← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 52

Sashe 9

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana da hasken fata daidai misali, Wanda daka kalle ta kai kasan ba hasken fatar bane kad'ai hadda tsabar Hutu da kwanciyar hankali. Abunda yafi d'aukar hankali a jikin ta be wuce surar taba. Wato idan boobs na wa mace yawa to zamu iya cewa har yawa Haajar yawa ,daga daidai hak'ark'arin ta kuma zuwa cikin ta ,a lafe yake abunda abunda ke kira (flat tummy), daga k'ugunta kuma ya baje. A tak'aice dai Haajar na d'aya daga cikin matan da ake kira a hausance masu siffar koka-kola, a turance kuma tana cikin mata da bature ke kira (MODERATE),,,,,komai nata me kyau ne, ba namiji ba ko mace ta kalli Haajar zata so ta k'ara kallon ta, komai nata me kyau ne da tsari ,se a yanzu suxee ta gane dalilin daya sa Haajar ta lizimci saka hijabi, Dan daga jiya zuwa yau ,so d'aya ta lura haajar ta cire hijabi ,shine da zata shiga wanka, kuma tana gama shirin ta ,wani hijabin ta d'auko ta saka me hannu. Hijabin data saka wa kuma be hana ka gane ita d'in me shape ce ,sedai yana taimakawa wajen rage ido akan ta ,ba kamar idan babu hijabin a jikin taba...

A hankali Suxee ta furta "fataba rakallahu ahsanul khaliqin"...

MUJE ZUWA💃

TAKU HAR KULLUM

SIDIYA...✍️
[7/19, 9:27 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠

*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)

*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*

_BABI NA GOMA SHA UKU_

*________________________*

_Koda suka fito a parlour suka taradda su daddy. Cike da k'warewar zamantakewar rayuwa na yau da kullum Haajar ta k'arasa tana fad'in_

_"Allah sarki Dan Allah kuyi hak'uri nasan kuna ta jira ,ni ban ma zata kun tashi bane"_

"Au to bari kar mu tashi ,tunda ana cin bacci a k'washi ne" inji Hajj Jamil kenan.

Shidai Daddy se dariya yake musu. D'an gurfa nawa Haajar tayi ta gaishe da Daddy ,fuska a sake ya amsata ,sannan ta gaishe da Hajj Jamil cike da girmama wa. Su suxee ma k'arasowa suka yi ,suka gaishe su a ladabce. Hajj Jamil janyo Auta yayi yana fad'in

"Autar daddy yaya? Kinsha bacci ko?"

Itadai auta se gyad'a masa kai take yi ,Dan tana da wani Abu d'aya ba ,matuqar tazo bak'on wuri koma wa take yadda kasan ruwa ya tafi da ita ,wannan kuma ba tarbiyyan kowa bane face Haseena, ba kuma wai Dan basu saba da Hajj Jamil bane ,har gidan shi suna zuwa lokaci bayan lokaci ,se dai basu tab'a zuwa sun kwana bane ,shiyasa suka kasa sabawa da gidan ,sannan da ace akwai qawance me k'arfi ne tsakanin kubra da Hajiya zaliha matar Hajj Jamil to da shak'uwar tafi yawa ,to kubra bata qawance se daidai da ita ,Hajiya zaliha bata cikin tsarin irin matan da ajin su yakai a wajen kubra, Hajj Jamil dai da daddy su suke Abokan tan su cike da nuna wa juna qauna, Dan da sun biye matan su ma baza su yi ba ,to se Allah yasa Abokan takan su bana yanzu bane ,Abotar su ta samu asali ne tun suna yara ,komai nasu tare suke yi ,har suka zama kamar 'yan uwan juna ,duk abunda ya shafi d'aya kamar ya shafi d'aya ne...

Su suxee kujera suka ja suka zauna ,inda Haajar ke serving d'in su ,su daddy ta fara zuba wa ,sannan ta zuba wasu haseena ,kowa yaci abincin se santi suke yi ,banda Auta da se wani cakalan abincin take yi, Haajar na lura da ita tace

"Auta ya ke bakya cin abincin?"

