Sashe 34
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
 Duk saboda abib da ya faru ya sa maganar Mimi ta ɗan sarara a ran Aji, amman kuma bai manta da mganar Mariya da ya ce za su yi da Auwalu ba ya same shi sun yi mgana ya ce ya san yaron zai bincika ita kuma Walida aka sama mata wani shagon koyon Computer za ta yi na wata shidda 30k Mu'azzam ya biya kuɗin ya ce tunda yayan na shi ya yi hidima, kuma da yake an san mai shagon ba matsala a anguwan su Yaya Amina ne, za ta rika ziwa monday to friday daga karfe goma zuwa huɗun yamma.
Sai da ya ga ta fara zuwa sannan ya fara Samun natsuwa su Nasir har gidan sun zo gaida Inna shi tare da matarsa Nafisa ya zo Mu'azzam ne ma yake gayamusu Makama ma yazo amman duk ba su samu Ajin ba sai daga baya Inna ke gaya masa zuwan su.
 Sai da kimanin sati biyu ya shuɗe da zuwansa kano sabgogi sun saka bai kara neman wayar Mimi ba itama ba ta neme shi ba, amman dai ya na akan bakan shi na zuwa gidan da aka ba shi auranta.
Sai ya bari ranar lahadi da daddare saboda yadda zai same shi baban nata a gida. Shigar manyan kaya ya yi a ranar kuma ya je aka rage masa gashin kansa sai ya saka hula yana kamshin turare, bai je da mota ba sai mashin yana zuwa megadi ya gane shi, Shi kuma ya tambaye shi Alhaji na nan? Megadi yace ma sa Eh bai daÉ—e da dawowa ba sai ya ce ya shiga ya gaya masa Mansoor ne mijin Mimi.
 Megadi ya tafi da sauri ya isar da saƙo Daddy na tare da matansa a lokacin sai kawai ya yi yar dariya kafin ya ce" Ɗan tselan uwa ashe dai ya san in da zai zo ya samu masalaha,"
Kai tsaye ya ce a shiga ada shi falon baƙi, Mama na zaune ta ga ya tashi ya na saka hula kai tsaye ta ce"Sai ka saurare shi? watan Mimin nawa a gida bai nemeta ba sai yanzu?
Ya na fita daga falon ya ce"In ji wa ya ce bai neme ta ba? Ke dai ba ki san komai ba, bari na je dai."
Anty ce kaÉ—ai ta bi shi da adawo lafiya, Mama kuma haushi ta ji tana ta ya É—an ta kishi yana ta murna kuma murna za ta koma ciki.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3008*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Mansor na tsaye a tsakiyar falon gidan tsohon Sanata Alhaji Hamza sulaiman Dabo. Hannayensa harɗe a kirjinsa, lokaci ɗaya yana nazarin falon, ya taɓa shigowa falon kusan sau biyu wani lokacin a can baya Mimi ta matsa masa ya shiga suka gaisa na farko rashin lafiyan Hajiya na biyu ya manta falilin.
A haka Daddy ya zo ya same shi yana tsaye bai zauna ba, yana ƙarisowa ya miƙa masa hannu suka yi masabaha.
Sannan Daddy ya nuna masa kujera ya ce ya zauna amman sai bai zauna ba sai ya zauna a saman tattausan cafet É—in da ya malale fallon gabaÉ—aya saboda ya tuna wayar su da Mu'azzam yana hanyar tahowa nan ya yi ta hadadda masa ya je neman sulhu ne kuma surukinsa ne ya kamata ya nuna masa girma da daraja.
"Haba ka tashi ka zauna saman kujera mana."
Kan Mansoor na ƙasa ya ce"A aa nan ma ya isa Alhaji."
Sai Daddy bai ja ba kawai sai ya gyara zama suka gaisa yana tambayan shi wajen iyayanshi a sanyaye ya ce Alhamdulillah, shuru na wani lokaci ba daɗewa sai ga Anty ta shigo da farantin ruwa da lemu ta sauke nan saman center table ɗin dake falon, Itama Mansoor ya gaisheta ta amsa cikin sakewa kafin ta ce"Ah yallaɓai ya ka bar surukin namu ya zauna a ƙasa kuma?
