Sashe 8
Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Yana isa k'ofar gate d'in gidan ,ya kira shi a waya ,tare da sheda masa zuwan sa. Hankalin Hajj Jamil idan yayi dubu ya tashi ,musamman daya duba ogogon bango ,yaga kusan sha biyu saura na dare ,shi kanshi har ya rufe gida ,wani d'an aiki ne ya hana shi bacci ,shi kanshi da tuni ya dad'e dakai Lagos. Yanayin muryan Daddy ya k'ara tabbatar masa da akwai matsala ,Dan haka be wani b'ata lokaci ba ,jallabiya kawai ya zura wa jikin shi tare da d'aukan makullan gida ,ya fito._
_Seda yad'anyi tafiya kamar na rabin kilo meter kafin ya kawo bakin gate d'in. Addu'a yayi tare da bud'e K'aramar k'ofa . Fitillun mota daddy ya hasko masa ,alamar ya bud'e masa gate ,maida k'ofar yayi ya rufe sannan ya saka makullin babban kwad'on gate d'in. Yana aniyar bud'e wa ne ,me gadin shi yayi firgigit ya fito hannun shi d'auke da gora da adda, hasken toci ya dannawa hajj Jamil a ido ,kan kace me har ya mamaye shi yana aniyar rafka masa gora a tsakaiyar baya. Seda Hajj Jamil ya daka masa wata uwar tsawa ,sannan ya shiga taitayin shi._
"Dan Allah kayi hak'uri Alhaji ,wallahi ban gane kai bane ,saboda nasan abune me wuya ka fito tsakar dare haka ,muddin ba tafiya kayi ba". Cewar Tukur me gadi.
Wani siririn ajiyar zuciya Hajj Jamil ya sauke kafin yace " Ba komai ,nasan ai baka gane waye ba, nima dole ce ta fito dani"...
Cike da nuna damuwa Tukur me gadi yace "to amma Alhaji lafiya kuwa ka fito cikin Daren nan ,kuma baka tashe ni ba?"
"Kar ka damu lafiya qlau Tukur ,Bak'i nayi ne ,kuma tafiyar dare sukayi shine suka mun waya sun iso" Hajj Jamil ya bashi amsa.
Daga nan ya maida hankalin shi wajen bud'e gate d'in. Shidai Tukur hankalin shi be kyauta ba seda yaga shigowar su daddy ,Hajj Jamil ya maida gate d'in ya rufe tare da yin Addu'a sannan ya koma d'aki.
Fuska a sake Hajj Jamil ya tari Daddy ,se anan take gaya masa tare dasu Haseena yake. Marfin motan gaba Hajj Jamil ya bud'e ,a lokaci d'aya kuma suxee ta bud'e marfin baya ta fito. Nan take Hajj Jamil ya d'aga waya ya kira Hajar ,Dan yasan ita kad'ai ce bata isa bacci ba a wannan lokacin kasancewar ta ma'abociya karatun alqur'ani da sallar dare ,bata runtsawa se ta tabbatar tayi raka'atanul fajr ,ta kuma jira an tada sallan asuba tayi ,sannan bata tashi a inda take har se ta tabbatar rana ta hudo sannan take samun yin bacci ,shima ba wani isash-she ba ,saboda aikace-aikacen gida...
Bugu d'aya biyu ,ta d'auki wayan tare da yin sallama ,cikin siririyar muryatta be matuqar dad'in sauraro. Amsa sallamar yayi tare da cewa "Haajar ki zo ki shiga da bak'i a haraba!"
"Tohm gani nan zuwa insha Allah!" Ta fad'a tare da mik'e wa ,dama akwai Baban hijabi a jikin ta har k'asa. Tafe take tana d'an rare karatun alqur'qni k'asa-k'asa ,a haka har ta k'araso inda suke a tsaye.
D'an gurfa nawa tayi ta gaida Daddy a nitse ,kafin ta mik'a wa suxee hannu tare da yi mata sallama suka gaisa ,haka da haseena ma. Duk da irin tashin hankalin da daddy ke ciki ,be hana yaji Haajar ta burge shi ba.
