Sashe 28
Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk wani motsi na su, daddy da ke gefe cikin wata mota me bak'in gilashi ya na kallon su, Wanda ba'a iya hango Wanda ke ciki sai dai na ciki yaga na waje,,,, zuciyar daddy har wani tafasa take saboda wani irin kishin Haajar da ke fizgar shi ,a gefe d'aya kuma wani irin haushin Dr.Zaidu ne ya kama shi ,musamman lokacin daya ga Haajar na masa murmushi, ji yayi kamar yabi takan su da mota ya taka su ,ko ya rage jin rad'ad'ad'i da zugin da zuciyar sa ke masa. Kan shi ya had'a da sitiyarin motar ,ya dad'e a haka a hankali ya fara samun nutsuwa ,hankalin shi ya dawo jikin shi ,kafin ya k'arasa cikin gidan...
A b'angaren Khaltum kuwa tun lokacin da Kubra ta gaya mata cewar babu mahaifa a jikin ta ta kasa samun natsuwa. Ko rufe ido tayi maganganun Kubra ne kad'ai ke yi mata yawa a k'wak'walwar kai. Gaba ki d'aya ta kasa samun kwanciyar hankali ,gashi ba ta da Wanda zata kira ya ba ta shawara. Sai a lokacin ta tuno da rabon da ta kira mahaifiyar ta har ta manta ,kuma ta sha ganin kiran ta a watannin da suka wuce amma ba ta d'auka, k'arshe ma sai dai ta katse kiran ,ba Dan komai ba sai Dan ganin da take yi kamar ta samu duniya a hannun ta. Jin dad'in duniya ya sa ta manta da komai da kuma kowa na ta ,ba ta sauraren kowa ,ba kuma ta da lokacin komai sai sha'anin gaban ta sharholiya. Sai a yanzu take da nasanin duk wasu abubuwan da suka faru a baya... Daga k'arshe ta yanke shawarar ta je asibiti wajen k'wararren likita ,ko zata cire shakkun dake zuciyar ta. Domin ta fi kowa sanin wacece kubra da kuma shu'umancin ta ,ta San kubra tantiriyar gaske ce matakin farko babu abunda baza ta iya aikata wa ba Dan ta cimma burin ta... Da wannan shawarar Khaltum ta yanke cewa za ta je asibiti ,duk da ba wai ta yadda da kalaman Kubra bane ,ta San da ran ta da lafiyar ta ba yadda za'a yi ace an cire mata mahaifa ba tare da sanin ta ba...
Washe gari da safe Khaltum ta shirya ta je asibiti. Kusan asibiti uku tana zuwa amma sakamakon iri d'aya ne shine ba zata tab'a haihuwa ba ,saboda babu mahaifar da d'a ze iya kwanciya a cikin ta balle har ta haife sa. Daga baya ma suka gano cewa ta tab'a samun ciki ta cire ,wannan Abu yayi matuqar d'aure wa Khaltum kai. Duk da irin jawaban da ta samu daga wurin likitoci daban-daban ,hakan be sa ta gama gamsuwa ba ,haka tayi ta yawo duk wani asibitin da ta ji ance sun k'ware wurin duba mata se Khaltum ta je ,amma maganar d'aya ce bata canza ba. Wannan al-amari ba k'aramin tayarwa Khaltum yayi da hankali ba...
Ta ci kuka kamar ba gobe ,idanuwan ta kamar za su fad'o k'asa Dan tsabar kukan da ta darza. Tana dawo gida sashen ta ta wuce ,ta fara watsi da duk wani abun da ya zo gaban ta. Tana kuka tana fad'in "Me nayi miki haka Kubra??? Wani irin laifi na miki da zaki mun wannan sakayyar??? Kubra kin cuce ni ,kin cuce ni,,, bazan tab'a ya fe miki ba,,, ko da zan tafi da zani d'aya se naga bayan ki ,,,,sai na d'au fansa akan ki,,, idan kuwa Kika ga ban zama ajalin ki ba ,to lallai ni ba 'yar halak bace..." Haka Khaltum ta yi ta sambatu iri-iri. Cikin d'an k'ank'anin lokaci ta fita a hayyacin ta ,idan ka ganta jiya ka ganta a yanzu ba zaka tab'a cewa Khaltum d'in daka sani bane.
