← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 52

Sashe 43

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SINADARAN TABBATUWAR NI'IMA DA ZAMA CIKAKKIYAR MOWAR GIDA.
wannan wata irin tsaraba ce ta musamman gare ki uwar gida
.
sassaken baure.
ruwan rake.
'ya'yan zogale.
ruwan zuma.
ruwan dabino.
Ki daka sassaken baure ko ki barshi a sassaken sa, ki zuba ruwa cikin kofi daya, mai girman ( jug ) idan gari ne sai ki sa cokali biyar idan sassaken ne sai ki kin tabbata kamar yadda idan kin daka zai ba ki cokali biyar din, ki Dora a wuta ya tafasa kamar awa guda, sannan ki sauke idan ya kwanta sai ki tace, sai ki zuba markadadden ruwan kankana kofi daya, ruwan rake ma kofi daya ruwan dabino ma kofi daya, zuma Rabin kofi garin ganyen zogale cokali biyu, sai ki Dora a kan wuta Yayi ta dahuwa sai ya dahu sosai , zai yi kauri amma ba kitif ba, idan ya huce sai ki dinga shan Rabin kofi safe da yamma Wanna yan dadewa a jiki, Zaki ban labari.

DAUKEWAR NI'IMA BAYAN HAIHUWA

sassaken kankana
sassaken baure
ya'yan zogale
idon zakara
asuwaki mata
ganyen kafi suga.
Ki hada ki dake ki tankade yayi laushi sossai ki dinga zuba cikin cokali abinci daya cikin madarar shanu kofi daya ko cikin madarar ruwa gwangwani daya kina sha safe da yamma.
:
JAN HANKALI GA MATA MASU BUSHEWAR FARJI

Sirin bushewar farji
yar'uwa ga dama ta samu, idan kina fama da bushewar farji, a koda yaushe to sai ki sami man zaitun da man habbatussauda, sai ki hada su waje daya, ki dinga shafawa a cikin farjinki insha Allah Zaki ga biyan bukata, domin kowace cuta tana da magani, sai dai in baki nema ba, amma in kika nema Zaki samu. Allah ta'ala yasa mudace.

QARIN NI'IMA

Ya'yan kankana
Danyar gyada
Dabino
Alkama
Garin kumasoriyya
'Ya'yan zogale
Ki dakesu suyi laushi ki rinka shan karamin cokali da madara ta ruwa safe da yamma, kuma shima mijin zai iya sha.

QARIN NI'IMA
Ki nemi ridi, ki daka ki tankade ki nemi madara ta ruwa ki hada ki gauraya kisha sai an gwada akan san na kwarai.

QARIN NI'IMA
Dabino
Dankalin hausa
Kwakwa
Mazarkwaila
Madara peak milk 1
Kanunfari
Kicire kwallon dabino saiki jika ki fere dankali kiyanka kanana ,kixuba kijika maxarkwaila tajiku kixuba kiyanka kwakwa kanana kixuba saikiyi blending dinshi duka saiki tace kisaka a fridge yayi sanyi ki wuni kina sha.

HADIN TANTABARA('YAN SHILA)
Bayani akan hadin tantabara ba sobon abubane kusan kowacce mace tasan amfaninsa domin akwai tabbacin yana hada dankon soyayya tsakanin miji da mata bayan ni ima da dandano yana saka gaban mace ya ciko wannan an dade ana amfani dashi kuma yana aiki idan kinason koya to ga yanda zakiyi
Da farko dai ga abubuwanda ake bukata ki nema

1️.Za ki samu Tanbaru guda biyu amma yaya ba iyayeba (Mace da Namiji)
2️.Habbatus-Sauda (Cokali biyu)
3️.Garin Raihan (Cokali hudu
4️.Ridi (Cokali uku)
5️.'Ya’yan Zogale (shima cokali uku)
Duk wadannan anaso kidakasu su zama gari saiki ajiye bayan kin fara dafa wannan tantabarun sama sama saiki tace ruwan sannan ki zuba wannan garin saiki saka duk wani kayan hadi da kikeso sannan ki zuba ruwa kadan ki mayar kan wuta ki barshi ya dahu sosai sannan ki sauke. kuma dukkansu akeso ki cinye ke kadai ki jarraba wannan ko amarya ko uwargida.