Daddy ya yi mirmishi kafin ya ce" Biko ya zo shi ya sa ya ninka biyayyarsa." Tare suka yi dariya shi da Anty sannan ta fice shi ko Mansoor kansa na ƙasa domin sai ya ji Daddy ya yi masa kwarjini ya kuma rasa ta ina zai fara ma mganar, In hr Mimi ta faɗa musu dukkan abin da ya aikata mata ai da Kunya, Shi kuma Daddy nazarinsa yake yi ta gefen ido amman bai nuna ba, wata Jarida ma ya ja anan gefe yana karantawa kamar yadda Daddy ya yi masa kwarjini haka shima Daddy ya ga ƙwarjinin Mansoor ya cika falon gabaɗaya.
"Ka sha ruwan mana."
Daddy ya katse shi lokaci ɗaya yana kallon sa, sai Mansoor ya muskuta ya ɗan mike ya isa ga wajen ruwa ya saka kofi ya tsiyaya Kaɗan ya sha sannan ya ijiye kofin sannan ya koma in da ya tashi ya zauna. Shuru ya sake wanzuwa na wani lokaci kafin Daddy ya sake katse shurun da cewa" Ya wajen aikin na ku? Kwanaki abokanka da ƙaninka suka zo sun ce wasa gare ku masu yawa baka samun lokaci."
Sai ya samu kansa da amsawa da E, shi kuma Daddy sai ya jinjina kai kafin yac e"Good! Allah ya saka albarka," Aji ya amsa da Amin cikin yanayin maganarsa amman muryansa ta yi kasa sosai.
Gani ya yi Daddy ya yi kamar bai san dalilin zuwanshi ba, ya ma cigaba da karatun Jaridarsa lokaci É—aya kuma ya na amsa waya in an kira shi.
Mansoor kuma na duke ya rasa ta in da zai fara dakyar ya iya kundunbalan É—agowa ya na kallon Daddy kafin lokaci É—aya ya fara da faÉ—in.
"Alhaji dama kan mganar Fatima ne.."
Sai ya dakata shi kuma Daddy sai ya kalle shi kafin ya ce"E, ina jin ka, Mimi ba ai ta dawo mana nan cikin kuka, ta ce ka ce ba ka sonta sannan ta ce za ta tafi ka ce is better da ta tafi É—in, ni kuma da na ji haka sai na ce ai ba dole a cikin aure kuma in ka ga alaqa ta fara lalacewa gwara rabuwar shi ya fi alheri."
Mansoor ya yi shuru kafin yac e" Alhaji ni ban ce ta tafin da gaske ba"
"To me ya sa bayan ta taho a daran ko washegari ba ka biyo sahun ta ba, in ba ka nufin ta tafin ba?
Kai tsaye Mansoor ya gyara zama yana faɗin" Ina da dalilina Alhaji, saboda ka san su mata wani lokacin in ransu ya ɓaci gwara ka yi nesa da su su huce, na ga ranta ya ɓaci a lokaci to ba laifi ba ne domin ta dawo gida ta huta amman ba na nufin wai ta tafi saboda ba na sonta, in ba na sonta ai ba zan yarda na aureta ba. Kawai na bata lokaci ne ta huta sannan ta huce daga ɓacin ran da take ciki."
Magana ɗaya bayan Ɗlɗaya haka Manaoor ke fitar da ita, Daddy yana kallonsa amman yana mirmishi kafin ya gyaɗa kai ya ce"Na ji dalilin ka, ta wani fannin kana da ƴar gaskiyar ka ta wani fannin kuma ba ka da shi, amman duk ba wannan ba babban abin shi ne ga rashin ba ka sonta sannan ta ce ka kasa manta abin da ya faru a shekarun baya sai ka riƙa kallonta da abin, ka ga kuwa ai ba kyau irin haka riƙo ba shi da amfani sannan tunda har da bakin ka ka ce ba ka so ai ba wanda zai yi maka dole da sai ka zauna da ita ko ba haka ba?
Kan Mansoor Aji na ƙasa ya ce"E, ta nan kam ina da laifi, amman na gane kuskurena Alhaji a yi hakuri in sha Allahu hakan ba zai kara faruwa ba."
"Maganar rashin son fa? Ba zan ba ka bikon Æ´ata ba sai na ji gaskiyar mgana.*
Ya faɗa ya na ɗan haɗe rai. Sai Mansoor ya sadda kansa ƙasa cikin jin nauyi kafin ya ce"Ita ce ko a da, a yanzun ma ita ce har gobe da jibi ma ita ce, ɓacin rai ne ya sa na yi mata mganganu cikin fushi amman in sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba."