Sashe 48
Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hankalin Mimi ya yi bala'in ta shi. Jikinta sai rawa yake yi, ba ta ma san Jaheed ya riƙe ta ba sai bayan da Aji ya bar gidan sannan ta juya da sauri ta koma cikin falon tana rawan jiki da na zuciya saboda tsabar firgita da Irin kallon da ta ga Aji na yi mata
Kamar za ta faɗi har da gudu take haɗawa Jaheed ya bi bayanta yana kiran sunanta amman ina ko jin sa ma ba ta yi, wayar ta na cikin ɗakinta a gaggauce ta shiga ta ɗauko wayar ta fara laluɓan lambar wayarsa ta fara kira amman tana ta ringing amman bai ɗauka ba, da wayar ta tsinke sai ta ƙara kira wajen kira a jere ya fi sau goma amman bai ɗaga ba.
Haka ta fito falo a firgice sai suka ci karo da Hajiya da ta fito daga É—akinta amman yanayin da ta ga Mimi ne ya sa ta san ba lafiya saboda ba ta ma tsaya ba sauri sauri ta wuce ta, Sai Hajiya ta bi bayanta tana kiran sunanta. A falo Jaheed na zaune Baaba Uwani na zaune a kasa a gefensa ta na ta yi masa surutu amman da alamu baya sauraranta mamakin irin tashin hankalin da ya gani a tare da Mimi ne kan wannan Mijin nata da ta ce ba ta son auran yanzu.
Kawai yana zaune sai gani ya yi ta dawo falon kamar za ta fita saboda tsabar ruɗewa. Sai ya miƙe da sauri yana kiran sunanta daidai hajiya ta kawo cikin falon, ta tsaya kawai tana bin su da kallo cikin mamaki, Mimi ta rasa ina za ta je ta ji daɗi, ha waya a hannunta tana sake kiran Aji amman tana ta ringing amman ba ya ɗauka, Jaheed kuma ya ƙariso kusa da ita lokaci ɗaya yana faɗin" Mimi wai saboda ya ganmu ne kika ruɗe haka? To ba kin ce sakin ki zai yi ba?
Tana jin shi sai ta yi kamar ba ta ji ba, Ta cigaba da kiran wayarsa tana matsawa daga gaba zuwa baya. Ganin ba ta tanka sa ba sai ya saka jannu ya riƙo hannunta lokaci ɗaya yana faɗin" Zo ki zauna..'
"Kar ka ƙara taɓani.."
Haka Mimi ta faÉ—a a fusace kamar za ta yi kuka tana yi ma Jaheed wani irin kallo, Hajiya ta karisowa tsakiyar falon lokaci É—aya tana faÉ—in" Me ke faruwa ne?
Ita kuma Baaba Uwani faÉ—i take yi. "Subhanallah Binta me ya faru"
Jaheed kuma sai ya tsaya sororo yana kallon Mimi wacce ta cigaba da danna wayar ta. Sai Hajiya ta juya tana kallon Jaheed lokaci É—aya tana faÉ—in" Jaheedu me ke faruwa ne?
Shi ne ya ɗan yi bayanin ain da ke faruwa ya ƙarishe da faɗin" Ni ban san me ya faru ba kawai na ga duk ta ruɗe saboda ya zo ya ganmu tare ya fita a fusace ta bi shi tana masa magana ya yi banza da ita. Saura Kaɗan fa ya ture ta da mota Hajiya."
Hajiya ta yi shuru ta na kallon Jaheed kafin ta ce"Dole za ta damu mana, mijinta ne fa kuma ba daÉ—i ya zo ya ganku tare."
Cikin mamaki ya ce" Mijinta kuma? Ba ta ce ba ta son auran ba yanzu?
Sai Hajiya ta kasa mgana Mimi kuma tana cikin tashin hankali amman sai da ta watsa ma Jaheed wani banzan kallo kafin ta ce"Da na ce zai sake ni ai ban ce maka ya sake ni ba. Wanda yake ma tunanin zai sake ni to ya daina bayan sallah zan koma gidan Mijina."
Tana gama faɗin haka ta wuce fuu,Sai ya bita ya na ƙara kiran sunanta kawai sai ta juyo a fusace cikin tsawa tana faɗin" Don Allah ka kyaleni, wannan bala'in da me ya yi kama! Kai ba ka ga abin da ka ja min ba ne? In ba so kake yi ka kashemin aure ba ka fitar mana daga gida"
Cikin mamakin kalamanta Jaheed ya nuna kansa yana faÉ—in" Ni yau kike kora daga gidan nan Mimi?.
Kai tsaye ta ce"Eh In dai alheri zai kawo ka ba. Ni ce kuma na gaya maka ina da aure kaai na bibitayata Allah ya baka wata wacce ta fini."
Daga haka ta yi wucewarta ta bar sa nan tsaye baki buÉ—e Baba Uwani ne ke ta jinjina kai, Hajiya kuma sai ta koma ta zauna ta yi shuru ba ta yi mgana ba. Jaheed ya kaÉ—a kai kamar ya yi kwallah kafin ya juya yana faÉ—in" Sai da safe Hajiya.". Ba ta ma amsa masa ba, Baaba Uwani ce ke ce masa bai ko ci wani abu ba ya tsaya mana ya sha ruwa anan ko sauraranta bai yi ba ya fice daga falon da sauri.
Baaba Uwani ta kalli Hajiya kafin ta ce"Hajiya ba ki tsaida shi ba?
Hajiya ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" ƙyale shi kawai."