HADIN KAZA NA AMARYA DA UWARGIDA
Hadin Kazar Amare
Yanzu za mu yi bayanin sirrin dafa kazar Amare wanda idan har mace tayi kafin Aurenta da kamar sati 1 zataga amfaninsa. Irin wannan ne idan baki San sirrin ba zakije ki saya da tsada.
Koda yake wasu qiwuya ke hanasu had'awa da Kansu. To ga sirrin

Yadda ake : Anaso kisamu bushashen ganyen magarya da kanunfari da idon zakara duk ki hadasu waje daya ki dakasu ki tankade su zama gari to idan kika samu:
Budurwar kaza, kika gyarata saiki zuba wannan garin acikin tukunyar sannan zaki iya zuba kayan miya yanda kikeso. Bayan ta dafu saiki cinye gaba daya. Yana saka Farjin mace ya kumbura ya ciko da Ni'ima, kuma yana karawa mace dàn dàno...

MAGANIN K'AIK'AYIN FARJI KO KURAJE KO WARIN GABA
Yawanci Ciwon Sanyi Na mata ne ya fi haddasa irin wadannan matsalolin.

1. Ganyen lalle Wanda bai zama gari ba
2. Yayan Hulbah
3. Tafarnuwa Guda 3 a 6are busashshen 6awonta
4. Kaninfari (Qudnuful)/clove chokali uku
5. Ganyen magarya ko garinsa
6. Ruwan khal tuffah ko white khal ko malt khal, Amma an fi son khal tuffah (Apple Veneger)/cedar
Za a hadasu wuri Daya a dafa Su Su tafasa sai a sauke a juye a baho, in ya Dan huce yadda bazai cutar ba sai a Dan zuba ruwan khal din daidai gwargwado sai a shiga Ciki a zauna tsawon mintuna goma ko 15 sai a fito, kuma YAKAMATA a ce kin aske Gashin gabanki ta yadda ruwan zafin Zai sami damar penetrating in to ur Virgina's hole. Sannan ki bubbude cinyoyi Sbd ruwan ya shige ya ratsa, in kika fito sai ki zubar da ruwan da yamma ma sai ki kara Hada Wani ki dafa ki kara aikata haka, inshaaAllahu indai kaikayin Gaba ne ko zazzagiwar farji inshaaAllahu Zaki dace, sannan me fama da Warin Gaba ma Zata Iya amfani da wannan Hadin, haka me jin Zafi lokacin jima'i.

MATSALAR BUSHEWAR GABA NA MATA DA KUMA KARANCIN NI'IMA (VAGINAL DRYNESS AND LOW SEXUAL PLEASURE) DA KUMA HANYAR MAGANCE MATSALAR A SAUKAKE

