← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 93

Sashe 5

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Ya faɗa ya na huro iskar bakin shi, Nasir ya yi kasaƙe kawai yana kallon Aji har sai da yaji shuru shima ya Juya ya na kallonsa kafin ya haɗe rai yana faɗin" Ba kallo na na ce ka yi ba  amsa za ka bani."
Nasir ya sauke numfashi kafin ya gyara zama yana faÉ—in" Na É—auka duk waÉ—anan tambayoyin naka za ka fini sanin amsar su."
"Inda na sani zan zo har nan in tambaye
ka? Aji ya faÉ—a cikin jin haushi.
Nasir na danne dariyan shi ya ɗaga hannu yana faɗin" Shike nan mai da euƙar  kai ka girma ammman ba ka daina gitina ba."

"Da gaske kenan ni fitinanne?

  Ya faɗa ya na kallon Nasir wanda ya yi jim kafin ya ce" E,wannan ai jalittarka ce tun a baya, ka manta in dai mu ka zauna waje ɗaya kafin mu rabu sai mun yi faɗa kamar Sau uku ko sau huɗu, Ko da yaushe Makama da Ahmad na cikin raba tsakanin mu, kai fitina ni kuma rashin jaƙuri."
Ya karishe faÉ—a yana yar dariya Aji kuma kansa ya kauda bai ce komai ba sai Nasir ya Cigaba da faÉ—in.

  "Mansoor mutum ne mai kirki da sanin ya kamata, sannan kana da kyakyawan mu'amala da mutane a baya. Sai dai tun bayan abin da ya fru tsakanin ka da mahaifin Mimi ka sauya Aji. Rayuwarka ta yi Juyin waina daga sama zuwa ƙasa."

  Aji ya juyo ya na kallonsa kafin ya ce" Daga sama zuwa ƙasa? Kamar ya? Ban gane ba."
Ya faɗa cikim sigar tambaya sai kawai Nasir ya dafa kafaɗansa lokaci ɗaya yana faɗin" Yes ka sauya tun faruwar abin da ya faru a Lokacin, ka guji kowa naka ciki har da mu, ka yanke alaqa da kowa ka koma kana wata irin rayuwar kaɗaici wanda ya ba ma sheɗan Ddman kara hura wutar gushi da zafn zuciya a cikin ranka. Ka koma mai wata irin zuciya mara yafiya da afuwa,  ka koma abu kaɗan in aka yi maka sai ranka ya ɓaci, Sannan sai ka riƙa gayyato mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ka riƙa saka su cikin Fushin ka, mu ina Laifin mu a cikin abin da ya faru? Ko laifin waɗanda ka haɗa kana Jin haushi? Ita kanta Mimi ba ta da laifi har ga Allah Mahaifinta ne kuma ya rasu  Aji me ya sa ba za ka bar zuciyarka ta huta ba? Sai ka riƙa fushi da wanda ta shi rayuwar ma ta ƙare tuntuni, Allah ma fa muna yi masa Laifi ya yafe mana duk girmansa. To kai me ya sa ba za ka kasance mai afuwa da yafiya ba? Duk abubuwan nan da suka faru rashin Afuwarka ne da maida komai ba komai ba ne da a ce ka kasance mai barin abin da ya faru a matsayin kaddara da ka kasance mai sanyin zuciya da kyakyawan daɓia a cikin mu."

  Ya karishe faɗa yana mai kallon Aji ido a cikin Ido kuma ya ga maganganunsa sun shige sa sosai, domin shuru ya yi na wani lokaci kafin ya fesar da numfashi ya ce" Yanzu kana ganin ni da a ka saɓawa in na nuna an ɓatamin sai ya zama Laifi?
Nasir ya girgiza kai kafin ya ce"In ka nuna an yi maka ba dai dai ba, ba ka yi laifi ba amman riƙon nan ba shi da wani amfani Aji, mutumin nan daga baya ya yi nadama ya aiko har gida a ka zo a ka baka hakuri Saboda su wanke laifin su, suka ɗauki Mimi suka aura ma a bisa tsarin ka shin ko zaman da yarinyar ta yi da kai duk da ka yake mata wasu haƙoƙinta ba ta chanchanci saboda ita ka manta abin da ya faru ka Fuskanci gaba ba?
Aji ya yi shuru domin ya san gaskiya Nasir yake faɗa masa sai ya kasa mgana domin nadaman abin da ya aikane ya zo ya ƙara lulluɓe sa.

  Nasir na ganin haka ya cigaba da faɗin" Don Allah ka manta baya mansoor ka bar zuciyarka ta samu salama, ka ɗauka a ranka da duk abin da ya faru Ubangiji ne ya shirya sannan ka rika tuna lokaci, a can baya Allah ya rubuta a wancan lokaci ba za ka auri Mimi ba shi ya sa abin da ya faru ya faru a baya, sannan a lokacin da ka aureta a lokacin ne Ubangiji ya ce Kum fa yakun Mansoor shi ya sa kagl ga alokacin ka aureta, abin da kake nunawa dai dai yake da ka na ja da ƙaddaran Ubangiji akan rayuwarka Mansoor."

