← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 52

Sashe 30

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kwanan daddy uku a asibiti be San Inda kan shi yake ba. Hajj jamil ne ya kira hajiyar daddy ya sanar mata. Ba shiri hajiya ta taho sakkwato hijab a baibai...

Hajj jamil ne ke kula da daddy yayin da Hajiyar daddy ke kula da sauran majiyatan ,da basu qone ba ,sai dai jikata da suka yi had'ida qananan raunuka...

A rana ta hud'u daddy ya farfad'o. Kuka sosai ya ke na rashin 'ya'yan shi. Dan shi duk a tunanin shi gaba ki d'aya ba'a fidda kowa ba. Dan idon shi ya riga ya rufe ,ba ze iya tantance lokacin da aka fito da wasu ba balle har ya iya Sanin ko su waye daga cikin su...

Hak'uri Hajj jamil ya shiga ba shi tare da yi masa nasihohi akan qaddara, ya d'ora da cewa "wannan itace taka qaddarar MISBAHU,,, ba kuma dan Allah baya son ka bane yayi maka haka. Kar kayi mamakin wani tanadi ya maka Wanda yafi Wanda ya karb'a daga wajen ka"...haka hajj jamil ya dinga rarrashin daddy.

Daddy na kuka yace " ka banni inyi kuka jamilu. Na rasa komai da kowa nawa. Ba ni da kowa ba nida kowa. Wannan wani irin musiba ce??? Wani kalar baqar qaddara ce ke bibiyata haka??? Me na aikata Dana cancani irin wannan tashin hankalin??? Gidana ya dawo tamkar kushewa"

Hajj jamil na hawaye yace "Ka dena fad'ar haka MISBAHU. Baka rasa komai da kowa ba tunda ka na da Allah. Ya kuma San dakai. Shine kuma ze Isar maka ga dukkan al-amurran ka...MISBAHU kar ka manta Allah s.w.t Idan ka ga kayi dariya ni na saka ka ,idan kuma kaga kayi kuka to ni ne na saka ka shi ma...idan allah ya saka ka dariya ba wanda ya isa ya sa ka kuka ,idan kuma ya saka ka kuka to wallahi ba wanda ya isa ya saka ka dariya. Wannan shine karantarwa ta aqida... Allah dakan shi yace a cikin littafin shi mai girma "WA ANNAHU HUWA ADHAKA WA ABKA" Wato Allah shine me dariyantarwa, kuma shine me kukantarwa. Saboda haka ka yi tawakkali da Allah sai ya kaga ya Isar maka ga dukkan al-amurran ka..."

Wannan nasiha ba kad'an ba ya shigi Daddy. Hajiya da ke gefe ita ma ta karb'e shi ,sai abunda Allah be bata ikon fad'a wa daddy ba na Kalmar nasiha da rarrashi. Daga k'arshe tace "MISBAHU baka tab'a baqanta mun ba ,ban tab'a rik'e ka a raina koda na sakan d'aya ba. A koda yaushe Addu'a ta da albarka ta na tare da kai. Ba zaka tab'a ganin ba daidai ba ,insha Allahu lafiya zaka gama..." Wannan Kalma ba kad'an ba ya sake kwantar wa da Daddy hankali.

Satin daddy biyu aka sallame shi daga asibiti. Ranar da aka sallame shi ,Hajj Jamil yace yazo ya raka shi yana so ze dubo wani a cikin asibitin. Ba musu daddy yabi bayan shi.

Sallama suka yi tare da shiga d'akin majinyatan. Haajar ce akan gado daya ,daya gadon kuma dake gefe Suxee. Ga hajiya a zaune akan kujera tare da auta. Da mamaki daddy ke bin su da kallo ,murza yayi yana so ya tabbatar da abunda yake gani. Ganin kamar yana shakku yasa Hajj Jamil ya janyo hannun shi suka zauna daga gefe kan gadon da Suxee ke kwance.

Cike da al'ajabi daddy yace "Haajar,,, Hajiya k'arama da ma Baku mutu ba?""... Murmushi Haajar tayi tare da cewa " Allah ya raya mu Daddy ". Dariya maganar ta ya bama kowa. Suxee tace " Daddy ya jikin ka?" Tsabar farin ciki yasa daddy ya ma kasa amsa ta. Se bin su yake da ido kamar yau ya fara ganin su. Hannu ya d'aga sama tare da godewa Allah, ya kuma sake gasgata maganganun Hajj Jamil ,ga shi yanzu Allah ya dawo masa da wasu daga cikin ahalin shi a lokacin daya fi buqatar su...

Hajiya tace "ka gani dai ko? Dama mun Bari ka samu sauqi ne tukunna kazo ka gan su. Amma haqiqanin gaskiya da aka ce maka kowa na ka ya mutu ba gaskiya bane ,Allah ya fitar maka da wasu daga ciki. Ka ga shi Allah ba'a yanke rai da rahmar sa. A koda yaushe kuma Rahma da ni'imar sa kewaye take da bayin shi salihai"...

