar Mimin tana kashe ne ta ina zai iya sanin adireshin gidan yayan nata.
Sai Mu'azzam ya ce ya na da lambar Dr. Sulaiman saboda tun a wajen ɗaurin auran shi suka karɓi lambar juna tun wata hira da ta shiga tsakaninsu ya gaya masa a kano ya ke aiki, to tun a lokacin ayyuka ya sa ba wanda ya neme wani a cikin su.

Mamaki ya kama Aji cikin É—an shan kunu ya ce"Me kuka haÉ—a da su da kake ijiyar lambobin su?
Mu'azzam na dariya ya ce"Mun haɗa mana, tunda Yayana na auran ƙanwarsa ai an zama ɗaya in sha Allahu"
Uhm kawai yace domin ya ga Mu'azzam ne da Kalan dangi,  har ya na cewa kada ya damu zai raka shi gidan in ya zo kanon,  shi kuma ya ce bai saka shi ba, kuma ya ƙi gaya masa ga lokacin da zai zo ya ce kuma in ya dame shi zai fasa zuwa daga nan Mu'azzam ya kama bakin shi. Bangaren su Nasir da Makama sun yi fushi sun ce in dai Aji bai ba su haƙuri ba to ba za su haƙura ba.
Mu'azzam ya ba su haƙuri a madadin sa amman Nasir ya ce ya fita a wannan faɗan ba ruwan shi, shi ko gogan ya manta da abin da ya faru suna can sun ɗaukan ma kansu da Mu'azzam ya kara mgana sai cewa ya yi wani abu daman ya faru ne? Ya fahimci Nasir ya koya ma Makama banzan halinshi, shi yana da abubuwan da suka sha masa kai ba shi da Lokacin tunawa da abin da ya faru in kuma suna jiran ne shi ya Kira su ya ba su haƙuri alhalin shi dai bai san ya yi musu laifi gaskiya su yi ta jira. Suma ɗin fa su san halin shi kawai saka ma rai wahala ne amman Nasir na kira Mu'azzam ya ji ina aka kwana, saboda ya damu ko ya ya zai yi fushi da Aji abokatansu ba karya ba ne.

Kimanin shuɗewar sati biyu Sannan ya samu natsuwar kansa. Ranar Asabar da Yamma ya shiga anguwan Arawa saboda maganar da za su yi da Baba, anan ya yi sallar Mangariba da Isha'i tare da su Baba A masallaci. Su Baba Sani har suna tara shi gefe suna mai faɗan zama haka ba amfani ya kamata ya ƙara aure, Baba Sani ya ce akwai yar abokinsa mallam mati in yana so yarinyar uwarta Jajir tunda Bafullatanace, kuma ta dauko kyan uwar ne, Baba Ɗanlami yace gwara dai ya zo ya duba a cikin anguwa in da ake ganin mutumcin ba inda ba'a ganin shi a wata tsiya ba.
Duk bai katse su ba sai da su ka gama koro jawabinsu sannnan ya gyara tsayuwa yana faÉ—in" Na gode Baba da kulawa. Amman ni ban saki matata ba, ta je gida ta huta ne amman za ta dawo soon in sha Allahu."
Yasan harda kuɗi suke bukata a hannun shi haka ya ba su 20k kowanne suka karɓa suna washe baki, duk da yana da abin da ya fi haka amman ba ya sakar musu kuɗi tunda yasan halinsu ba zuwa gidan suke yi su ba ma matansu a ji daɗi ba Sharholiyansu kawai su ke yi acikin gari shi ya sa ko kayan abinci ya gwammace ya ba ma Auwalu ya siya musu ya kai musu.

A kofar gida suka samu keɓewa da Baba Ɗanjuma ya yi masa mganar Walida da Mariya ya ce zaman su ne ya ishe sa ba sun gama karatu ba?
Mansoor ya ce" Eh sun gama matakin sakandiri ba, Ina so su cigaba har matakin jami'a in sha Allahu."
Baba ya yi shuru kafin ya ce"A'a ni na fi son kowacce ta kama É—akin ta kamar sauran Æ´ayana."
Mansoor ya ce"To Baba, sun samu maneman ne?
Baba ÆŠanjuma ya gyara zama kafin ya ce" To ban sani ba, amman abin da ya sa na kira ka kenan, ka kira su dukkansu ka zauna da su ka ji in akwai waÉ—anda ke nenan su, in ka ji akwai sai a bincika in an aminta da nagartansu shikenan."
Mansoor ya yi shuru kafin ya ce"In kuma babu fa? Baba ÆŠanjuma ya ce shikenan sai ka ba su daman fara yin zence har Allah yasa a dace.
Bai yi gaddama ba ya ce zai yi mgana da su in ya shiga cikin gida anan waje ya bar Baban wajen abokinsa Mallam Hashimu ya na ko shiga da Mariya ya fara cin karo tana wankin kayan da za ta saka gobe a dara nan shi bai ma ganeta ba sai da ya ji tana gaishe shi sannan ya tsaya ya na kallonta shi ya daÉ—e ma bai ganta ba.

"Ke ina kike zuwa, ba na ganin ki a cikin gidan nan?
Chapter 20 · 0% Book details