← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 52

Sashe 22

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wallahi duk Sharrin mutum duk hassadarsa in Ya matsa maka in kayi Wannan sha da Wankan wallahi sai Ya Koma kansa da yardar ALLAH kuma duk me son ganin bayanka wallahi saidai kai Kaga bayansa, batun Jifa ko sammu ko hassada ko kiyayya cikin lokaci Guda yake ruguzawa, sannan yana boye kurwa (spirit/Arwah) mayu baza su ga kurwarka ba bare su tab'a ka, kuma in mutum yana Cutar da kai daga ranar da kayi Wannan sha da Wankan wallahi Allah zai gwada maka shi ko ita a cikin barcinka a mafarki, in ka gani Kar kace masa/mata komai, ka godewa Allah ka cigaba da neman kariya Kawai... Wannan kenan a tak'aice ,fatar Allah ya k'ara karemu daga sharrin masu sharri...
Domin Neman k'arin bayani zaku iya tuntub'ar Mlm Abdulrashid Adam Ahmad d'an baiwa kan wannan lambar 08060606050.

Lubabatu har ta zuqunna zata d'au marfin tankin ,haseena ta k'araso a guje Wanda har seda ta bangaje lubabatu ,idan kaga yadda tayo gadon kai kace biyo ta akayi, Ba shiri lubabatu ta saki marfin ta kama hannun k'ofar parloun daddy ta shige ,dawo wa haseena tayi da gudu tace wa Haajar "Anty Haajar kiyi sauri ki zuba waccan matar ce ,kuma zata iya fitowa, cikin hanzari Haajar ta tattaka matakalan tahau ta juye ruwan maganin sannan haseena suka mik'a mata marfin tankin ta kulle ta sauko.

Da sauri suka bar wajen ,se haseena suka bari data zuk'unna wajen famfon dake gefen wajen tayi kamar tana wanke fuska... Lubabatu ce ta fito cike da tsiwa ,tana fad'in

" Ke!ke!"

Haseena tayi banza da ita. Seda lubabatu ta k'araso har inda haseenan ke wasa da ruwan famfo ta sakar mata duk a gadon baya "ke kurma ce? Baki ji ina miki magana bane?"

D'agowa haseena tayi tana mata wani kallon raini tare da cewa "dama magana kike? Ai ban d'auka dani kike ba. To da can baki San sunana bane kike ta famar wahalar da fatar bakin ki?"

A hasale lubabatu tace "Bansani ba"

Cike da tsiwa Haseena tace "da kince MISBAHU ma ai da base kin k'araso ba zan juyo ,Dan mune kad'ai 'ya'ya a _GIDAN MISBAHU_, kuma duk inda naji wannan sunan dole zan waiga inji ko lafiya saboda muhimmanci me sunan a waje na" haseena ta fad'a ko a jikin ta...

Ihu lubabatu ta mata "keeee! Karki kuskura ki kawo mun raini k'aramar Mara kunya"... Hannu ta d'aka zata kaiwa Haseena duka

Bata rufe baki ba itama haseena ta daka mata tsawo tare da nuna mata Dan yatsa alamar kashe di " Karki kuskura. Ki tsaya iya matsayin ki amma banda kaiwa kura harawar rago, Dan kuwa ba abincin ta bane. K'ashi se kare shi kuma nama se kura. Is better u mind u own business"... Tana gama fad'ar hakan taja wani siririn tsaki tare da barin waje.

Takaici ne ya taru ya tsaya wa lubabatu a wuya ,ta rasa yadda zatayi ,abubuwa sun cakud'e mata ,ga wancan yanzu kuma ga wannan. Cike da b'acin rai tama fasa komawa sashen daddy ,sashen ta ta wuce kai tsaye, Dan tsabar bak'in ciki ma ko ta kan marfin tankin bata k'ara bi ba...