Cike da shagwab'a Auta tace
"Ni na k'oshi"

Karaf Haseena ta k'wace zancen "A-hap! Auta ce fa, ai wallahi baki ga komai ba indai wajen cin abinci ne ,haka take"

"A'a ba wani ,Ku dai bakwa mata yadda zata ci d'in ne." Cewar Haajar ,sannan taci gaba da cewa "Auta zaki sha chocolate? " da sauri Auta ta kad'a kai ,Dan an ambato mata favourite d'in ta.

Haajar taci gaba da cewa "yauwa to taso abinki kinji ,indai kika ci abinci sosai naga kinci ,to zan baki chocolate kisha kin ji".
Mak'e ka fad'a Auta tayi alamar rashin yadda. Wanda seda abun ya bama kusan kowa dake wurin dariya , itama Haajar d'in dariya take ,tashi tayi taje d'aki ,ta d'auko mata chocolate d'in tare da cewa " kin gani ko ,to zaki ci se in baki"

Ba musu Auta ta sauka kan carpet inda Haajar d'in ke zaune da plate d'in abinci. A baki tashiga bata ,har seda taci sosai ,sannan ta mik'a mata chocolate d'in. Kowa se jinjina lamarin yake ,yau Auta ce taci abinci sosai haka, Daddy kam abun ba k'aramin burge shi yayi ba ,dan yana matuqar son a nuna wa yaran shi kulawa...

Bayan sun kammala, Haajar da Suxee suka kwashe komai suka kai kitchen, haseena kuma ta tsaftace dinning area d'in. Daga nan daddy da Hajj Jamil suka koma parlour suna ta tattauna matsalolin yau da kullum, a inda su Haajar suka fara shirye-shiryen d'ora abincin rana.

A tattaunawan da Daddy keyi da Hajj Jamil ne yake sheda masa tafiyar zuwa kano. "To amma tafiyan Nada muhimmanci ne?" Hajj Jamil ya tambaye shi

Daddy yace "eh to Hajiya Gwaggo ce ke kirana ,kasan wancan zuwan Dana yi bata da lafiya an tafi da ita Sudan, to nasan baze wuce labarin auren khaltum da akayi bata nan ba"

Ajiyan zuciya Hajj Jamil ya sauke ,kafin yace "To ina ganin kaje kai kad'ai kabar su Hajiya k'arama anan ,Dan kar kaje dasu kuma Abu na babban gida ,se ya zama gutsiri tsoma, in yaso duk yadda kuka yi Seka sanar mun"

Cike dajin dad'i ,daddy yace

"To shikenan.

" kwana nawa zaka yi? Hajj Jamil ya tambaye shi

Daddy yace "Har wani kwana ki zan ke inyi ,inaga cikin ma nayi in kwana d'aya ko biyu".

" to ba damuwa ,Allah ya kaika lafiya ,ya kuma dawo dakai lafiya"

Daddy ya amsa da "Ameen"

Seda suka ci abincin rana ,Daddy ke sheda wa suxee tafiyan shi ,sosai taji dad'in daya ce ze bar su a gidan Hajj Jamil ,Dan dama abun da ke ranta kenan ,badan komai ba sedan Haajar ,lura akwai abubuwan k'aruwa sosai da baiwa a tattare da Haajar. Addu'a ta masa na Allah ya tsare.

Misalin k'arfe uku na rana Hajj Jamil yakai daddy Airport, tare da masa addu'an Allah yasa suji alkhairi, duk da a k'asan zuciyar Hajj Jamil yasan Abu ne me wuyan gaske ace Hajiya Gwaggo tayi wa mutum kiran azziki, amma ba yadda ya iya ,sedai yabi lamarin da Addu'a...

