← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 93

Sashe 32

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Take faɗa tana wani hura hanci, Mansoor ya yi niyar zagayeta su wuce ne amman Inna ta hana ta kalli Magajiya na wani lokaci kafin ta yi mirmishi ta ce" Kin ce wai dangin ubansa me suka yi masa ko? Ai ko sun yi masa komai tunda dai tun zuwan Baban Inna gidan nan abin naira biyar baki taɓa taimakon shi da shi ba kin ga baki da ikon faɗi wata mgana ba. Sannan na daɗe ina hakurin duk irin cin kashin da kike yi min a cikin gidan ki yi ta aibatana ɗana kina kiran shi da Agola Allah Sarki da ace Ibrahim ya yi tswon rai Magajiya na rantse ga Allah kila har ki koma ga Ubangiji ba za ki  haɗu da ni ba. Ba zan zo aure a wannan gidan har na zo da Baban Inna ba mutuwa ce ta yi ma shigar sauri ita ce ta maida shi mara uba amman ba Agolan da kake tunani ba, ni  ce nan na matsa sai na taho da shi saboda ba na son ya yi nesa dani amman ke kam shaida ce ba domin dangin Babansa sun gaza da ga riƙon sa ba. Na zauna da kowa bisa amana a wannan gidan ban taɓa tunanin cutar da kowa ba, ban sani ba ko tun zamana na taɓa yi miki wani abu na ɓacin rai da ya sa kika tsane ni. To yau ta kare ki yi hakuri ki yafe min Magajiya, Allah ya baki hakuri in dai laifina auran Mallam da kuma riƙon Yayan da ya bani to duk kiyi hakuri rayuwar nan duka duka nawa take? Wata rana ba ni ko ba ki a duniya nan? Ko kuma ba Mallam ko mu rasa wasu daga cikin yaran mu duka sanin gaibu sai Allah ki yafe min Allah ya kaddara saduwa."

  Inna Meri ta gama faɗa tana mai fashewa da kuka sai jikin Magajiya ya yi sanyi duka masifanta ta kasa magana, Inna Meri na kuka ta kalli su Gaje tana faɗin" Saboda zama da rayuwa in na taɓa saɓa muku ku yafe min, ni dai wlh ban taɓa rike kowa a cikin ku ba na yafe muku duniya da lahira, Sani da Ɗanlami ku ma ku yafe min ƙila zama na tare da ku na yi muku wani abu ni dai ba ku min komai ba wlh, ina rokon ku da yafe min saboda rayuwa."
Tana magana tana kuka  Gaje da Harira jikinsu duk a sanyaye su ka ce wlh ba ta yi musu komai ba ita ce ma suka yi ma laifi ta yafe musu ta ce bakomai su baba Sani sun kasa mgana Ɗanlami ne ya ce su kam ba ta yi musu komai ba.
Magajiya na ji da gani Mansoor na rike da inna Meri su k fice daga gidan su Gaje suka raka su har da Baba Danjuma aka bar mata gidan gabaɗaya amman kuma ta kasa farinciki Har Auwalu da shi a masu rakiya,  tuni makota sun fara taruwa,  su Gaje ke faɗin Inna Meri ne za ta bar gidan sai ga shi an fara cika wajen tuni Dije matan Mallam Hashimu ta garzayo, ta lna kuka tana faɗin Ina Inna za ta tafi ta barta Inna ta ce ba inda za ta je, amman ta san duk in da Baban Imna zai kaita in da za ta samu natsuwa ne amman ba auranta ba ne ya mutu gidan ne kawai ta fahimci alheri ne ta bar shi.

  Shi amfanin zama da mutane lafiya yana da kyau haka makota ke ta sharan hawayen barin Inna anguwar nan saboda kyawawan hallayanta wasu har suna faɗin ita ce Alherin gidan wanzamai wasu kuma su ka ce tunda Innar Mu'azzam ta bar gidan nan Sun daina shiga gidan daman saboda ita ce mace mai kirki da karamci mai zumunci duk abin da ya faru in dai ta ji sai ta je abun kaico kaico da abun Allah ya sanya alheri ga hannun kyauta ga son mutane da mutumci hatta da su Gaje sun koka wlh, Baba Danjuma duk jikinsa ya yi sanyi amman shima gwara haka ita kuma Magajiya ga ta ga gidan sai ta zauna.