"Ki shiga dasu ciki!" Cewar Hajj Jamil.
Daddy ne ya bud'e mota ,ya d'auko Auta ,da sauri hajar ta k'araso ta karb'e ta a hannun shi. Sannan ta maida duban ta gun su suxee tace
"Sisters muje ko?"
Jiki a sab'ule suka rufa mata baya ,har suka k'arasa ciki.
Seda suka tafi sannan hajj Jamil ya maida duban shi wajen Daddy tare da cewa
"Daddy mu k'arasa ciki muma ko?"
A tare suka shiga sashen Hajj Jamil ,kasancewar me d'akin shi Hajiya zaliha tayi tafiya. Hajj Jamil beyi k'ok'arin tambayar Daddy meke faruwa ba ,seda ya kawo masa lemu me sanyi yasha ya sarara ,sannan yake tambayar sa
"Daddy wai meya ke faruwa ne haka ,ka kwaso 'ya'ya cikin Daren nan ,kuma daga gani ma yaran suma ba'a hayyacin su suke ba?"
Wani guntun ajiyan zuciya daddy ya sauke sannan ya fara zayyanawa Hajj Jamil duk abunda yake faruwa ,daga auren khaltum ,zuwa had'e masa kai da suka yi ,har kawo abunda ya faru a Daren yau d'in...
Cikin tsananin tashin hankali ,da rud'ani hajj Jamil ya dafe kai tare da furta
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Hasbunallahu wani'imal wakil"...
A Daren ranar kusan daga Daddy har Hajj Jamil basu iya runtsawa ba ,jamamin lamarin suka kwana suna yi...
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[7/19, 3:43 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠
*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*
_BABI NA GOMA SHA BIYU_
*_________________________*
_Sai wuraren asuba su daddy suka samu damar runtsawa ,ko kiran sallan da akayi daga shi har Hajj Jamil ba Wanda yaji. A b'angaren Haajar kuwa ,har ta tashi su suxee ,ganin ana k'ok'arin tada sallah su Daddy basu fito ba yasa ta kira Hajj Jamil a waya. Har wayan ya gama ringin be d'aga ba, mamaki ne ya kamata ,cikin ranta take cewa "yau kuma wani irin nauyin bacci Abbu samir yayi" (haka take kiran shi ,Wanda suna ne na alkunyar d'an shi na farko). Sake kiran wayar tayi a karo na biyu ,nan ma ba'a d'aga ba, ganin lokaci na k'urewa yasa ta fito zuwa sashen shi. Batayi tunanin ganin kowa a parloun ba ,Dan haka kawai ta murd'a handle d'in ta shiga bakin ta d'auke da sallama, se ta kunne bulb d'in parlourn (wato haske), A mamakin ta se ganin su tayi kwakw-kwance akan kushin da alama hira suke bacci ya kwashe su ,kuma daka ga yanayin baccin kai kasan basu San suna yi ba, baran ma daddy da k'afar shi d'aya ke kan kushin d'in, d'aya kuma a k'asa, shi kuwa Hajj Jamil ga system nan a gaban shi se aiki take ita kad'ai ,kan shi jingine da kujera._
_Tunanin yadda zata fara tashin su tayi ,Dan haka kawai se ta yanke shawaran bubbuga k'ofa, shiru ba Wanda ya motsa. Jin kamar za'a tada sallah ,gashi bata so suyi asarar jam'i yasa ta k'araso da sauri ta shiga tashin su. Hajj Jamil ta fara tadawa ,sannan ta bubbugi k'afar Daddy
"Abbu samir Ku tashi lokacin sallah ya fara k'urewa" ta fad'a cikin siririyar muryar ta. Ba shiri daddy ya mik'e ,kafin Hajj Jamil shima ya wats-tsake ,wani dogon mik'a yayi tare da salati ,ganin sun tashi yasa tabar sashen zuwa nasu sashen. A gaggauce su Daddy sukayi alwalla ,suka fita zuwa masallaci, koda suka fita tukur na jiran fitowar su , a tare suka k'arasa masallacin.
