← Book details Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 93

Sashe 58

Idan An Ciza Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka ko a ka yi, Inna ya yi ma shirin tafiya da kuÉ—in mota da abin da za ta je da shi, ita kaÉ—ai ta tafi, Walida kaÉ—ai aka bari a gida da farko har Mimi ta ce ta dawo gidansu ta zauna kafin Innar ta dawo. Gogan ya ce a'a bai gama cin amarcinsa ba. Ko ta koma gidan Bintu ko kuma a nemi wata mafitar to sai ga shi ma Mariya ta ce za ta zo ta ya ta zama har Inna ta dawo tunda jikin Magajiyar da sauki, shike nan sai a ka samu mafita Inna Meri kuma ta je ta iske jikin Yalwa sai a hankali daga kwana huÉ—u sai ga ta ta yi sati amman tana waya da Æ´ayanta suna jin halin da ake ciki.
Ta ce za ta ɗan kwana biyu saboda ta kula da Yalwan an kaita asibitin Bauchi, Baba Yakubu ma ya taimaka, a gidansa suka sauka ana ta faman hidiman asibiti. Ganin Inna Meri sama da sati biyu ba ta nan ya sa suka yi magana da Mu'azzam gwara ya je Bauchin ya duba su, sun shirya tafiya tare da Mimi amman kuma sai zuwan su Mommy ya sa tafiyar da ita bai yu yu ba, shima a ranar bai tafin ba sun yi Meeting sai a washegari amman a daran sun je gidan Hajiya sun gaida Mommy da Inna Zainaba kano ta fara sauka shi ne suka ƙariso gamobe tare.

Mimi ta yi mamakin ganin yadda Aji ya zauna suna ta hira da Mommy kamar ba shi ba daman Dr shima ya gaya mata suna waya sosai, balle Daddy da sai dai ta ji ya ce mun yi mgana da Daddy ya ce ya na gaishe ki. Washegari ya kama hanyar Bauchi tare da Yaya Halima da ta tambayi izini a ka barta sun je sun iske jikin yalwa da sauki amman duk ta rame Inna da matan Baba Yakubu ke kula da ita ciwon sugar ne bai kwana ba a ranar ya juyo amman nan ya bar Yaya Halima za su dawo da Inna nan da kwana uku, tun da nan gidan Baba yakubu za'a bar Yalwa saboda tana zuwa ganin likita sai zuwa gaba in ta ƙara murmurewa sai ta koma tunda can Karimu ma yana fama da kansa ne, ƴayan Gwaggo Yalwan ma kowa na ta kanshi da iyalansa ne.

*****

Bayan wata É—aya.
02:20AM.

Suna ƙamkame da juna, ba su daɗe da samun natsuwa ba, sun yi wanka sun tsarkake jikinsu saboda babu kyau zama cikin najasa, sun lulluɓe jikinsu da bargo har zuwa cikin su, kansu na kan matashi guda ɗaya sun kuma juya suna fuskantar juna bayan sun kamkame juna kamar za'a raba su, Mimi nata wasa da suman kan Aji ba tare da ta yi mgana ba amman sun taru sun yi shuru suna jin bugun numfashin juna ɗakin ya yi duhu amman akwai iskar fanka kaɗan kaɗan yana hurasu lokaci ɗaya yana yawo da labulen window ɗin bedroom ɗin Aji.

Kitso Mimi take yi masa sai ta yi sai ya warware duk ta yamutsa masa gashin kai, da ya gaji ya riƙe mata hannuwa lokaci ɗaya yana faɗin" Yarinya ta ga gashi ba irin na ta ba." Dariya ta yi masa ta na shafa kitson dake kanta a wajen aiki Aisha Farida ta yi mata da kuma ta ce a wajen aiki aka yi mata sai ta tuna diraman da suka kwasa tsakanin da Aji faɗa ya fara yi mata me ya sa ta je ta buɗe gashinta gaban maza, an taɓa yin wani kitso ne a wajen aiki ban da wulakancin? Ta yi masa bayanin a wani keɓantattacen waje ne maza ma basa shigowa amman ya kasa ganewa amman ya gargaɗeta kada ta sake yin irin haka baya so, dole ta koma tana ban hakuri domin ta manta waye take aure shi ya sa ta ba shi wannan labarin.

