← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 93

Sashe 65

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

  Haka suka isa gidansu Mimi na shan kamshi, Aji kuma sai ya nuna kamar bai gane ba ya na ta ɗiban ta da mgana ita kuma ta na basar da shi, kuma duk gajiyan nan haka ya saka ta sai da ta yi musu girkin dare ya je ya siyo amman ya ce shi wlh ya daina siyan abinci yana magidanci har da cewa zai taya ta amman kuma ban da ɗauko miko ba abin da ya yi mata. Sai juya kayan miya kawai ko greeting cewa ya yi baya son hannunsa ya taɓa ya ji, ganin da ta yi duk fushin da ta ke yi bai gane ba dole ta saki fuska kamar komai bai faru ba. Daman ya gaya mata ranar litini zai yi tafiya shi ya sa a daran dai kamar in ya tafi ba zai dawo ba. Da kuma safiyar ranar suka tashi da wayar Inna da labarin rasuwar ƙaninta Tanimu, saboda haka za ta jima tunda yanzu sai bayan an yi bakawai, duka dai yaran sun kirata sun yi mata gaisuwa ya yi nisa ba lalle ace sun tashi daganan zuwa can shiyar sakoto ba.

  Ranar lahadin a gida suka yini washegari litini kuma tun safe su Aji suka kama hanyar katsina tare da sauran team ɗin su, Mimi dai ta sha dokoki kada ki yi kaza kada ki yi kaza, har sai da ta gaji da amsawa da To, shi dai ta kular masa da kanta da gidansa,  itama ranar a wajen aiki ta yini ba kuma su haɗu da Rukky ba an ce ta zo ta fi daga baya ta kuma kira wayarta ba ta same ta ba, Bintu ta kirata ta na masa tsiyan shike nan sai ta gudu ta bi mji tana ta dariya nan take gaya mata suma ba su daɗe da shigowa garin ba, an ba su kayan fulawanta gobe Bintun ta ce za ta zo ta kawo mata.
Suna cikin wayar ne ra ga madiha na ta kiranta  bayan sun gama sai ta kira ta wanda tun bayan tarewanta sau ɗaya suka yi mgana nan ta ke gaya mata ta shigo garin tana gidan Hajiya ta na so ta zo ta ga gidanta amman Hajiya tace ta yi tafiya sai ta ce mata ta dawo tun shekaranjiya tana wajen aiki amman in ta ta shi za ta biyo ta gidan Hajiya.

  Haka ko a ka yi da gidan su Rukky ta so ta wuce amman zuwan Madiha ya sa ta fasa,  saƙo ta turama Aji kan cewa Anty Madiha ta zo za ta biya ta gidan Hajiya, da yamma ta je ta iske ta ko a gidan hajiya kamar ita kaɗai ta zo ba yara ba mijin ta ce wasu kaya ne suka kawota za ta ƙarisa Abuja ta ga kayan da ganan ta ga Mommy, sun gaisa sama sama kamar yadda suka saba Madiha sai wani ƙare mata kallo ta ke yi ƙasa ƙasa ita dai a dole sai ta samun abun kushewa sai kuma ga shi ta kasa samu. Duk Mimi na kallonta a ranta tace mai hali dai baya fasa halinsa, amman saboda ta kure Madihan ya sa ta ce mata ta zo su je gidanta ta kwana.
Cikin mamaki ta ce"Gidan ki kuma? Shi mijin na ki fa?
Mimi ta ce"Ko ya na nan akwai É—akuna, balle ma baya nan sun tafi katsina buga wasa."
Hajiya na gefe ta ce" Ai ko dai ki je ki kwana gidan Æ´ar'uwan ki Madiha."
Sai ba ta yi gaddama ba. Bayan sallar Isha'i Mimi ta É—auke ta a motar ta zuwa gidanta Madiha ta sha mamaki domin duk kyan gidan a hoto a fili ya zarce tunaninta.
Acikin bedroom ɗinta ta sauke Madiha ta kuma tuɓe tana ta hidima da ita abincin ta yi musu mai rai da lafiya suka ci suka sha ruwa.