_GARIN KANO, HAD'EJA ROAD..._

MUJE ZUWA💃

TAKU HAR KULLUM

SIDIYA...✍️
[7/20, 2:45 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠

*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)

*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*

_BABI NA SHA HUD'U_

*__________________________*

_Daddy na isa kai tsaye sashen Hajiya Gwaggo ya nufa ,be ko yi tunanin fara ganin hajiyar shi ba ,Dan kuwa matuqar Hajiya Gwaggo ta samu labarin seda ya biya can kafin ya shigo wurin ta ,to fa jarabar duniya se Wanda ta manta ,kai bashi kad'ai ba hatta hajiyar tashi ya ja mata jangum. Gashi dai asalin mijin Hajiya Gwaggon ya rasu ,wato kakan daddy namiji ,amma bashi yasa Hajiya Gwaggo ta canza wasu halayen nata ba ,ita ke mulkin komai tun kakan daddy Nada rai ,ba Wanda ya isa ya d'aga d'an tsaya matuqar tana wuri ,da tace 'Eh' kuma ba a haifi Wanda ze ce a'ah ba, kishiyar ta Hajiya sakina ba k'aramin wahala tasha ba a hannun Hajiya Gwaggo ,musamman ita da yaran ta mata ne gaba d'aya ,bata tab'a haihuwan namiji ba ,ita ko Hajiya Gwaggo yaranta biyar maza ,kakan daddy shine Auta ,to fa se abunda ta b'ata, wannan yasa lokacin da me gidan ya rasu ,ta kame komai tayi kane -Kane ,rabon gado ma da akace za'ayi hana wa tayi ,daga k'arshe ma kawai se ta kuka ,wai dama so ake ya mutu aci gado ,to ba abunda ya isa matuqar tana da rai , ba yadda za'ayi da ita ,haka aka hak'ura aka k'yale ta ,haka dai kishiryar tata ke zaman hak'uri a gidan ,da Allah ya tashi nuna ikon shi ma ,gaba d'aya yaran Hajiya sakina biyar mata ,manya-manyan attajirai suka aura ,daga wacce ta aura mijin ta bako sisi ,suka kud'ance tare ,se wacce taje ta taradda azzikin, ba yadda basu yi ba akan ta koma d'aya daga cikin gidajen da aka Gina mata amma ina k'yameme Hajiya sakina tak'i ,saboda ta saba da zaman wannan family house d'in. Duk kuma lokacin da zasu zo da abun azziki ,ko da basu yi niyyar bawa Hajiya Gwaggo ba ,tilas Hajiya sakina ke matsa musu se sun je sun bata, saboda a zauna lafiya ,sannan rayuwar mu ba d'aya ba ,Hajiya sakina mace ce me sauqin hali da faranfaran da mutane ,ita ko Hajiya Gwaggo tak'adarin budurci ne ke yawo akanta sama da shekaru aru aru Ana Abu d'aya, da Allah ma yaso nuna mata ishara ,kaf a 'ya'yan ta mazan nan data ke tak'amar ta Haifa gwal ,Alhaji k'arami Baban Daddy shine kad'ai Wanda Allah ya d'aga a cikin su ,shiyasa komai nashi take ham-ham. Sannan kaf a sauran 'ya'yan daga Wanda yabar 'kasa zuwa Neman nakan shi ,se Wanda yana wani gari da iyalan sa ,Baban daddy ne kawai tayi wa kafi a kusa da ita. To sauqin suma tsufa daya kamata gadan-gadan ,ciwon yau daban na gobe daban. Wannan kenan..._

_Sallama yayi ,ba kowa a sashen duk mutanen gidan suna sashen Hajiya sakina ,Dan kusan kullum acan ake wuni. K'arasa wa yayi suka gaggaisa ,Hajiya sakina na tambayar shi iyalan sa ,yace duk suna lafiya. Ba wani jimawa yayi ba ,Dan yasan masifar kakar tashi ,yace wa Hajiya sakina_

"Bari inje mu gaisa da Hajiya Gwaggo"

Tace "To shikenan. Ga wannan hurar me sanyi kaje da ita kasha ,yanzu na gama damun ta kaga ludayi nan gashi, nasan an kwaso hanya" ta mik'awa daddy k'waryan furan ,daya ji kidirmo ,ga k'ank'ara an farfasa a ciki. Kai daga ganin furar nan zata yi dad'i musamman irin lokacin zafin nan...lolz😛
Chapter 9 · 0% Book details