Sashe 80
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Shi kaɗai yake da burin biya ma Inna saudiya ko da Mu'azzam bai taɓa yin zencen da shi ba, Saboda baya son taimakon kowa yanzu dai haihuwan Mimi ne a gabansa sai Jamb ɗin da Walida za ta sake yi, ga bikin Mariya na matsowa duk da shi sai bayan ƙaramar salla gabda nabban sallah sannan za'a yi bikin.
Ya dai fara ba ma Mimi kuɗi ta rike na siyan kayan haihuwa, itama a ɓoye tana siyan ma kanta saboda in megidan ya gani zai yi mata faɗan cewa shi ya gaza ne? Ko ya sakata ne? Shi ya sa ma ta ke ɓoyewa ba ta bari ya gani ba saboda dai a samu zaman lafiya, duk da tana da kuɗi amman bai yarda da ta kashe ma kanta naira biyar ba, sai dai komai take so ta yi masa mgana, in bai da shi a lokacin sai ya ce ta ba shi lokaci, in ya samu sai ya ba ta, ba ya taɓa duba aikinta ko gadon da ta tara shi dai ya sauke nauyin shi, sai kuma yake ganin kamar gazawa ce da ci baya ya zauna mace na masa hidima da kuɗinta amman za ta iya siyan kayan ado domin kanta ko ta yi wani sha'anin a bangarenta ko kyauta ga wanda ta ga dama ba zai hanata ba.
Ya sake biya ma Walida Jamb bayan ya gama ja mata kunnen saura ta je ta faɗi, sannan ya saka ta jamb class, sai faɗa yake yi in aure take so ta yi mgana kada ta saka shi kashe kudi, Mimi ke tausan shi da cewa Jamb fa sa'a ne da rabo shi kuma ya ce har dakewa kuma da gaskiyansa duk abin da aka yi ma dakiya za ka iya cin ma nasara, itama Walidan ai ta sani dole ta dake da ƙoƙari. Sannan BUK ya cike mata saboda Mu'azzam ya ce za ta zauna a gidansa ta yi karatun ta, bai yi mata katsalanta kan ra'ayinta ba ya ce ta zaɓi Course ɗin da take so sai ta saka Microbiology.
 Rayuwar dai haka ta cigaba tafiya a kwana a tashi ba wuya ga cikin Mimi na wattani takwas, Mommy ta yi mganar za ta koma gaban Hajiya ta haihu, Mimi na gaya ma Aji yace bai amince ba a tsarin shi ba tsarin matarsa ta je gida wanka a nan gidan za ta zauna ta yi wankanta da jegonta. Tunda kuma ya ce haka ta san yana kan matsayarsa sai ba ta matsa ba, ta ce ma Mommy za ta yi jegonta a gidanta ai suna kusa ba matsala, A watan ta je kaduna Khadi ce ta samu ɓari ta yi ta zubar da jini kamar ba za ta rayu ba.
 Ba tafiyar mota suka yi ba Jirgi ne ita da Hajiya da Mama suka kwana biyu suka dawo. Amman ta je gidan Ahmad sun gaisa da Matarsa ta na kuma dawowa Rukayya ta taso ta gaba kan shiryen shiryen biki tunda saura wata ɗaya da an yi ma sai dai an ƙara ma wata ɗaya ne a sama.
Ga cikinta ya tsufa ba ta iya wannan zaryan Aji ma ya ce Rukayya ta É—aga mata kafa, ita kuma ta ce sai sun rama ma kura aniyarta itama haka ta wahala da na su bikin Aji ya ce dama ba don Allah ta yi ba kenan? Rukky ta na dariya tace eh sai an rama biki ba.
 Karamchi Tibi ta yi rashin ma'aikaciya Irin Rukayya domin tun saura wata ɗaya da wani ta ijye aiki, duka ma'aikatan sun yi kewarta musamman ma Na Misau,itama Mimin ta na so ta ɗauki hutu amman sai ta haihu saboda ta samu ishashen ookaci a gida tana kula kanta da abin da ta haifa tare da mijinta.Saboda shi ya na son kulawa ba zai mata uzirin domin ta haihu ta yi masa banza ba, nauyi ne zai haɗu mata dole sai ta samu lokaci da hutu.
Zuwa Lokacin sun gama siyan kayan haihuwa har na fitar suna, Itama ta ƙara ta siya ma kanta abin da take so da kuɗin ta.
Zirga zirgan bikin Rukayya ma ya sa ta sassaɓe. Ga shi biki gida biyu ga gidan su Rukayya ga gidan Daddy ana saura sati biyu biki a kai kai lefe akwati takwas kuma kaya sai wanda ya gani. Nan gidan za'a kawota ta yi sati ɗaya sannan mijinta ya ɗauketa zuwa lagos gidan da Jaheed ya siya fili ya na ginawa ba'a gama ba, sai an gama za'a yi ma amarya jere anan Gombe.