  A gaban mota Inna ta zauna su Walida har da Mariya da tana kuka ta ce za ta bi su ta ga in da za su koma suka shiga baya, Sai Baba Danjuma ya ja mansoor gefe yana tambayan shi in da zai kai Inna?. Kai tsaye ya ce" Gidana za ta koma Baba."  Cikin mamaki ya ce"Gidan ka? To kai fa?
Mirmishi ya yi kafin ya ce" Kada ka damu Baba, zan iya siyan wani gidan ko na gina wani, Allah ya rubuta daman gidan zai zama na Inna nw wata rana.".
Sai kawai Baba ya dafa kanshi yana ta saka masa albarka. Makota kuma ma su jajen tafiyar Inna ta ce duk su yi hakuri in har ta ga in da suka koma za ta sa Bintu ta zo ta gaya musu sai su zo su ga in da take amman zumunci ba zai yanke ba.
Haka aka yi dafifi wajen motar Mansoor suna  ɗagama  makota hannu suma suna ɗaga musu, hatta su Baba Sani sun kasa motsi kamarin ya girgiza su, Magajiya na cikin gida ta kasa fitowa domin ta rasa me ke mata daɗi, Zuwaira na fadin daman ya san yana da in da za kai uwar tasa ya barta anan ta ce ma magajiya ai gida ya zama naki yanzu, Saddiqu kuma sai kumfar bakin sai ya ɗauko ma Mansoor yan daba sun yi masa dukan tsiya yake yi   Matarsa kuwa ta ja jikinta ɗaki ba ma wanda ya ƙara ganinta tuni aka manta da dukan ciki ballantana maganar zuwa asibiti.

  Magajiya ɗaki ta shige, tana zaune Zuwaira da Saddiqu suna mganganu amman ba ta sauraransu ita kaɗai ta san hqlin da Zuciyarta ta ke ciki. Kamar ta ɗora hannu ta rusa ihu. Ga shi dai Meri ta bar mata gidan amman ta kasa farinciki sannan ji irin yadda Mutane suka taru suna kukan tafiyarta wai har da su Gaje, sannan ita me ya sa ta kasa farinciki? Ina za ta koma? Ko dai gidan shi zai kaita? Ta na hasaso wanman katon gidan domin lokacin da aka gama ginin Danjuma ya matsa sai da su ka je gidan suka saka albarka, in dai Meri ta koma wannan gidan ai ta ci gaba ita kuma ta bar ta a gidan gado? Kamar ta saka kuka haka take ji Kallon Zuwaira ta yi Idanuwanta sun kala sun jajir kafin ta ce"ina Mariya?
Saddiqu ya ce"Kila ma ta bisu, tunda daman ba ta da kishi, duk irin su Auwalu ne." Sai Magajiya  ta yi  tagumi domin ta rasa kuma wani nazari za ta yi. Ga shi dai gida ya zama sai ita kaɗai amman kuma ba ta jin farinciki saboda tunanin in da Meri za ta koma ya fi in da ta ke sau ɗari da saba'in keman ita ta ci gaba ita kuma ta na nan a waje ɗaya.
Duk mganganun da su Zuwaira ke yi ko É—aya ba ta ji ba, ta yi nisa cikin tunanin makomar rayuwarta a wannan gidan ga shi dai burinta ya cika gida ya zama nata amman kuma a kasan ranta ta kasa farinciki.

*****

Bangaren su Inna Meri kuwa daga nan ƙofar gidan Wanzamai sai gidan Mansoor, dake anguwan Tunfere, Ya nan a yadda yake kamar sabo tunda ba zama aka yi a gidan ba shi ne kuma regular ne wata rana ma ya na cinye satin shi a Camp.
Bintu ya ba ma Key din gidan ta buÉ—e shi kuma ya riko Inna Meri har tsakiyar falon gidan da ba komai sai katon tibi da cafet, Inma sai kallon gidan take yi, Bintu da Walida kamar za su suma saboda daÉ—i.
Gidan akwai kura saboda ba mutane a ciki amman komai sabo ne. Sannan gidan 4Bedroom ne, Sai daga waje haraban parking in da mashin ɗinsa take sai ɗakin megadi da wani ɗaki daga waje sai Fulaowin da ya shuka suka ƙarama gidan kyau a ciki akwai katon Kitchen sannan kowani ɗaki akwai Tiolet a ciki daman a cikin ɗaya yake zaune ɗaya kuma ya saka kayan motsa jiki. Sai ya ce ɗayan su share ma Inna ɗayan kuma Walida ta zauna a ciki kafin ya san in da zai kai kayan shi.
Su kam ai suna can suna faman zagaya gidab suna murna daman sau ɗaya suka zo gidan tun bayan an gama shi tun lokaci suke  santin gidan. Mariya ma ji ta ke yi kamar ta dawo nan itama su zauna tare da Walida.
Chapter 32 · 0% Book details