Idan muka ce ni'ima to muna magana ne akan sha'awa waton (libido) a Turance kenan. Tana taruwa ne ga matan da suka balaga, masu koshin lafiya, walau budarwa ce ko kuma matar aure.
Sha'awa halittace wacce ta banbanta daga wata mace zuwa wata macen. A lokacin da mace take jin sha'awa haka kawai ko sanda take karanta wani labari ko tinanin wani abu dake motsa sha'awa ko a yayin da ake gabatar da wasanni (fore play) kafin saduwa to idan dai har tana da ni'ima to zata ji duk ta jike dan wasu fararen ruwane masu yauqi zasu rinka fito mata. A lokacin ta riga ta kamu kenan wannan ne ake kira Natural lubrication ko Vaginal wet wanda idan har za a sadu da ita a lokacin to a shirye take. A hakika shima mai gidan zai yi matukar gamsuwa da ita. Bazata ji zafi ko ciwo ba saboda ta jika sosai ta yanda bata bukatar ayi amfani da wani vaseline ko ointment. To wadannan ruwan masu yauqi dake fitowa mace a sanda sha'awarta ta motsa to ita ke nuna alamun tana da ni'ima. Wasu matan sun fi wasu yawan sha'awa da samun ni'imar jiki dan yanayin halitta da lafiya, da ma abincin da suke ci ya sha banban. Wasu matan tun fil azal suna da ni'ima mai tarin gaske. Amma daga baya takan gushe sai su rasa sanin dalili. Hakan zai sa su tsunduma suyi ta neman kayan mata suna cusawa kansu abubuwa masu cutarwa duk da sunan ni'imarsu ta dawo. matsaloli da dama kan faru a sanadin haka.
Akoi matsaloli da rashin lafiyoyi da dama dake haifar da gushewar ni'ima ga mata, wadanda suke bukatar bincike a maimakon haka mata da dama sukan yanke hukuncin cewa ai ciwon sanyi ne ke gare su alhali wata matsala ce ta daban. Akwai matan da basu da ni'ima a koyaushe gabansu a bushe yake ba wata ni'ima ko jin sha'awa. wasu matan sai sun shafa vaseline kamin a iya saduwa dasu. Hakan kan haifar da rashin samun gamsuwa musamman ga maigidan. Cushe cushen da mata ke yi da sunan matsi yana daya daga cikin abinda ke zuqe ni'imar mace ya haifar mata da bushewar gaba Musamman in abinda suke cusawar bai dace da Farjinsu ba, misali amfani da ruwan bagaruwa wacce tana matse fata amma kuma tana zuqe damshin dake ga wurin gaban mace, zai matse amma kuma zai kasance a bushe.To miye fa'idar yin haka kenan ?
Maigida na saduwa dake amma yana jin kamar ana zoza mashi katako.
wasu cushe cushen na haifar da cutukan gaba da kuraje da kaikayin gaba da irin wani wari wanda ke kanki sai ki rasa wanne irin wari ne? Dan an dauki wani abun na daban an tura a inda bai dace ba. Akwai magani Natural fruits da mata zasu iya rinka amfani dasu dan su karawa kansu shawa da ni'ima kai hattama da koshin lafiya.
Kamarsu kankana ,ayaba, gwanda abarba, lemu ,timatir ,rake, dabino, kwakwa, dafaffiyar gyada, zuma ,nono, zogale, ridi, ruman cukwi(Nonon Rakumi), inabi, tuffa, zaitun, tafarnuwa, albasa, da dai Sauransu

Wallahi wadannan duka sun fi duk wani cushe cushe ko kayan sha na mata da kuke gani amfani da kuma saukin saye.

Zaki iya cin ayaba da dabino a yau.
Gobe sai ki canza ki nemi kankana ki sha, jibi ki nemi dafaffiyar gyada ki ci, gata ki nemi zogale da albasa da quli quli kiyi datu/Kwadanta ki ci. sai kiga kina ta canzawa lokaci zuwa lokaci.
Wallahi ina baki tabbaci idan kinka rike haka to ba wai ni'ima ba ko lafiya da fatar jikinki zaki ga tana canzawa.
Amma an rungumi kayan maiqo da kayan zaqi da kayan yaji kawai ake ci dare da rana ana ta faman shan kayan mata da cushe cushe amma a banza dan ba sune abinda jiki keda bukata dasu ba ai dole shawa ta ja baya.
Haka kuma zaki iya hada wadannan dan karin ni'ima da gamsarda mai gidanki. Amma akwai bukatar a kiyaye da tsabta. mata a daina cusa duk wani magani a cikin gaba wanda Bai dace da farji ba, farjin mace kaman ido yake baya son bako. A dinga tsarki da ruwan dumi amma banda sanya sabulu.
A daina sanya pant da bai bushe ba. Idan an wanke to a rinka shanyawa har sai ya bushe.
A ringa yi ana canza shi akai akai.
Banda yin musanya da fatar za a kula.

Ga wannan hadin sai a jarraba
za a iya daukar daya ko biyu daga ciki ayi amfani dasu.

1-Qwai (Egg) da albasa da timatir, sai a soya amma kada a bari suyar ta kone. Banda sanya maggi da gishiri da yawa.zaki iya sakawa amma dan kadan ake so.
Namiji zai iya ci hakan zai kara mashi da yawan ruwan maniyi.
Chapter 43 · 0% Book details