Bayan haseena ta koma sashen su, ta taradda su Haajar na jiran ta. Tambayar ta sukayi ya tayi da lubabatu Dan basa so ace ta gano ,muddin ta gane an zuba wani Abu a ruwan nan to zata ma iya hana daddy yayi wanka dashi ,wannan shine fargaban Haajar. Haseena tace Ku manta da wannan na gama da matsalar ta.

Haajar tace "A'ah fa"

Suxee tace "Anty Haajar I trust haseena ,she can do more than dis"

Haseena tace "4get kawai. Akan wannan gayen, na tambayi me gadi yace wai Daddy yace ya dinga barin shi yana shigowa saboda k'anin matar shi ne, amma duk da haka ya kamata mu kula sosai ,zan kuma ci gaba da saka musu ido. Yanzu menene next?""...

Da haka dai suka ci gaba da tattaunawa akan yadda tsarin su ze kasance. Wanda a b'angaren Lubabatu ma kusan raba dare tayi tana tufka da warwara.....

MUJE ZUWA💃

TAKU HAR KULLUM

SIDIYA...✍️

[8/7, 11:58 AM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠

*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)

*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*

_BABI NA TALATIN DA D'AYA_

*____________________________*

_Da daddare bayan daddy ya dawo kuwa akayi sa'a yayi wanka ,ruwan maganin ya tab'a jikin shi. Tunda daddy ya shiga ruwan nan ya sauka akan shi gaba d'aya yaji kamar an zare masa lakkar jikin shi ,shi dai yasan lafiya qalau ya dawo ,amma yanzu wasu 'yan sauye sauye yake ji a jikin shi Wanda ya kasa gane ko menene ,ba zazzab'i ba balle yace ko rashin lafiya ne ,balle yunwa Dan daya fita seda ya biya ta gidan Hajj Jamil dam ya ciko masa cikin shi, to amma ya rasa me ke masa dad'i._

_Zama yayi har kusan d'aya na dare ya fara tunanin wasu abubuwan da suka wuce ,daya ga dai wannan baze fish she shiba haka ya tashi ya d'auro alwala ya gabatar da sallan lafila ,yayi addu'o'i sosai akan Allah ya shiga lamarin gidan shi ya kuma kawo masa sauyi na alkhairi cikin gaggawa ,,,,wannan shine addu'an shi na k'arshe kafin ya Shafa yaci gaba da zama akan dadduman. Abun mamaki a karo na farko kenan da daddy ya tab'a tashi yayi sallar dare ya rok'i Allah akan sha'anin gidan shi, ba baya sallan daren ba yana yi idan buqatun shi sun taso na kasuwanci ,amma dai akan gidan shi kam kamar wannan ne na farko, be kuma San dalilin daya sa baya iya kai kukan shi ga Allah game da sha'anin gidan shiba, ya dad'e akan sallaye zaune har bacci ya soma d'aukan shi. A baccin Dave wuce mintuna talatin ba yayi wani rikitaccen mafarki daya kasa gane shi..._

Farkawa yayi Kamar daga sama ya fara jiyo hayaniya, hankalin shi be gama natsuwa ba se jin yayi an sa key ana bud'e k'ofar parloun shi tare da banko k'ofar ,shi dai daddy gaba d'aya ya kasa koda motsi zaune yake darsashan kamar an dasa icen karas ya zuba wa sarautar Allah ido yaga waye me shigowa...

Wasu manya manyan gardawa ya gani su uku ko wanne d'auke da bindiga k'irar AK47 fuskokin su rufe da bak'in k'yalle ,ba abunda zaka iya hangowa daga fuskar su se idanuwa. Da ga suka ja daidai inda daddy ke zaune kan sallaya ,be k'arewa idanuwan shi kallo ba seda yaga wani ya shigo yana janye da mutum ,seda suka kawo daidai inda yake sannan suka je fata. Ya duba wa ze gani idan ba Haajar ba ,fuska da idanuwan nan nata sun kad'e sunyi jajir ,gata duk a d'ad'd'aure da igila kamar goro, hatta bakin ta k'yalle suka saka suka k'ulle Dan kar ta musu hayaniya,,,, kaida ka gani base ka tambaya ba kasan 'yan fashi ne kuma guma-guman ,marasa imani...

