Sashe 26
Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Haajar tayi tare da cewa "Auta muje in yi miki wanka kinji. K'yale su zan ga me tab'a ki a gaban ido ne ,se dai ayi idan ba na kusa"...
Tsalle Auta ta shiga yi tana fad'in" yeeeh Anty Haajar! " ta fad'a tare da yi wa su haseena gwalo.
Wani guntun tsaki haseena taja tace "Ji ta fa Dan Allah! Kwatakwata Auta bata San ta fara girma ba. Zallar wauta ne da yarinta ke damun ta. Bansan yaushe za ta yi hankali ba wallahi"
Dariya Suxee dake gyara musu kaya tayi tana fad'in "Ai Auta Autar ce. Allah dai ya raya ta musha biki"
Haka suka ci gaba da tab'a hirar su cikin nuna qauna irin na 'yan uwan taka...
Sallama kubra tayi kamar wata mutuniyar azziki ta shigo d'akin su Suxee, lokacin Haajar na band'aki tana wa Auta wanka. Tun da suka amsa mata sallama ko wacce ta d'auke kan ta. Duban su Kubra tayi tare da cewa "Ba Ku gan ni bane?"
"Mun gan ki" Suxee ta bata amsa a tak'aice
Mamaki ne ya kama Kubra, Dan idan akwai Wanda ya kamata ya yi mata hakan be wuce Haseena ba Dan ita ce me fitsarar cikin su ,amma kuma yau se ga Suxee.
Duk da halin ko in kulan da suke nuna mata ya mata ciwo ,amma se ta share tare da zama a gefen gado kusa da inda haseena ke zaune ,shafo gefen fuskar ta tayi tare da cewa "me yake damun kine haseena naga duk kin rame ?" Kayan dake kusa da haseena Suxee tazo ta kwashe ,nan magungunan Haseenan suka fad'o k'asa. Haseena tace "Yaya Suxee magani ne" ta fad'a tare da nuna mata.
Kafin suxee ta d'auka Kubra ta kai hannu ta d'auko tana dudduba magungunan. Kallon haseena ta sake yi tare da dafa kafad'ar ta tace "Haseena ba ki da lafiya ne? Me yake damun ki haka?"
Kwab'e hannun ta haseena tayi daga kafad'ar ta rai a b'ace tace "Menene damuwar ki dani da har zaki damu da lafiya ta?"
Kubra ji tayi ba dad'i a ranta ,amma ta danne tare da sake da fa kafad'ar haseena a karo na biyu tace "Wani irin magana kike yi haka Haseena? Na damu daku mana ,ni fa mahaifiyar Ku ce!"
Wani irin murmushin takaici haseena tayi tare da cewa "Na riga na manta da wannan tuntuni ,ni ba ni da wata uwa. Amma nagode da kika tunanin da hakan ,amma inaso ki sauke hannun ki daga kafad'a ta tun kafin in manta da cewa ke ce kika haife ni. Ina kuma baki shawaran ki manta da cewa kin tab'a zama uwa ko kina da wasu 'ya'ya kamar yadda mu ma tuni muka manta da cewa muna da uwa irin ki a duniya..."
Ba kad'an ba maganganun Haseena ya tab'a Kubra matuqa. A karo na farko da ta fara jin cewa bata kyauta wa rayuwar 'ya'yan ta ba ,amma son zuciyar ta ya hana ta ganin lefin abunda ta ke aikata wa. A sanyaye kubra ta tashi ta zata fita. Haseena tace
"Du be ta Dan Allah! Tana yi kamar ba ta da hannu a duk abubuwan da suke faruwa da mu. Wacece silar tarwatsewar rayuwar mu Dana mahaifin mu idan ba ita ba!" Haseena ta fad'a cikin b'acin rai. Nan take hawaye suka fara sauko mata.
Da sauri Suxee ta ajiye kayan da ta ke gyarawa ta matso ta dafa ta tana share mata hawaye tare da cewa "Relax Haseena! Kinsan ba wata isash-shiyar lafiya kike dashi ba. Yau fa aka sallamo ki daga asibiti. Be kamata ace har kin fara ta da hankalin ki haka ba. Babban burin mu a yanzu be wuce muga kin samu lafiya ba"...
" Bazan tab'a samun lafiya ba matuqar ina ganin waccar matar!!! Matuqar tana ci gaba da kiran kan ta mahaifiya ta!!! Yaya suxee waccan matar da kike gani ba kowa bace silar faruwar abunda ya faru dani fa ce ita ,itace ummul abasin faruwar komai. Na tsane ta bana son ganin ta, wallahi idan aka yi wasa ni ce ajalin ta ,idan kuwa hakan bata faru ba ,to ita zata zama sanadiyyar nawa ajalin. Yaya suxee na tsane ta ,kice ta fita daga nan bana son ganin ta" Haseena ta k'arasa maganan tare da fashewa da wani marayan kuka ,a lokaci d'aya ta fad'a jikin Suxee tana ci gaba da rera kukan ta me ban tausayi. Suxee ita ma nan da nan hawaye suka fara sauko mata na tausayin kan su...
Rai a matuqar b'ace Kubra ta juyo tare da cewa "Kin fita a hankalin ki ne? Me..."
"Ya isa haka Dan Allah." Suxee ta katse Kubra ,sannan taci gaba da cewa " Ya isa! Wasan kwaikwayon ya isa haka. Dan Allah ki tafi. Kin zo ganin mu ko ? To mun gode da ziyara Allah ya ba da lada. Ki tafi pls ki bar mu da abunda muke ji ,tun kafin ki janyo mana wata masifar bayan wacce muka shiga"... Suxee ta fad'a hawaye na sauko mata.