 An shiga satin biki zirga zirga da hidima ya ƙaru, Mimi da katon ciki a gaba ta ce ma ita ba wani kyau za ta yi ba tunda duk hallita ya sauya, sannan Gogan bai hana ta amman duk dare zai je ya ɗauko ta ta kwana a gida da safe ya maida ta, ba ta zama a gida ga zuwa aiki ga hidiman biki, shi yavsa ba ta san Mu'azzam da yayan na shi sun samu matsala har sai Baba ya yi musu sulhu ba, kan mganar biyama Inna aikin hajji ne, an ta biya sannan ga Walida ta samu Jamb har Buk sun ba ta admmission shi ne ya kira Mu'azzam kam hidimar makarantar anan ne ma ya ke faɗa masa kuɗinsa kaf zai haɗa ya biya ma Inna saudiya, shi kuma Mu'azzam ya na jin haka sai ya ji haushi ya ce ai tare suka ce za su haɗa kudi su kai Inna Saudiya me yavsa ya zare shi a ciki? wato ya nuna masa shi Inna ba ta haife shi ba kenan?, shi ta haifa Mansoor ya so ya fahimtar da Mu'azzam cewa ba haka ba ne. Amman ya yi fushi Ya riƙa kiran shi a waya bai ɗauka ba sai da Mansoor ya je ya gayama Baba shi ya kira Mu'azzam ya yi musu sulhu, amman sai dai a ka yi yarjejeniyar Mansoor zai biya miliyan shida shi Mu'azzam ya cika sauran, dole a ka tsaya a haka sai dai Inna ta ji kawai ƴayanta za su biya mata ta je ta sauke farali ai sai ta saka kuka ta yi sujudaan godiya ga Allah ta na kuka ta na yi musu addu'an Allah yasa su gama da duniya lafiya.
 Ko kafin a gama bokin Rukayya har an kai Inna an mata pasport, an biya mata hajji ƙarkashin jihar Gombe.Kowa na ta zuwan ma inna murna baki ya ki rufuwa, ita kuma Walida sai bayan salla za ta wuce kano makaranta tunda azumi ya kusa. Gefe ɗaya kuma su Inna sun fara zuwa bita. Rukayya Amarya suna gama satin su suka yi sallama da ƴan'uwa suka ɗaga sai garin Ikko Mimi ta ba ta lambar Madiha tacce ga Yaya nan ta yi mata ba za ta yi kaɗaici ba.
 Bikin Mariya zai kama gabda babban sallah ne, Magajiya ta ce a ɗaga shi sai bayan babbar sallah Uwar amarya ba ta nan lokacin ta dawo Inna kenan, tunda yanzu Magajiya ta saduda ta nemi gafaran Inna suna zaune lafiya sannan ƴa'yan gabaɗaya sun haɗe kansu, Maeesha da Mimi ma sun haɗe kansu waje ɗaya kamar wani abu bai faru ba Saddiqun ma harkan gini Auwali ya saka shi tunda shi yanzu sai godiyar Allah ya samu ɗaukaka.
 Ana azumi saura sati ɗaya Mimi ta sauka, cikin dare gab da asuba Naguda ya kamata Aji ya ɗauke ta zuwa asibiti daman tuni ta shirya akwatin kayan hqihiwanta cikin ikon Allah ko awa ba ta kai tana nqguda ba, ta haifi ƴarta mace jajir da ita idanuwan da bakin da hancin na Aji ne fatar da suman kan kuma duk na Mimi ne. Turbarakallah mssha Allah sanda ta haihu Inna na asibitin da Yaya Amina sai Baaba Uwani da Mama tunda ya kira su a waya ya sanar da su.
Kafin gari ya waye labarin haihuwan Mimi ya karaÉ—e Gombe da kewayenta.
Kuma kai tsaye uban ƙarnin ke fadin an samu wata MARYAMA ta biyu.
*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3019*
*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
Mimi ba ta kwana a asibiti ba, ta dai yini zuwa dare bayan an tabbatar da lafiyanta da na abin da ta haifa a ka rubuta musu takardan sallama amman fa asibitin nan ta ga gayya kashi kashi kama daga Æ´an'uwanta zuwa Æ´an'uwan Abu Maryam É—in. Gidanta a ka maidata, saboda daman Aji ya ce ba ya son wankan gida matarsa a gidanta za ta zauna ta yi jegonta sai dai a samu mai zama da ita, Mommy tuni daman ta yi ma Inna Zainaba mgana ta na jin an haihu a ranar ta iso, amman a gida ta same su tunda ba ta taso a kan lokaci ba.