Hannunsa ta kama ta É—ora bisa kanta tana faÉ—in" Ka ji bambamcin ko sai na yi maka bayani?
Shafa kanta ya yi kafin ya ce"Tsawon gashi kawai za ki fi ni, amman santsi wane mutum? Ni fa da ina da barin shi ya taru da tuni na fiki gashi."
"Me ya sa to ba ka bar shi ya tarun ba? Ai da yanzu sai ka fara kitso."
Ta faÉ—a tana Æ´ar dariya kara jawo ta jikinsa ya yi lokaci É—aya yana faÉ—in" Inna ba ta so ta ga na tara gashi, ni kuma ina so amman saboda ita na ke ragewa shi ya sa in dai zan je gida sai na saka huka saboda ba na son ta yi min faÉ—an na tara suma ban yi aski ba."
Mimi ta kara tusa yatsunta a cikin sumar kansa da ya tara, sai kamshi take yi tunda ta na shan gyara kafin ta ce" Nima ina so zan dinga yi maka kitso ka ji."
Sai ya tura mata kan yana cewa"Ki yi mana, Za ki tsefe shi da kanki ne yarinya."
Ta fara curkuÉ—a masa kan amman kitson baya kamuwa da ta yi sai ya warware, gajiya ya yi ya janye kansa yana faÉ—in"Mu yi barci MIAJ." Galala ta yi ta na kallon shi a cikin duhun É—akin saboda mamakin sunan da ya kirata, to a ina ya san tana amfani da wannan sunan? Tana cikin tunanin ya É—ago kanta ya É—ora saman kirjinsa ya kamkameta yana faÉ—in"Kina mamakin a ina na san wannan sunan ko?
Bai ba ta damar mgana ya cigaba da faÉ—in" Na san ki, na san ke kike amfani da sunan Miaj da boyayyen account É—in da kika buÉ—e saboda ni."
Mimi ta zaro ido kafin tac e"Ka sani ka ce fa? To ta ya ya?
Mirmishi ya yi kafin ya ce"Mun zama É—aya lokaci ya yi da za ki san wasu abubuwan da yawa waÉ—anda ba ki sani ba Fatima."

Goshinta ya sumbata kafin ya ce"Ina son ki, na yi miki wani irin so mai tsananin da na kusa mutuwa saboda soyayyarki Mimi, bayan dawowata daga gidanku da faruwar abin da ya faru kaɗan ya rage ban hqkura da rayuwa ta ba. Sanadin ki na sallama Komai ina tunanin in ba ki cikin rayuwata mafarkina bai cika ba, ciwon rasaki sama da shekaru goma ya ke damun zuciyata bayan ke ban ñara ganin wata mace da sunan so ko vurgewa ba. Shi ya sa na sha gaya miki ke ce a jiya da gobe da shekaranjya da jibi a cikin zuciyata ba ki da kishiya ke ɗin da na zaɓa tun farko na kuma ƙasa sauya ki Fatima. Soyayyarki ce duk ta wahalar da ni ta sakani na riƙa rayuwa dabam da na sauran mutane, gani nake yi duk abin da ya faru babanki ne ya yi sanadin faruwan shi da farko ba na bibiyanki saboda Ina so na manta dake amman daga lokacin dana fahimci ina sonki ba kuma zan taɓa daina sonki ba sai na fara bibiyan ki a lokacin kina Univesity of Ibadan har ranar graduation ɗin ku ina cikin makarantar ku, na ganki amman ke ba ki ganni ba."
Mamaki ya kama Mimi cikin alj'abi ta ce"Ka je har ibadan?

Aji ya gyaɗa kai kafin ya ce"E. mana, na je har hoton ki na ɗauka a lokacin zan nuna miki da safe, ina bibiyan duka motsin ki saboda ina so na gani ko kin manta dani sai na samu tabbacin ke ma ba ki manta da ni ba. Dawowarki Abuja ya sa na cire rai dake saboda na san mahaifinki ba zai bani auran ki ba,nima kuma na haramta ma kaina ke a lokacin na fita batun ki daga bibiyanki amman kin kasa fita daga rayuwata faɗawata harkan kwallon kafa ya sa lokacina ya zama ragagge. Sai ya riƙa ɗauke min hankali daga tunani da shiga damuwa amman na kasa mantawa dake, a cikin kirjina na ke jin kuna amman ina samun salama in nasan ke ma ba ki yi aure ba, kamar yadda nima ba wata ƴa mace a gaba na.Nasan ke ce mai accuout ɗin Miaj kuma ba wani ya gaya min ba a jikina na ji hakan ko daga yadda kike yawan bibiyata, amman ban tuna nuna miki na gane ki ba. Na dawo da sanin komai na rayuwarki ne daga fara aikin da gidan Tv hankalina ya tashi kin san ina da bala'in ki shi ba na so na ga wasu mazan suna yabon ki, ko suna ambaton kin birgesu, kuna nake ji in na tuna kina can kina birge wasu mazan, na kalli hiran da kika yi a gidan talabijin ɗin ku kina ba da labarin ki da yanayin yadda a ka riƙa comments na yabawa gare ki, kwana na yi ban yi barci ba sai na fahimci duk ɗauriyata ba zan iya ba Na fi ki farincikin haɗuwata dake a Dinner bikin Makama domin ganin ki ya sa na ji kamar zan iya samun ki. Sai dai na kasa ba ma zuciyata dama kan abin da take so saboda tunanin abin da mahaifinki ya yi min.
Chapter 58 · 0% Book details