← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 52

Sashe 31

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Barr dake zaune kan kujera mazaunin mutum d'aya ,yana ganin hajiya ta fito ,har k'asa ya zuqunna yana gaishe ta, tare da jajanta mata kan abun da ya faru. Barr Kabir ba tun yau ya san hajiya ba ,da kuma tarin alkhairan da hajiya ta yi masa a rayuwa, Dan karatun da ya je yayo game da shari'a a qasar waje Allah ne sanadi hajiya ce sanadi ,Dan ita ta biya masa komai da komai ba tare ma da daddy ya sa ni ba. Wannan na d'aya daga cikin abunda yasa ba zai taba iya mantawa da hajiya ba. Auren sa na farko ma hajiya ce ta nema masa ta kuma yi masa komai duk a sanadiyyar zaman shi abokin daddy na k'uruciya kuma an yi zaman mutunci da iyayen shi lokacin da suke raye. Wanda Allah ya yiwa matar tashi rasuwa wajen haihuwa ,bayan ta Haifa masa 'ya mace wacce taci sunan hajiyar daddy suna kiran ta da HAJIYEYE. Zaman lafiya da soyayyar da Barr Kabir yayi da marigayiyar matar shi yasa ya kasa k'ara aure sama da shekaru bakwai ,kullum jiya iya yau ,hajiya ta yi masa fad'a amma koda yaushe maganar Barr Kabir shine shi fa a ganin shi ba ze tab'a samun wacce zata maye masa gurbin matar sa ba. Daga k'arshe ma da hajiya ta matsa masa ,sai ya ce ta sake nemo masa ,in dai ita ce zata nemo masa ya yi mata alqawarin ze yi aure Dan ba yada shakku ko haufi akan zab'in hajiya. Tun daga wannan lokacin hajiya ta sarara masa ,Dan a cewar ta ita ma sai ta yi bincike mai tsawo akan wacce zata samo masa ,Dan qaunar da ke yiwa Barr Kabir yasa bata son duk wani abun da ze zo ya kawo wa rayuwar shi cikas. Ta na kuma son shi da qaruwa kamar yadda take son Daddy da abun da ta Haifa da abun alkhairi. Wannan kuma na cikin karamci irin na hajiya ,duk Wanda ze zauna tare da ita to fa lallai ne yasan kirkin ta.

Bayan sun gama gaisawa ,nan suka shiga tattauna abun da ya faru ,da kuma yadda ya shirya case d'in ganin sun samo bakin zaren. Suna zaune Lubabatu tayo sallama kamar wata mutuniyar azziki hannun ta d'auke da tiren lemu. Har gaban hajiya taje ta aje mata ,ta juya zata fita Barr dake bin ta da ido ya dakatar da ita. Gaban lubabatu ne ya yanke ya fad'i ainun. Hannu Barr Kabir ya sa a aljihun gaban rigar shi ya d'auko wayar sa. D'an danne danne yayi a wayar ,wani folder ya shiga da ke d'auke da hotunan lubabatun. Sake duban ta yayi ya kuma mai da kan shi kan wayar ya duba dakyau ya ga lallai itace ba wa ta bace.

Ita dai lubabatu sai kallon shi take yi ta na so ta gane inda tasan wannan fuskar amma ta kasa tunowa.

Tashi Barr Kabir ya yi yazo har inda lubabatu ke tsaye ,ya dinga zagaye ta yana qare mata kallo Sama da qasa ,Wanda ya sa lubabatu tsarguwa. Kowa ya zuba wa sarautar Allah ido yaga me ke shirin faruwa.

Barr Kabir yace "kin yi kama da wata matar marigayi Alh sambo".

Dummm! Gaban lubabatu ya yanke ya fad'i ,tabbas tasan ko waye ya mata farin sani musamman da ya ambato mata sunan Alh sambo. Zufa ne ya shiga tsiyayo mata ,kan kace me jikin lubabatu ya fara karkarwa.

Murmushi Barr Kabir yayi kafin yaci gaba da cewa "ko da yake duniya ta fa d'i ba lallai ya zama ke ba ,ina ga dai kamar Ku ce ta yi yawa.

Girgiza kai lubabatu ta shiga yi cike da sarqewar murya tace " umm...ummm ba ni bace". Ta na gama fadin haka ta yi hanyar waje da gudu. Sai dai a rashin sa'a sai jin tayi taci karo da mutum.

'Yan sanda ne sai dai ba'a kayan aiki su ke ba. Saboda kar su ja hankalin mutane, wanda Barr Kabir ne ya tura mu su adireshin unguwan da layin. Cafke ta suka yi ta na ta kokarin ta k'wace ,tare da cewa "Ku sake ni in tafi ,ba ni na kashe shiba wallahi Ku sake ni"

Barr Kabir yace "da ma wa ya ce kin kashe shi ai yana nan da rai ba mutuwa yayi ba.

Hannu lubabatu ta Dora akai tare kurma ihu tana fadin " na shiga uku na lalace"

Barr yace "ba ki shiga ba za dai ki shiga" yana gama fadin haka yace su tafi da ita.

MUJE ZUWA💃🏻

TAKU HAR KULLUM

SIDIYA...✍️

[8/17, 3:30 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠

*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)

*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*

_BABI NA ARBA'IN DA D'AYA_

*_______________________________*

Ba su kai ga fita da ita ba Sai ga Haajar ta shigo ,wacce sun shigowar su ta fice bata San wainar da ake toya wa ba. Hannun ta rik'e da wani buhu duk ya yi datti ,ba kuma Wanda yasan me ke ciki sai ita data shigo da shi. Tace wa 'yan sandan "Ku dakata tukunna". K'arasawa ciki ta yi , sai da ta k'arasa tsakar parlourn in da kowa ze iya hango ta ,sannan ta zuqunna tare da zaro abun da ke cikin wannan buhun. Da sauri daddy ya mik'e tsaye yana bin abun da haajar ta Ciro a buhun.

" wannan ba akwatin takaddu na bane?" Daddy fad'a tare da nuna akwatin.

Haajar tace "ka sake dubawa dakyau dai ka gani. Ta fad'a tare da mik'a masa akwatin. Karb'a ya yi tare da zama a lokaci d'aya ya bud'e akwatin ya shiga duba takaddun da ke ciki...

Da ido daddy ya bi ta, cike da matsuwar son jin k'arin bayanin In da ta samo akwatin bayan a idon shi komai ya k'one na sashen shi.
Chapter 31 · 0% Book details