Da sauri daddy ya mik'e yana fad'in "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!!"

Wani daga cikin su ne yayi nasarar maida shi zaune ,ta hanyar daka masa kan bindiga a kafad'a. Koma wa zaune Daddy yayi tare da sake maimaita Kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!". Har so uku.

K'ofa suka wangale masa ya hango Suxee ,haseena da Auta duk an d'ad'd'aure su a jikin bishiyar dake kallon sashen shi ,ko wacce an rufe mata baki da k'yalle ihun su baza'a ji ba sedai gunguni...

Nan fa hankalin Daddy idan yayi dubu ya sake tashi. Lallai wannan musibar babba ce ,ya furta a cikin ran shi ,ya sake furta Allah gamu gare ka k'asa-k'asa da muryar da shi kad'ai ze iya jiyo abunda yace.

Dak'yar daddy ya iya tattaro wata nutsuwa data k'wace masa had'id'a wata jarumta Wanda shi kanshi be San yana da ita ba, idanuwan shine suka kad'e suka canza launi zuwa ja jamar Wanda aka watsawa barkono Dan tsabar tafasar da zuciyar shi ke yi. Har wani kokuwa lab'b'ansa na k'asa Dana sama keyi wajen furta

" Me kuke so?"

Babban cikin su daya wurgo Haajar ciki ,ya k'araso ya zauna kan kushin tare da d'ora k'afar shi kan gadon bayan Haajar dake kwance malala a k'asa tana shashsheka, yace cike da k'warewa kan aikin shi na ta'addanci "Saurin me kake yi? Dama kana tunanin munzo shan shayi ne ko cin gurasa? Sanin kanka ne Azziki baya kawo mu se tsiya. Daka kwantar da hankalin ma ai zamu gaya maka meke tafe damu Wanda zamu tabbatar maka daba shawarar ka muke nema ba umurni muke baka"...

Bakin daddy be mutu ba sake cewa " Ku gaya mun me kuke so ,idan kud'i ne zan Baku amma kar Ku kuskura Ku tab'a mun iyalina"..

Wani shed'anin dariya wannan d'an ta'addan ya fashe dashi ,seda ya tsagaita sannan yace "kud'i!!! Kud'i kace ko? To daga naira d'aya zuwa naira million hamsin zan iya magance maka idan kana da buqata, kud'in ka chicken change dahar kake mun barazana dasu ,ka adana su dakyau Dan nasan zasu maka amfani wajen cefanan gobe, sakarai kawai"...

Ran daddy iya b'aci ya fara kaiwa maqura Dan kuwa jikin shi har cira yake yi ,Dan ya gane wannan b'arayin ba kud'i ne ya kawo suba illa cin mutunci...

Ogan tashi yayi daga zaune ya fara zagaye su daddy dake tsakiyar su se kace wani gafiya ,yafe yake yana Jan zungureriyar bindigar shi a k'asa dake k'ara tsabar taji ado da albarusai zagaye da ita...

Yace cikin kakkausar murya "Naji ka ambaci iyalin ka ko? Wannan" ya nuna Haajar da bindiga itama iyalinka ce?"

Shiru daddy be amsa suba. Wani irin shed'anin dariya ya sake fashewa dashi kafin yace "Zan kuwa so ka tabbatar mun da haka. Ka kawo yarinya me kyau irin wannan ka aje a gidan ka da sunan holewa kana yaudaran mutane. Gata kyaky-kyawar gaske kuwa" ya k'arasa maganan tare da zuk'unna wa daidai setin fuskar Haajar yana kwashe gashin daya rufe mata ido...

Wani d'aci da takaici ne ya daki k'irjin daddy ,Wanda ya haifar masa da wani irin kishi dashi kanshi be San yana dashi ba, a hasale ya sake maimaita tambayar shi "Nace Ku gayamun me kuke so in Baku Ku fita Ku bar mun gida na"
Chapter 22 · 0% Book details