Vduk kushe irin na Madiha ta rasa abun kushewa sai bin ko'ina ta ke yi da kallo, ta na gani Mimi na waya da Aji bayan ya sanar da ita sun sauka lafiya, ita kuma sai take gaya masa ga Yayarta ta zo.
Kai tsaye ya ce"Wacce daga ciki? Ta kaduna ko ta Lagos?
Sai tace masa da ta Lagos abin mamaki sai ya ce ta  bata wayar su gaisa, a karon farko Madiha da Mansoor Aji suka gaisa cikin girmama juna sannan suka yi sallamam
Da dai Madiha ta rasa abun cewa sai ta bige da faÉ—in" Ina fatan dai kuna nan zaune lafiya ko?
Mimi ta ce mata suna nan lafiya kalau. Sai Madiha ta gyara zama lokaci É—aya tana faÉ—in" To gwara dai haka, kar dai ki zauna soyayya É—a namiji ta rufe miki ido, duk da kina aiki ya kamata ki fara tunanin fara wani kasuwancin da kuÉ—in ki."
Kai tsaye Mimi ta ce"To zan yi magana da mijina in sha Allahu."
A karkace Madiha tace"Mijin ki? Au daman kuÉ—in shi ne?
Mimi ta ce"Kuɗina ai kuɗin shi ne tunda ina ƙarkashinsa, ko Mommy ma ta ce duk abin da na gada nawa ne, kada na kuma zartan da wani abu ba tare da na shawarci  mijina ba ko a addinmun hakan ba laifi ba ne, kada kuma ki manta ko yau na faɗi na mutu abin da na tara rabi na shi ne."
Sai Madiha ta kasa mgana saboda ta ga kamar Mimin ta fi ta gaskiya.

  Da yake ba wata sakewa tsakanin su ya sa ba su jima suna hira ba suka kwanta sai da eafe Khadi ta kira Mimin ita ke gaya mata Madiha a gidanta ta kwana kai tsaye Khadi ta ce"Mimi na ji kun fara yawon honneymoom ke da mijin ki, Kaduna ba ta zo muku a layi ba ne?
Mimi na dariya ta ce"Ta kusa zuwa layi in sha Allahu."
Khadi na dariya ta ce" Yauwa, don Allah ku zo mun nima muna da wajen kwana ko wata ne ma za ku iya yi."
Da haka suka rabu bayan ta ce ta miƙa ma Madiha wayar nan ta bar su suna waya ita kuma ta fita zuwa kitchen.

  Tare suka fita Mimin ta sauke Madiha a gidan Daddy za ta gaishe shi itama ba ta tsaya ba ta wuce wajen aiki, tana zuwa bayan ta gama karanta labaran safe ta karisa bangaren su Rukky ta same ta ta zo aiki amman duk ta faɗa ta yi wani iri kamar Rukky ba, Mimi ta damu ta kalli Rukayya lokaci ɗaya tana faɗin"Me ke faruwa ne? Kin ga yadda kika wani lalace? Kuma kin ce za ki zo gida ki same ni kuma ban gan ki ba."
Sai Rukky ta furzar da numfashi kafin ta ce" Ki bari in muka tashi mu je gidanki mu yi magana, nan ba wajen mganar nan ba ne."
Da haka Rukky ta samu kan Mimi ta yarda sai sun ta shi aiki za su tafi gidanta su yi zauna su yi mgana.

  Da wuri suka baro ma'aikatan na su ita da Rukky suna tafe ne amman ba wani mganar da ke shiga tsakanin su, Rukky ta yi tagumi daga ganinta tana cikin dqmuwa Mimi dai ba ta ce mata komai ba amman tana tuki tana kallon Rukky cikin tausaya ba ƙaramin abu ne zai saka Rukky ta zama haka ba, ta ma fita surutu fa amman ji ta ko mgana mai karfi ba ta son yi.
Sun isa gidan amman ko ruwan da ta kawo ma Rukky ba ta sha  ba zaune kawai ta yi , kamar mara lafiya, Mimi ta kariso ta zauna kusa da Rukky lokaci ɗaya tana dafa Kafaɗanta cikin wani yanayi ta ce"Me ke damun ki ne Rukayya? Na damu da ganin ki cikin wannan halin don Allah ki gaya min abin da ke damun ki.?
Rukky ta furzan da numfashi kawai sai ta sakar ma Mimi kuka kamar wata ƙaramar yarinya. Ta ɗora kanta  a saman kafaɗan Mimi tana shesshekan kuka daga gani kukan na fitowa daga ƙasan ranta ne wanda ya daɗe yana cin ta a cikin zuciya ta kasa furtama kowa.

  Mimi ta riƙa lallashinta ta hanyar ɗan bubhuga bayanta da sigar lallashi. Har sai da Rukky ta daina kuka sannan Mimi ta ɗago kanta ta saka hannu tana share mata hawaye lokaci ɗaya tana faɗin" Ki daina kuka ki natsu ki gaya min abin da ke faruwa."
Rukky ta ja numnfashi kafin ta ce"Nasir ne."
Mimi daman ta tsammaci haka amman kuma sai da ta nuna mamakinta kafin ta ce"Me ya faru da Nasir É—in? Ko kun yi faÉ—a ne?
Chapter 65 · 0% Book details