_Haajar koda ta koma taradda su suxee tayi har sun fara sallah, ita ma gabatar da nata sallan tayi ,seda ta kammala ta Shafa Addu'a, sannan ta dubi suxee data lura kamar itace babban, murmushi ta sakar mata tare da cewa
"Kun tashi lafiya sisters?"
Suxee Murmushin itama ta maida mata ,tare da amsa gaisuwar
"Lafiya qlau sister. Ya gajiya?"
"Gajiya ai se Ku masu tafiya" Haajar ta fad'a fuska a sake. Haseena ma gaishe su tayi kafin ta koma ta kwanta.
Haajar maida duban ta tayi gun suxee tace
"Sedai sister bansan sunayen Ku ba?"
Murmushi suxee tayi tare da cewa "Sunana Suwaiba ,amma ana kira na da suxee ,Baba na kuma na kira na Hajiya k'arama ,saboda sunan mahaifiyar shi ce". Nuna Haseena tayi data yi d'aid'ai tana kwasan baccin ta tace " wannan kuma Haseena ita take bi mun, se Auta Shukra"
Jin jina kai Haajar tayi tare da cewa "Sunaye masu dad'i da ma'ana. Naji dad'in had'uwa daku"
"Muma haka!" Suxee ta fad'a cike dajin dad'in kasantuwa da Haajar.
Misalin k'arfe takwas ,Haajar ta fito ta nufi kitchen, koda ta fito babah ta-tata me aiki har ta gyara ko ina, amma bata taradda ita a kitchen d'in ba. Tunani ta fara akan me zata dafa ,Wanda tasan bak'in su zasu so shi. Tuno wa data yi Hajj Jamil yafi son yin breakfast da kunun gyad'a me madara yasa tayi tunanin ma Daddy ze so shi, nan ta shiga shirya musu kunun gyad'a me d'an karan daddy da d'aukan ido, a lokaci d'aya kuma ta soya Arish tare da yi masa mahad'i na sauce din k'wai da soyayyen anta. Seda ta kammala ta zuzzuba a mazubi me kyau, tana k'ok'arin fitowa se ga suxee ta fito ,k'amshi tabi har ya kawo ta kitchen d'in. Haajar na ganin ta suka sakarwa juna murmushi.
Ciki suxee ta k'araso tana fad'in " kai Sister Haajar ,shine baki tashe ni munyi tare ba?"
Haajar dake ta kai kawo tana k'ok'arin tsaftace wajen tace "Haba dai Hajiya k'arama! Idan nayi haka ,ai da ban kyauta ba. Kufa bak'i na ne ,ko kin manta hadisi na manzo s.a.w dayace , " Imanin d'ayan mu baya cika ,har se ya kyautatawa bak'on sa?" To kinga kar nayi missing wannan aikin ladan. Kuma ma kuda kuka zo jiya-jiya ,ina wani kika isa fara tayani aiki? Aikya bari ki huta tukunna"
Dariya kawai suxee tayi, a ranta take jinjina karamci irin na Haajar. A tare suka kwashe komai ,suka kai babban parloun gidan inda aka saba karyawa, sannan suka dawo suka k'arasa gyara kitchen.
Haajar ce ta dubi suxee tare da cewa
"Sannu da k'ok'ari"
"Kaji sister Haajar, wai sannu ,se kace wani aikin kirki kika bari nayi ,aike za'ayi wa sannu."
Murmushi Haajar tayi sannan tace " Yanzu dai muje muyi wanka kafin su Abbu Sameer su fito.
A tare suka Jere ,kai idan ka gansu zaka d'auka sun jima tare ne.
Seda suka gama shiri tsaf suka jero zasu fito ,Suxee ta ke k'are wa Haajar kallo, badai wani kwalliya tayi ba ,Dan tana gani ma ko powder bata Shafa ba, iya mai kawai ta Shafa se man baki. Doguwar Riga ne yellow a jikin ,Wanda ya tafi da shape d'in ta. Fuskar ta dauke d'auke take da manyan idanuwa zagaye da zara-zaran gashin ido ,tana da karan hanci ,ga bakin ta daidai ita.