  Kansa ya jinjina kafin ya ce" Haka ma Mimi ta ce min jiya, wai ina ja da kaddaran Allah a kan rayuwata."
Nasir yace"Yes! Is Truth, duk abin da ta faÉ—a maka gaskiya ne, gwara ka buÉ—e zuciyarka."
Aji ya yi shuru kafin ya sauke numfaahi lokaci É—aya yana faÉ—in" Na ji, to yanzu in ina so na manta abin da ya faru ya zan yi? Ko ina so na manta sai na kasa saboda zuciyata ce ta kasa manta abin da ya faru a baya."
"Sheɗan ne ke rinjayar ka, amman ka fara Koyon yaƙi da abin da ke cikin zuciyarka ka yi yakinin cewa na yafe ma duk wanda ya taɓa cutata, sannan sai ka fara kokarin manta baya ko da zuciyar taka tana dawo da kai acan baya sai ka yi saurin neman tsarin Ubangiji ina mai tabbatar maka cikin lokaci za ka manta komai sannan zuciyarka za ta samu salama da amincin da ta jima ba ta samu ba."
Nasir ya gama faÉ—a hannunsa saman KafaÉ—an Aji, wanda ya runtse ido lokaci É—aya sannan ya buÉ—e yana faÉ—in" Shike nan zan yi kokarin na gwada haka."
Nasir ya gyaɗa kai kafin ya ce"Allah ya sa, sannan don Allah ka rage kafiya da zafin zuciya, kuma ka daina jin cewa a cikin ranka sai abin da ka ga dama za ka yi, ka yi tunani da kanka ka gani ka girma yanzu  kana bukatar natauwa waje ɗaya da kyakyawan zamantakewa a wajen matarka."
Kansa na ƙasa ya fitar da Iska ta bakinshi kafin ya ce" Na ɓata komai Nasir, jiya nan na gaggaya Mimi mganganu ni har Babanta ina ji na kira da azzalumi."

  Nasir ya zaro ido lokaci ɗaya yana faɗin" Innalillahi, Aji garin ya ya ka yi wannan ɗanyen aikin?.
Mansoor ya saka hannu ya shafo kansa sannan ya fara faɗa ma Nasir abin da ya Ffru tun na kan tafiyarta Abuja zuwa jiya daga karshe yac e" Inna ma ta ji komai Nasir kuma kasan halinta, Ni banjin Mimi saboda nasan ta na sona za ta gama fushinta ta hakura, kuma ni tun jiya na yi nadaman maganganun da na faɗamata,  Inna nake ji za ta ɗauki fushi da ni, ka gani ma Mu'azzam na ta kirana shi da Baba kuma nasan kan mganar ne."
Nasir ya kalli Aji cikin matsanancin takaici kafin yac e" To da gaske ashe baka son Mimi? Ka daina sonta ne daga baya ko daman can tun farko ba  son ta kake yi ba?
Wani sakaran kallo Aji ya yi masa kafin ya ce" Wannan wani irin tambaya ne Nasir? Kasam Mimi ita ce rayuwata."

  "Ba ita ba ce rayuwarka, domin da ita ce rayuwarka da ba ka ci zarafinta tare da na iyayenta ba sannan da ba ka baro ta tana kuka ka yi tafiyarka ko a jikin ka ba Aji."

  Nasir ya faɗa cikin ɓacin rai, Aji ya dafe kansa kafin ya ce"Oh! Na ce maka na yi nadama, kuma kar ka damu da ita tana sona ba za ta iya dogon Fushi da ni ba?
"Haka kake gani ko?  yanzu kana da tabbacin ba ta tafin kamar yadda ta bukata ka amsa mata ba?
Cikin ƙwarin gwiwa ya ce"Yes! Ina za ta je? Na faɗa maka ba za ta iya tafiya ba, ni ne rayuwarta kamar yadda nima take matsayin rayuwata" Sai da Nasir ya yi yar dariya a cikin ransa ya na fatan Mimi ta yi tafiyar ta domin har yanzu Aji bai yi laushi ba akwai jin kai a tare da shi.

  Aji roƙansa ya yi akan ya zo ya raka shi gida ya t ba ma Inna hakuri, karo na farko da Mansoor yake jin tsoron haɗuwa da Inna, Sai Nasir ya ce bari ya shiga ya yi wanka wani harara Aji ya sakar masa kafin ya ce"Dilla mallam mu tafi, nima ai ba wanka na tsaya na yi ba."
Nasir yace"Shike nan ba zan shiga na sallami Iyalai na ba?
Kafin Nasir ya rufe baki sai gani ya yi kawai Aji ya ja mota sun bar ƙofar gidan sai Nasir kawai ya saki baki yana kallonsa shi kuma sai kawai ya ɗauke kansa har ya na wani ɗaga wuya lokaci ɗaya da tattare naman goshin sa.

  Lokacin da suka isa gidan a kofar gida su ka haɗu da Baba Sani da Baba Ɗanlami suna ta kuskus sun haɗa kai, suna ganin Mansoor jikinsu na rawa suka tare shi,Irin gaisuwarshi ya yi musu, Nasir ne ya yi musu irin gaisuwar da suke so. Yana ƙokarin ya wuce cikin gidan amman Baba Sani ya tare shi da faɗin" A she kuma abin da ya faru kenan, To Allah ya kyauta na gaba kune yaran zamani in an gaya muku gaskiya sai kuka ga kamar ana muku bakin ciki ne, yanzu ina amfanin abin da ya faru?
Baba Ɗanlami ya karɓe da faɗin" Ba amfani fa, shi ya sa a kace kowa ya tsaya matsayinsa, ina kai ina auran ƴar masu kuɗi? Da cikin yaranmu ka nema ai da ba'a ji kan ku ba, ina riba ace aure ko shekara bai yi ba ya ƙare, abun dai ba daɗi."
Mansoor ya yi kasaƙe kawai yana kallonsu Nasir ma su yake kallo sannan ya koma ya na kallon Aji cikin mamaki.
Domin shima yana so ya fahinmci mganarsu ne.

  "Na ce ba, saki nawa ne ka yi mata? In ba uku ba ne sai a shiga a gyara lamarin saboda ko bakomai mu cece darajan wannan gidan kar a fara kirga ma ƴaƴan mu auri saki."
Chapter 5 · 0% Book details