Baaba Uwani ta yi shuru kafin ta ce" Shike nan Hajiya" daga haka ta wuce ta shiga Kitchen ita dai har ga Allah tana tausayin jaheed sannan ya fi mijin Binta fara'a da son mutane, kuma ga na gida ai gwara na gida da wani bare.
Hajiya ta haÉ—o ma kayan shan ruwa ga abincin da a ka shiryama Aji nan a kamalle waje É—aya, Mimi kuma na cikin É—akinta ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta kira wayar Aji kamar ba gobe amman bai É—aga ba.
Gajiya ta yi ta hakura ta koma ta zauna Gefen gado kamar ta yi kuka, kanta ta dafe lokaci É—aya tana fitar da huci daga bakinta.
Wannan wani irin kishi ne. Wannan kishin na Aji ya na bata tsoro kada ya zame mata wata matsala anan gaba, tunanin kiran Mu'azzan ta yi, Sai ta ga ya na nesa ba amfanin kiran shi. Har Nasir ta yi tunanin kira sai ta fasa. Sai daga baya tunanin kiran wayar Inna Meri ya faɗo mata amman kuma ta na jin Kunya tun bayan barowanta gidan ba ta ƙara kiranta ba sai yanzu ta kira ta ce ta na neman ɗanta. Abun da kunya kamar ta fasa amman kuma ta kasa hakura ta riƙa Allah yasa wayar tana hannun Walida Allah kuma ya amshi addu'arta, tana kiran wayar Inna Walida ta ɗauka ita kuma damab wayar na hannunta, pokacin da ta ga Binta ta ɗauka Bintu ne ba ta ma tsayawa dubawa ba ta ɗauka sai ta ji muryan Mimi tana faɗin" Walida ce?
Sai walida ta sake É—ago wayar tana ganin mai Kiran sai kawai ta daga tsalle tana faÉ—in" Anty Mimi".
Ta faÉ—a cikin tsananin murna. Daman wayar na hannunta a cikin É—akinta tana faman latse latse.
"Walida Yayanki na gida?
Haka kawai Mimi ta faÉ—a.Sai walida ta ce"Anya? Ba ya nan me ya faru?
Sai kawai Mimi ta ce"Bakomai ki gaida Inna." Sai kawai ta katse kiran, abin ya ba ma Walida mamaki ta bi wayar da kallo, to kuma me ya faru? har ta shi ta yi ta fita falo ta iske Inna na zaune daga kallo ta fara gyangyaÉ—i haraban gidan ta leka ta ga motar ba sai mashin tabbacin Yaya Mansoor ba ya gidan kenan sai kawai ta koma É—akinta, Ita da Junoir wanda tun É—azu daman ya yi barci amman sai da ta kashe tibin dake ta yi shi kaÉ—ai, domin Inna na zaune sai faman gyangyaÉ—i take yi.
*****
Mimi na jin cewa Aji baya gida tunaninta ya ba ta yana Camp ɗin su, duk da ba ta taɓa zuwa ba amman tasan wajen yana cikin gari ne. Sai kawai ta ɗauki mayafi ta yafa ta zura wani saukakƙun takalma ta fita falo ta iske Hajiya na shan kayan marmari ita da Baba Uwani ba ta ma tsaya ta kansu ba ta faɗa Kitchen, ta kwashe abincin da ta yi ma Aji ta zuba acikin kwando mai zif ta zage sannan ta fito falon a gaggauce tana faɗin" Hajiya zan je na dawo."
Cikin mamaki Hajiya ta ce" Ina kuma za ki Binta? dare fa ya yi kuma kin yi Azumi amman komai ba ki ci ba."
Kawai wucewa ta yi tana faÉ—in" Hajiya sai na dawo zan iya cin wani abu."
Kafin ma Hajiyar ta sake wata mgana ta fita, Sai da ta fita ta tuna ba ta É—auko Key É—in Mota ba sai ta dawo da gudu gudu ta koma É—aki ta É—auko Key É—in motar ta fice ta na jin Hajiya na faÉ—in"Binta dare fa ya yi"
Ita dai ta fice tana faÉ—in" Hajiya ba zan daÉ—e ba. In sha Allahu"
Ko ba ta faÉ—a ba tunda Hajiya ta ga ta kwashi abinci ta san in da za ta je. Sai kawai ta kaÉ—a kai ta cigaba da shan kankanarta, Duk Binta ta jaa ma kanta da ba ta baro É—akinta ta zo gida ba da duk haka bai faru ba, Baaba Uwani ko mgana ce a bakinta amman yadda Hajiya ta kame fuskarta ya sa ta kasa furta wani abu.
Megadi ma ya yi mamakin fitar Binta da daddare abin da ba ta yi, duk tsiya ana mangariba take dawowa gida. Amman yau bayan mangariba wajen takwas saura ta shiga mota ta fita sai dai ya bi ta da fatan dawowa Lafiya, ita kuma tana tuki amman hankalinta na kan wayarta tana ƙara kiran lambar Aji anman bai ɗauka ba. Kusan ɓacen hanya ta yi ma sai da ta sake komawa tunda ta manta wajen daga karshe sai da ta tsaya a bakin hanya ta yi tambaya sannan a ka yi mata kwatance kai tsaye sai ga ta a bakin get ɗin Gombe United Camp. Akwai Security masu kula da shiga da fita domin tana zuwa sai suka hana ta shiga tun da ba su taɓa ganinta ba.
Sun tambayeta wa take nema?
"Mansoor Aji.."
Kai tsaye Mimi ta faÉ—i sunansa. Security É—in guda biyu ne suna sanye da uniform da kuma manyan fitilu suna haske motar Mimi da ita kanta tunda kamar cikin Camp É—in ya yi duhu ba wuta.