← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 93

Sashe 60

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai ko dai Walida ta sha gwangwanja a lokaci ɗaya sai ga waya da sabuwar laptop, Shi ya siya waya Mimi ta siya mata laptop tunda ta kusa gama ma koyon computer, an kusa yaye su daman wattani shida ne Walida kamar ta suma saboda daɗi Inna na yi mata dariya. Haka ta riƙa kiran yan'uwanta ta na gaya musu abun arzikin da ya sa me ta, Hajiya kuma har gida ta zo ta ga gida ta yi ma Inna Meri murna sannan itama Innan ta na zuwa duba Hajiyan lokaci bayan lokaci.
Gidajen yan'uwansa ko Mimi ta leka sau daya, gwara ma gidan Bintu da mijinta ya siya mota sun je Allah ya sanya alheri ta bi Walida sun tafi tare, gidan Yaya Amina sau É—aya taje haka ma gidan Yaya Halim gwara ma can gidansu Hibba in aka yi wani abu Inna ta gaya masa sai ya ce ta shirya ta bi su, ita dai daga gidan Hajiya sai gidan Daddy shima tare su kan je sai gidan Rukky da yanzu ya ke barinta zuwa amman Rukkyn ma ta fita zuwa wajenta lokaci bayan lokaci.

Sannan Meesaha ma ta zo wajenta ya fi sau biyar, ita dai ba ta sakar mata ta yi ta kawo mata mganganu Saddiqu yanzu babu komai ya daina zuwa Lagos ɗin sai zaman banza a gari, ita kuma Mimi sai ta ba ta shawaran tunda ta yi karatu ta nemi aiki domin ta taimaki mijinta. Mansoor bai hanata mu'amala da kowa ba domin ya ce ita ba yarinya bace ta san yadda za ta tafiyar da komai, ba ruwan shi da yana da matsala da wani shi dai matarsa kawai ya sani ita yafi kiyyewa fiye da kowa, in ta zo in ta na da abu za ta ɗauka cikin mallakinta ta yi mata taimako ba ta tasallake iyakarta, Tasan wanda take aure shi ya sa ba ta karambanin taɓa abin da yake na shi ne sai da izinin shi.

Ya sanar da ita ya na so ya samu lokaci su je can kwami ta ga tushensa da ganan su shiga Bauchi in sun dawo kuma ya ba ta izinin za ta je Abuja ta ga Mommy ko na kwana biyu ne Mimi na ta murna, shi kuma ya yi mata kara ne ganin ba ta taɓa nuna masa ƙosawar ta ba, shi kuma farincikinta yake so, adalci ya ke son yi mata kamar yadda ta yi masa, kuma ba ya son yau ace Mimi ta ji ta na son wani a bu ya kasa yi mata shiyasa kafim ma ta tambaya yake kokarin yi mata shi, Har cewa ta yi ya kamata su je kano ya ce ita da kano sai Hibba ta haihu, ai ta je kafin tareewarsu ba ta gaji da zuwa ba. Dole ta kama bakinta, iya ma Abujan ta gode ma Allah da ya barta shima baya nan lokacin za su je kaduna.

In ya na gida tana girki ya kan taya ta da niko wannan É—auke wannan, baya takura kansa abin da zai iya shi yake yi, ya ce girki na mata ne amman ba shi zai hana ya É—an taimake ta da abin da ba'a rasa ba. Rayuwa dai suke yi dai dai rayuwar mallam bahaushe.

*Janafty*
[9/8, 19:53] Auntyna: *INZB3014*

*INZ IS A PAID BOOK PAY N500 FOR REGULAR OR 1K FOR VIP SECTION. VIA 0007468217 ZAINAB INUWA TAJ BANK,*
*09069067488*

https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC

No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.

_28TH. MAY 2023_
*SUNDAY, 12:00PM*

Tunda yau lahadi ana cikin hutun ƙarshen mako, da ga shi har ita suna gida ba su fita ba gwara shi caach ya kira shi da safe ya fita zuwa camp sun yi mgana a kan wani gagarumin taron da babban kungiyar ƙwallon Kafa ta ƙasa baki ɗaya za ta shirya a garin Abuja wato Super Eagles shi Aji baya son zuwa taron Caach ɗin su kuma ya matsa masa ya na so ya wakilci jaharsu tunda shi ne Captain tunda abin kamar dukk an gayyaci manya manya kungiyoyon ƙwallon kafa na Nageria ne gabaɗaya.

  Shi kuma Aji ya ce Coach ya fi shi matsayi shi ya kamata yaje, shi kuma ya na nuna masa shi dai ɗin ya kamata ya je haka suka rabu ba su samu matsaya ba. Tunda Aji ya kafe har da cewa tafiya za su yi zuwa garin su shida Mimi amman Coach ya ce ya ma fara shirin tafiya Abuja ba fashi, da wannan haushin ya dawo gida Mimi na barci ba ta tashi ba daman sanda ma ya fitan ba ta sani suna kwance ne suna barci ya zare jikinsa ya fita, sanda kuma ya dawo sai ya yi zamansa a falo kawai yana wani lissafin.
Shi fa ko da yake sanannen ɗan ƙwallo a jiharsa shi mutum ne mara son shigewa mutane kada ma ace yana neman wani abu ko kuma neman fada da wajen zama. Shi ya sa rayuwarsa yake yi kai tsaye baya neman kowa sai wanda ya neme shi Coach ɗin su ma ya yi ta son haɗa shi da sanannu manya a ƙwallon kafa na ƙasa gabaɗaya amman Aji sai ya riƙa noƙewa.