Wayar ta ta d'auko ta kira mahaifiyar ta ko zata ji dad'i a ranta. Sai da kiran ya kusa yanke wa sannan Hajiya khairi ta d'auka. Wani matsananci Kuka Khaltum ta fashe da shi tana fad'in "Hajiya kubra ta cuce ni,,, kubra ta min kisan zaune,,, ta gama da rayuwa ta"...
Hajiya khairi tace " wai me kubran ta yi miki?"
Khaltum na kuka ta zayyanawa Mahaifiyar ta duk abunda ya faru....
A mamakin Khaltum sai jin tayi Hajiya khairi ta fashe da dariya tare da cewa "ba kiga komai ba khaltum. Wallahi so nayi ace kubran ta kashe ki gaba d'aya kowa ma ya huta. Mutuniyar banza kawai""" Hajiya khairi na gama fad'ar haka taja wani dogon tsaki tare da yanke kiran...
Wani irin ihu khaltum tayi ,Cike da tashin hankali ta yi jifa da wayar hannun ta ,se da wayar ta fashe ,a lokaci d'aya ta sake fashe wa da wani marayan kuka. Haka ta kwana a zaune tana aikin Abu d'aya.
Can cikin dare ta fara jiyo hayaniya sama-sama. Kamar dai ba zata fito ba ,Dan abunda ya ishe ta ya ishe ta ,sai kuma ta ji hayaniyar yayi yawa Dan haka ta leqo ta ga meke faruwa...
Wuta ne ke tashi daga sashen daddy. Dukkan ma'aikatan gidan sun taru a wajen suna ta aikin kashe wutar ,amma wutar kamar dad'a hura ta suke yi. Lubabatu se ihu take tana kururuwa ,wannan ne ya k'ara janyo hankalin mutane da dama zuwa wurin. Daddy baya nan d'aya daga cikin ma'aikatan gidan ne ya kira shi a waya ya sanar mishi da abunda ke faruwa, cikin mintunan da basu Gaza biyar zuwa goma ba sai gashi. Kubra ma bata nan ,sai su Haajar ne da basu San wainar da ake toya wa ba.
K'arar motar ruwa ta kashe wuta ne ya sa suka leko su ga abunda ke faruwa. Cikin tsananin tashin hankali suka k'arasa wajen. Mutane sai rirrik'e daddy suke yi dake ihun
"Dukiya ta!!! Jama'a Ku taimake ni!!! Duk Wani abunda na mallaka yana ciki!!! Ku taimake ni!!!""
Haka aka yi ta rik'e shi ,a cikin masu rik'o shi hadda Haajar dake ta aikin kuka.
Duk rashin imanin ka idan ka ga daddy a wannan ranar Dole ka tausaya masa. A haka yana ji yana gani komai da komai ya k'one k'urmumus ,sai wuraren asuba aka yi nasarar kashe wutar ,lokacin komai da komai na sashen daddy ya koma gawayi....
