← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 93

Sashe 64

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  Haka ko a ka yi daya ke ɗaurin auran na Rana ne ɗaya da rabi ne. Shi ya sa suka samu ishashen lokaci. A can Bauchi kuwa Mimi ta ga karramawa sosai wajen Maman Bauchi tare da sauran yaran gidan, ta yi mamakin yawan iyalan gidan daman Aji ya gaya mata duka ƴaƴa mata gare shi Allah bai taɓa ba shi haihuwan wani ɗa Namiji ba Sai mata amman kuma Allah na son shi da Rahama tunda da sun taso sai kuma Allah ya kawo musu mazajen da ya ke aurar da su zuwa gare su. Da safiyar ranar bikib an raka Mimi ta je ta gaishe da Baba Yakubu da yake shi  mutun ne mai faɗin mgana kai tsaye, Kai tsaye yace ma Mimi" Ke ce matar Mansoor ɗin?
Ta É—aga kanta sai ya yi mirmishi kafin ya ce"Ba shakka shi ya sa a baya ya yi ta cewa baya so da na ce ya zo gidana na bashi mata sai ya ce min shi bai ce baya son ki ba."
Kan Mimi na ƙasa ba ta yi mgana ba shi kuma bai damu ba sai ya cigaba da faɗin" Duk da fa yaƙi amman ban janye maganata ba,  har yanzu ina da sauran yara in ya na so bazan hana shi ba."

  Ya karishe faɗa da sigar zolaya Maman Bauchi na wajen Sai ta yi saurin cewa" Alhaji mganar nan ai ta wuce ko? Kai dai a matsayinka na uba ka saka ma auran su albarka." Sai ya kaɗa kai kafin ya ce" Haka ne to Allah ya yi ma auran ku albarka"
Mimi ta amsa da Amin acikin ranta maman Bauchi ne ta amsa a Fili.
Sai ya gyara zama lokaci É—aya ya na faÉ—in" Meri ashe ta na can garin su ko? Jiya ta kirani mun gaisa ta ce min É—an'uwanta ne ba shi da lafiya."
Sai Mimi ta ɗaga kanta gefe ɗaya kuma Maman Bauchi sai ta kwace hian suna cikin mganar sai ga Bintu da Anty Halima sun shigo sai a ka haɗu ana ta tattauna mganar kan  Baba karimu da ya samu hatsari Mimi na gefe ba Kasafai ta kan saka musu baki ba.

  Bayan sun baro falon megidan suna komawa ɗakin maman Bauchi da suka sauka suka ƙarya. Sannan suka leka ɗakin da Yalwa ke ciki itama jiki ya yi saukí Sai hamdala. Daga nan sai suka yi wanka suka shirya tunda babu wani aiki duk aikatau su ka kai, ko wanke wanke da shara akwai masu aiki balle su baki da sun ce za su yi wani abu sai Mama ta hana ta ce ga masu aiki sannan ga ƴan'uwanta nan sun zo z su yi komai.  Amaren kuma suna gidan da ke kallon na Baba Kabiru can su ka kwana Bayan sun yi wanka sun shirya Bintu ta ja ta suka koma can gida suna ganin shiryawan Amarya da ƙawayenta.
Mimi ta yi shigar wani leshi ne  jikinsa baki aamman kwalliyarsa ja ne sai ta yi amfani da jan mayafi da takalmi da jaka ja, ba wani kwalliya ta yi ba amman kayan sun karɓeta ta yi wani irin fresh fatar ta na wani irin santsi kamar wata baturiya sannan ɗinkinta mai flenting ne ta baya ya yi mata wani irin cif a jikinta.

  A wajen sai ta zama abun kallo, ga ta yar gayu ga kyau ga kwarjini sannan ga Ilimi da kamala ga turanci domin tana gidan ta samu wayar wani ma'aikacin gidan radion Jamus ba ta yi mamakin in da ya samu labarta ba sun yi mgana da harshen turanci a kan suna son su yi aiki da ita, ba wannan ne na farko ba. Har NTA na ƙasa ma sun kirata D.W ma haka har da BBC, Sai dai ba ta da ra'ayi zuwa ko'ina ta fi kaunar zama a jiharta tun a baya ma balle yanzu da ta yi aure ta auri miji irin Aji ba zai taba barinta ta je wani gari ko ƙasa da sunan aiki ba. To ta sha turanci fa sai ta zama kawai abun kallo in an tambayi Amare wace ce Mimi? Sai su ce matar yayansu ne yaron yayan Abbansu da ya rasu ɗan ƙwallon nan da suke ba su labari saboda suma suna yawan faɗa mana ƙawayen na su suna da wani yaya a Gombe ɗan kwallon kafa ne, to daman mai mata irin Mimi me kuma zai ƙara neman wajen wasu matan? Ai ya gama samun dukkan jin daɗin nan duniya.