Zuciyar Kubra ta shiga k'una ,iya b'acin rai ran ta ya b'aci. A fusace ta fita hawaye na sauko wa daga idanuwan ta. Da gudu ta haura sama ,ba ta ko lura da Khaltum dake lab'e a wurin ba ,da alama taji duk abun da ya wakana tsakanin Kubra da 'ya'yan ta...
Wani irin dariya Khaltum ta yi na makirci. Tare da d'aukar alwashin gano bakin zaren...
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[8/11, 9:14 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠
*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*
_BABI NA TALATIN DA SHIDA_
*_____________________________*
_Kubra kai tsaye d'akin ta nufa ,tana zuwa ta fa d'a kan gano tare da fashewa da wani sabon kuka me tattare da takaici da bak'in ciki. A rayuwa bata tab'a tunanin rana me kama da wannan za ta zo mata ba. Ace yau 'ya'yan ta na cikin ta ne suke furta mata Kalmar tsana da k'iyayya har suna furta k'ila su ne ajalin ta. Wannan Abu ba k'aramin tab'a kubra ya yi ba. Dan yinin ranar ko ina ba ta iya zuwa ba ,a d'aki ta wuni..._
Ganin haka yasa Khaltum ta zo sashen ,a kan gado ta samu kubra tayi rufda ciki ,da alama wani gajeren bacci ne ma ya kwashe ta ba tare da ta sani ba. D'an bubbuga gadon Khaltum tayi. Firgigit Kubra ta farka.
Daga gefen gado Khaltum ta samu ta zauna tare da tambayar Kubra abun da ke damun ta
"Ya na gan ki haka ne hajj Kubra? Ba ki da lafiya ne? Tun d'azu ina ta jiran ki har na gaji da jira na koma ciki. Yanzu ma gani nayi shirun yayi yawa nace bari in leqo inji ko lafiya. A karo na farko da kika fa sa zuwa chasu ,nasan ko menene lallai babban dalili"... Khaltum ta fad'a kamar ba ta ji komai ba.
Wani nannauyan ajiyan zuciya Kubra ta sauke tare da cewa " Khaltum ina so in gyara tsakani na da 'ya'ya na!!! Ina so in ba su kula wa na tsakanin uwa da 'ya'ya... Khaltum ina son yara na ,bazan iya jure ganin su cikin wani hali ba... Ba zan tab'a yafe wa kaina ba idan wani abun ya same su ta sanadiyya ta ,balle ace wani na da hannu a cikin b'ata musu..."
Wani kallon mamaki Khaltum ta bi Kubra da shi kafin tace "Me hakan ke nufi kenan? Ya na nufin zamu da ne shaqatawa da shar holiya? Kin San hakan ba k'aramin asara bane gare mu. Ki manta da wannan ,mu mori rayuwar mu. Naga cewar yaran lafiyar su qalau, kuma mahaifin su na kula da su ,me yasa zaki damu kan ki?"...
" Khaltum ba zaki tab'a gane abun da nake nufi ba ,ba zaki tab'a gane irin soyayyar dake tsakanin uwa da 'ya'ya bane. Da zaki shiga zuciya ta kiji irin zugin da nake ji a yanzu da baki fad'i cewa in manta da su ba. Ko da yake ta ina ma zaki San me nake ji bayan ba uwa bace ke??? Ta ina zaki san abunda nake ji a yanzu bayan baki san darajar 'ya'ya ba. Da ace kin tab'a d'aukan ciki ko da so d'aya ne ,ko baki haife cikin ba ki kayi b'ari ina ga zaki fi gane d'acin dake rai na a yanzu. Ban ma ga amfanin zama ina gaya miki wannan ba Dan be shafe ki ba ,kuma ba ki da maganin da zaki mun. Uwa ya kamata in fad'a wa wacce tasan darajar 'ya'ya ,wacce ta tab'a d'aukan ciki ta haihuwa amma ba ke ba"...
[8/11, 8:29 PM] SIDIYA...✍️: Ba kad'an ba kalaman Kubra ya yi matuqar k'onawa Khaltum rai. Dan ta fahimci akwai suka da habaici a cikin maganganun Kubra. Wato me Kubra ke so tace mata? Tana nufin ita juya ce ko kuwa? Tana nufin ita bata San zafin haihuwa ba shiyasa bata San darajar 'ya'ya ba? Lallai ya kamata ki farka daga dogon baccin da kika yi Khaltum' Khaltum ke ta faman sak'e-sak'e a ran ta. Tab'e baki ta yi tare da cewa
"Wannan haka ne kam. Amma ga wannan ina ga idan kika sha ze rage miki rad'ad'in abunda kike ji a yanzu, nasan zaki ji dad'in shi"... Khaltum ta k'arasa fad'a tare da mik'e wa Kubra wani syrup.
Ba musu kubra ta karb'a kwalban maganin nan ta d'aga ta shanye se dai ta aje kwalba ta shanye tas... Nan kubra ta fara sambatu iri iri akan tana so ta kasance da 'ya'yan ta. Wannan ya k'ara tabbatar wa da Khaltum cewa lallai kubra ta fara damuwa akan yaran ta ,ta San kuma komai ze iya faruwa daga wannan lokacin. Tashi tayi ta koma sashen ta. Ranar bata iya yin bacci ba ,kwana tayi tunanin yadda zata b'ullowa al-amarin, kafin safe ta yanke wa kan ta hukunci....