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[8/13, 8:58 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠
*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*
*INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN...ALLAH YA YI WA MAHAIFIYAR AUFANA RASUWA. D'AYA DAGA CIKIN MARUBUTAN QUNGIYAR MU TA INTELLIGENT. HAQIQA RASHIN MAHAIFIYA BABBAN RASHI NE DA YA FI KO WANI RASHI D'ACI A WANNAN DUNIYA. ALLAH YA JIQANTA DA RAHAMA YA KUMA KYAUTATA MAKWANCIN TA. AMEEN.😭😭👏*
_BABI NA TALATIN DA TAKWAS_
*____________________________*
_Haqiqa wannan al-amari na gobara ba k'aramin rikita daddy da duk wani masoyin shi ya yi ba fiye da yadda mai karatu ke tunani. Wannan na nufin duk wani wahala da daddy ya sha sama shekaru aru-aru ya tafi a banza. Dukiyar daya dad'e ya na tarawa yau rana d'aya ta qone qurmumus. Ka ma daga takaddun manyan gidajen shi ,takaddun manyan filayen shi ,takaddun kamfanonin shi ,kai hadda na kwantiragin shi komai ya qone. Lallai dole daddy ya shiga rud'ani da tashin hankali Mara misaltuwa. Domin kuwa kariyar azziki babban masifa ne ,Wanda ya zo mana a hadisi ingantacce cewa Annabi s.a.w yace "A TAUSAYA WA DUK WANDA KARIYAR AZZIKI YA SA MA"..._
Tun a washe garin ranar da abun ya faru Hajj Jamil ya samu labari. Dan haka be yi qasa a guiwa ba wajen zuwa yi wa daddy Jaje. Nan da nan gari ya d'auka, kasancewar daddy babban mutum ne. Nan fa k'ananan maganganu suka dinga tashi ,wasu suce " ije aka yi wa daddy saboda d'aukaka shi da Allah ya yi...wasu kuma suce da sa hannun abokan kasuwancin shi...kai wasu ma cewa suke da sa hannun uwar gidan shi wato Kubra... Haka dai maganganu suka yi ta yawo lungu da sako ,sakkwato da kewaye...
Har tsawon sati biyu da faruwar abun mutane kai kawo suke a gidan daddy wajen yi masa jaje. Yayin da matakan tsaro suka ba da k'aimi wajen tuhumar duk wani Wanda aka San abokin hammayar daddy ne. Daga k'arshe daddy yace ya fawwala wa Allah komai na shi, saboda haka a dakatar da binciken da ake yi Dan kar a d'au haqqin mutane da da ma.
Wata d'aya da faruwar wannan iftila'i wani masifar ya sake tunkaro wa. Dan kuwa Khaltum na nan akan bakan ta na ganin ta d'au fansa kan abunda kubra ta yi mata...
Wata rana Haajar, Suxee da Auta sun fita tare da daddy ,an je kai Haajar asibiti kasancewar ba ta jin dad'i. Haseena kuma tana gida tana bacci ko da suka tafi ganin hakan ma yasa basu tashe taba suka tafiyar su Dan ba dad'e wa zasu yi ba...Bayani Haajar tayi wa likitan akan duk abunda take ji. Ya basu gwaji na fitsari dana jini ,bayan an yi ,aka ce su dawo gobe Dan karb'an sakamakon. Da haka suka juyo suka dawo gida.
A garden daddy ya tsaya tare da auta. Haajar tace bari ta k'arasa ciki ta kwanta Dan wani jiri da take ji. Tare da suxee suka k'arasa...
Duk wani motsi na su akan idon Khaltum su ke yin shi. Sai da ta tabbatar ta ga shigar su sannan tabi bayan su. A tunanin ta ko Suxee da Haseena ne ,Dan bata ma San da Haajar a gidan ba.
Khaltum ce ta fito ta nufi sashen kubra. Sai da ta tabbatar ta kulle duk wani k'ofa da window na ciki da na waje, sannan ta haura sama ,inda ta tabbatar za ta samu kubra...
A kwance ta samu kubra ta jingina da kujera ,idanuwan ta a lumshe ,k'arar sauti na tashi a hankali. A gefe kuma ga lemu me sanyi a kofin glass da alama ta gama sha ne ta ajiye...
Jin kamar alamun tsayuwar mutum akan ta yasa ta bud'e idanuwan ta. A hankali ta sauke su akan Khaltum dake tsaye tana qare mata kallo tsaf. Tashi zaune kubra tayi ta zauna daidai kafin tace "Sannu da zuwa! Se kuma kika tsaya a tsaye sai kace wata baquwa? Ki zauna mana" ta fad'a tana nuna mata wurin zama