  Suna tare da Amaren har a ka ɗaura aure, Tana ma cin alalan da a ka yi ne ta gama cin waina kena  ta samu kiran Aji, yana tambayan ta  tana ina? Sai ta ce suna makota tare da Amare sai ya ce ta fito ga su a waje abun sai ya ba ta mamaki ta tsame hannunta kan abin da take ci ta fita ta wanke hannu ta lulluɓa mayafinta a saman kanta ta fita, ba sa waje ashe suna cikin gida suna gaisawa da mutane ciki ta shiga sai gamu da Yaya Halima sai ta nuna mata ɗakin da Gwaggonsa Yalwa ke ciki tace suna ciki,  ta yi mamakin ganin shi tare da Nasir ko alama bai sanar da ita zuwan shi ba, har da Mommy da Hajiya sun yi waya da safe su ka ce ko mijin nata zai zo ɗaurin aure ne? Sai ta ce musu a'a saboda ba su yi mganar zuwan na shi ba.

  Ta ji daɗin ganinsa kwana biyu kawai sai da ta yi wani irin kewarsa ta na masa mirmishi ya na yi mata, ya sha shadda fara dinkin zamani tqzarce har da hula sai ya yi wani irin kyau kamar ba shi ba.
sun gaisa da Nasir da tambayan yara, Sai kawai ta ce"Da na san za ka zo, da na ce ka zo min da ƙawata."
Nasir na dariya ya ce" Tafiyar ba tawa ba ce, ni kaina sai da safen nan na sani, kin san halin mijin nan naki akwai yi ma mutane karfa karfa."
Wani kallo Aji ya yi ma Nasir shi kuma sai ya na dariya, Yalwa na gefe itama tana mirmishi, nan É—akin a ka kawo musu abinci suka ci, suna gama ci wajen uku da rabi su ka ce za su tafi lokacin Baba Kabirun ma bai dawo ba ya na can yana sallaman bakin da suka zo daga nesa.
Kawai sai Aji ya kira wayar Mimi kai tsaye yacl ce ta shirya ta fito suna jiran ta, Sai mamaki ya kamata saboda ita dai sun yi da shi sai gobe za su koma gida.
Cikin mamaki ta fito ta same su nan ƙofar gida baki a buɗe ta ce" Na ji kace na zo mu tafi ka manta sai gobe za mu koma tare da su Bintu?
Kai tsaye ya ce"Su dai za su dawo gobe amman ke yau za ki koma gida."

  Mimi ta ɓata rai kafin ma ta yi mgana ya ce"Gobe kaɗai gareni jibi za mu tafi katsina wasa sai mun yi sati, kinga ni ba zan je na zauna a gida ni kaɗai ba."
Mimi ta yi kamar za ta yi kuka har ga Allah ita ba ta saka ran komawa a ranar ba,
Kawai sai ta ji ya na rage murya har ya na faÉ—in" kin manta ma jibi za ki koma wajen aiki? Gwara ki zo mu tafi kin ji ko?
Cikin shagwaba ta ce"Su Bintu fa da Anty Halima?
Kai tsaye ya ce" Ina ruwan ki da su? Sun fi ki sanin hanya in sun gama bikinsu za su dawo ke dai ki je ki É—auko jakarki mu ta fi kada mu yi dare a hanya."

  Mimi ba ta da wata mafita dole, ta juya za ta koma cikin gida amman kuma sai ta rasa abin da za ta ce musu kawai sai ta ce za ta bi miji su koma gida? Sai ta dawo ta na ce masa" To ni me zan ce musu? kawai sai nace musu zan bika?
Kallon sama da ƙasa ya yi mata kafin ya buɗe mota ya shiga lokaci ɗaya yana faɗin" To shike nan sai ki zauna."
Ya faÉ—a a fusace dole ya sa ta koma cikin gida ta samu Yaya Halima ta gaya mata ita kuma sai ta yi dariya kafin ta ce"Ki bi mijin ki Mimi ai an gama biki, mu za mu zauna har zuwa jibi kada ki damu."
Yaya Haliman ce ta sanar ma mutane tafiyar Mimi ba wanda ya damu da tafiyarta Maman Bauchi har waje ta raka Mimi da abun arziƙi na jaka da kofunan biki da za su raba, ko Bintu ba ta samu komawa ta yi ma sallama ba suka ɗauki hanya.
Aji ke tuki Nasir na gefen bangaren mai zaman banza, ita kuma Mimi tana baya ta na ɓata rai. Shi ko Aji sai ya basar da ita ya koma suna ta hiran su shi da Nasir.

  Suna hanyar Rukky ta kirata cikin damuwa tana tambayanta ina ta je ta zo gidan ta bata nan? Mimi tace ba ta nan ta je Bauchi amman yanzu tana kan hanyar dawowa.
Yadda ta ji muryan Rukky a sanyaye ne ya sa ta ji jikinta itama ya yi sanyi har sai da ta ce" Me ya faru Rukky? Daga can bangaren Rukky ta ce"Bakomai sai dai kin dawo É—in."
Daga haka sai ta katse wayar sai abun ya ba ma Mimi mamaki kamar  ta yi ma Nasir mgana sai kuma ta fasa  ta bari gwara sai ta koma sai ta kira Rukkyn su yi mgana.
Wajen mangariba suka isa Gombe sun biya gida sun sauke Nasir, wani abun mamaki ita dai Mimi ba ta ga ko sau ɗaya sun yi waya da Rukky ba ahalin kuma ta san a baya ba haka suke ba dole ta fara zargin akwai wani abu a ƙasa.
Chapter 64 · 0% Book details