Jinjina kai daddy yayi cikin zuciyar shi ya sake godewa Allah. A fili ya furta " Lallai Allah ne abun godiya"...

Suna zaune likita ya zo ya kawo takaddar sallama nasu Haajar tare da magungunan su. Had'ida sheda musu cewa Haajar ta dawo sati na sama a sake duba ta. Hajj Jamil ya tambaya ko da wani matsalar ne? Likita ya mik'a mi shi sakamakon gwajin da aka yi wa Haajar. Karb'a Hajj Jamil yayi bayan ya karanta ya saka a aljihu...

Gaba d'aya suka d'unguma a mota zuwa gidan Hajj Jamil. Haajar na ganin an d'au hanyar da ba na gidan daddy ba ,tace wa Hajj Jamil dake toqa motar "Abbu sameer ina kuma za mu je?" Ba tare da ya juyo ba yace "Gida na zamu je mana". Girgiza kai tayi tare da cewa " A'ah Dan Allah! Ina so muje gidan daddy akwai abunda nake so in d'auka". Gaban daddy ne ya yanke ya fad'i lokacin daya ji Haajar ta ce aje gidan shi. Ba kad'an ba ya tsani yaji wani labari akan gidan balle har ace wani Abu ya sake kai shi gidan...

Hajj Jamil be k'i ta tata ba ya karya motar zuwa gidan daddy...

MUJE ZUWA💃

TAKU HAR KULLUM

SIDIYA...✍️
[8/17, 3:30 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠

*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)

*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*

_BABI NA ARBA'IN_

*____________________*

Har sun kai k'ofar gida barrister Kabir ya yi wa Hajj jamil waya akan yana babban asibiti ,Wanda shi ne mai bincike akan case d'in gobarar gidan daddy ,komai na tafiya ne a k'ark'ashin kulawar Hajj Jamil. Hajj jamil yace masa ya same shi a gidan daddy yanzu... Parking ya yi a k'ofar gida tare da kashe motar. Dikkan su suka fito suka shiga gidan a tare. Tunanin wani sashen za su suka fara yi. Hajj yace su nufi sashen bak'i Dan shi ne kad'ai a gyare, kuma anan zauna lokacin da al-amarin nan ya faru saboda zuwan jama'a ,wasu ya sauke su anan wasu kuma ya kai su masauqin bak'i. Gaba d'ayan su can suka nufa kai tsaye banda Haajar ,da ta zagaya ta bayan gidan da alama ma gidan gona ta nufa. Lubabatu na jin zuwan su ,nan da nan ta isa sashen Har ta na fad'uwa. Kuka ta rushe musu da shi tare da jajanta musu kan abunda ya faru. Wani irin kallo kowa ke bin ta da shi Wanda ya sa ta sha jinin jikin ta, da mamaki kowa ke jinjina rashin kunya da ta ido irin na lubabatu...

A ce duk abubuwan nan da suka faru ,duk sintirin nan da aka yi ta tayi na asibiti babu ita ba labarin ta ,ba zuwa ba aike. Ai ko itace hajiya suwaiba uwar Daddy zata rarrashi zuciyar ta tazo idan ma tace duk rad'ad'in abun ne bai gama sakin ta ba...

Haka kowa dai ya share ta idan ta kamo wancan batu ta saki ta kamo wannan duk na borin kunya. Babu Wanda yace mata ci kan ki. Gara ma hajiya har ta iya amsa gaisuwar ta. Mik'ewa tayi tare da cewa "bari in kawo muku ruwa". Tana gama fad'ar haka ta mik'e tabar parlourn. Auta ce tace " Ni hajiya bacci nake ji" hajiya tace "to muje ciki, daga nan ma na yi alwala Dan na ji kamar an fara kiran sallah". Hajj jamil yace " mu ma bari muje mu yi sallan hajiya ,mu na dawo wa yanzu" hajiya tace "to Ku dawo lafiya jameelu" daga nan daddy suka fita zuwa masallacin da ke cikin gidan shi ,a cewar Hajj jamil idan suka fita masallacin waje mutane za su yi ta zuwa mu su jaje ,kuma yanzu ya fi buqatar daddy ya samu Hutu kamar yadda likita ya jaddada masa...

Fitowar su ya yi daidai da isowar Barrister Kabir. A tare suka shiba masallaci bayan sun fito sun jima suna tattaunawa kafin suka k'araso Dan Barr Kabir ya yiwa hajiya jajen abunda ya faru...

Hajiya na d'aki kan sallaye ,suxee ta shigo tace mata "Hajiya kizo anyi bak'o" shafa addu'a hajiya ta yi tare da cewa "To ga ni nan zuwa". Ta fad'a tare da miqe wa ta nufi parlourn.
Chapter 30 · 0% Book details