  Gajiya ya yi da zama a falo yana ta saƙe sake bai isa ya gujema wannan tafiyar ba Coach kamar uba yake gare sa. Da dai ace sanda ya yi turjiyan ne ya amince shikenan amma  yanzu tsarinsa ya rushe, zuwan shi kwami da Bauchi ba zai samu ba sannan Mimi ma ba zai hana ta tafiya Abuja tunda ya riga ya yi mata alƙwari kuma ya san ta sanar da Mommy, sai dai yanzu su tafi tare shi ya je ya yi abin da ya kaisa ita kuma ta je gidansu ta zauna in ya gama abib da ya kai sa sai su dawo tare, ga kuma babbar salla ta ƙarato sai dai su ɗaga tafiyarsu Kwami zuwa bayan sallah. Gajiya ya yi da zama ya tashi ya kunna talabijin a tashar kwallon ƙafa daman su yake kallo ko tasoshin wa'azi Mimi kuma daman kallo bai dame ta ba barta da barci sai kuma waya,wayar ma ba sosai ta dame ta ba.

  Bai san fitowarta ba sai ji kawai ya yi ta saƙalo hannayenta daga bayansa zuwa wuyansa lokaci ɗaya tana ɗora kanta a saman kansa cikin yar shagwaɓa ta ce"Shi ne ka tashi ni ba ka tashe ni ba ko?
Ta faɗa ta na sosa kirjinsa da ɗayan hannunta ɗayan hannun nata kuma ta fara sosa masa kunninsa guda ɗaya, juyowa ya yi bayan ya riƙe mata duka hannayenta sannan ya zagayo da ita har gabansa ya zaunar da ita kan cinyarsa suna masu kallon juna ya ce"Kina ta sharan barci duk kin bugemin jiki, kina ta munshari, ga shi kin saki baki galala da miyan barci."
Ya faÉ—a lokaci É—aya har ya na kauda kansa yana Æ´ar dariya. Rufe baki ta yi tana kallonshi cikin mamaki kafin ta ce"Ni ne ke minshari da miyan barci?
Ta faÉ—a har ta na zaro ido cikin tsoro domin har ga Allah ta É—auka da gaske ne.

  Rumgumeta ya yi yana faɗin" E, mana, ban taɓa faɗa miki ba ne, amman kada ki damu ke na ke so ba zan damu da minsharinki da miyan barcin ki ba" Yadda ya ƙarishe maganar da dariya ne ya sa ta gane abin da ya ke nufi, da sauri ta saka hannu ta mintsine shi a cikinsa har sau biyu kuma mintsinin da zafi da ya sa dole ya saketa ya yi gefe yana raɗin"Mimi ba na son mugunta fa daga faɗin gaskiya?
Mikewa ta yi daga kan cinyarsa ta riƙe kugu daga ita sai rgar barci fara mai shara shara iyakarta gwiwamta sannan surar jikinta duka yana buɗe ne gashin kanta ma yana ɗaure ne kanta ba hula ba ɗankwali.

"Waye mai miyan barci da minshari?

  Haka ta faɗa ta na zare masa ido har da ɗaga hannu kamar za ta kai masa duka ya saka hqnnuwansa ya kare kansa yana faɗin" Allah ya baki hakuri Inna Fatima."
Ya faɗa yana yar dariya sai kawai ta ja cution ɗin kujera ta mara dukanshi da shi ya na karewa da hannunshi yana dariya bai hana ta ba sai da ta gaji ta bari shi kuma daga kwancen ya saka hqnnu ya jawo ta ta faɗo jikinsa ya rumgumeta ita kuma tana neman ƙwace kanta lokaci ɗaya tana faɗin" Ina miyan barci ko?
Ya na yar dariya ya ce"Na tuba na janye mganata ina ga ni ne me miyan barcin da minshari ban sani ba"
Hararansa ta yi kafin ta ce"Za ka ma sani ne." Ta faɗa ta na kokarin tashi ya sake riƙeta ya nannaɗeta a cikin jikimsa yana mata raɗa a kunne ba ta san lokacin da ta yi dariya ba. Bai bari ba sai ya fara yi mata cakulkuli ta fara dariya kamar za ta shiɗe tana faɗin" Cikina na ciwo don Allah ka bari."
Sai da ya ga tana hawaye sannan ya kyaleta ya koma ya na sumbatan bakinta.
Daga nan suka rike kan juna suna sumbatar bakin juna cikin shauƙi da soyayya.

  Sun ɗauki lokaci suna farantama juna rai sannan suka saki juna suka koma su ka sake rumgume juna suna maida numfashi, kan Mimi na saman kirjin Aji shi kuma ya saka hannunahi ya na shafa gashin kanta,  Idanuwanta a lumshe tana jin wani irin farinciki na ratsa ta a nan duniya gani take yi kamar tafi kowa dacen samun abokin rayuwa nagari, shi ma a bangarensa addu'a yake yi Allah kada ya bashi ikon kuntata ma Mimi, Allah ya zaunar da su lafiya ya kaɗe fitina.

"Me za mu yi breakfast da shi yau Aji?
Chapter 60 · 0% Book details