← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 52

Sashe 48

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Haajar ta k'arasa sashen Hajiya sai k'asa take da kai. A nan ta samu Hajiya ,suxee da Matar hajj jamil sai hira suke yi. Hajiya zaliha tace "ke kuwa kasuwa kike je haka?" Haajar tace " me kike gani?" Tace "to naga ina shigowa Hajiya ke cemin kinje sashen ki wurin daddy yanzu zaki dawo amma shiru-shiru kake ji kamar an aiki bawa garin su". Yak'e Haajar tayi tare da cewa " Baya nan ne koda naje yayi bak'u. Dole sai da ya sallami bak'on sannan na samu na ganshi muka yi magana" Suxee tace "ai ko da nace. Nima na ga kin dad'e". Hajiya tace " to ai shikenan ,tunda gata yanzu ta zo Sai Ku tashi Ku tafi yamma na yi ,Dan Ku dawo da wuri". Gaba d'aya Haajar a tsarge take. Hijabin ta kawai ya sanya sannan tayi gaba tana cewa "Hajiya mun tafi" Hajiya tace "A dawo lafiya". Nan suka fice. Ba su suka dawo ba dai takwas na dare. Tun daga ranar Haajar bata sake bari daddy ya rutse ta ba. Ga gidan na su ya cika da jama'a tinjim ,dangi na kusa dana nisa kowa kawo jiki yake yi banda gudunmawa da ake ta kawowa, kasancewar biki saura kwana uku. Washe gari aka je aka yiwa amarya jere a k'erarran gidan ta da ke k'ofar nasarawa. Gidan amarya Masha Allah abun sai Wanda ya gani. Daren biki babu wanda ya iya runtsawa, duk ana zazzaune a sashen Hajiya ba bu abunda ake yi sai hira kake ji yana tashi, da dariya ,duk wanda ka gani kasan yana cike da farin ciki. K'anwar baban daddy mai suna Anty Asiya tace " To Haajar maganar abinci fa?" Haajar tace "An gama wannan maganar. Dan ba a gida za'ayi komai ba sai dai d'an abunda ba'a rasa ba. Duk na sa a yi a wani gidan abinci kawowa kawai za'ayi idan lokaci yayi". Asiya tace " to ai shikenan ma ,hakan yayi kyau". Haka dai suka ci gaba da tattaunawa kan sha'anin bikin. Suxee na uwar d'akan Hajiya tana waya da Barr cike da so da qauna. Yana gaya mata yadda yayi matuqar kewar ta, Dan tun lokacin da za'a fara gyarata Haajar ta yi masa magana da kanta akan fa shi da amarya suxee sai dai ko a waya ,ko kuma idan an kai masa ita. Gara ma ranar da aka kawo lefen ta ya samu ganin ta ,shi d'in ma satar jiki tayi ba Wanda ya Sani ta fita suka gaisa sama-sama. Ba yadda ya iya Dan dole ya hak'ura da zuwa ba Dan ya so ba. Ko wani sak'o yake so ya bata sai dai ya aiko wata k'awarta ta family kuma 'yar uwarta mai suna fanna ita take zuwa ta amso ta kawo mata. Gyaran da Suxee tasha yasa duk a cikin kwana kin nan bata iya wani dogon bacci ,kai yadda taga safe haka take ganin dare. Dan wani wutar sha'awa dake fizgar ta. Ina ganin wannan abun ma na d'aya daga cikin abunda yasa Haajar ta dakatar da Barr Kabir daga zuwa gidan, Dan tasan k'arfin abubuwan da take baiwa suxeen da kuma lura da tayi na cewa suxee bata da wuyar tafiya...

Da daddaren tela ya yiwa Haajar waya akan ga d'ikin su ya kammala. Dama kamar yasan shi take jira, ta yi ta kiran wayar shi tsawon kwana biyu wayar shi a kashe ,ga shi hatta kayan da amarya zata saka yana wajen shi. Hak'uri ya ba Haajar tare da bata uzuri. Haajar tace ba komai. Ta cika masa ragowar kud'in shi sannan ta amso d'inkin ta koma cikin gida. a parloun Hajiya ta baje d'inkunan. Sai da ta fara zare nata Dana amarya da na hajiya zaliha da ta bada da kuma sauran 'yan uwanta da suma gaya mata za su zo bikin, dama ita Hajiya da auta tuni aka kawo musu nasu, sannan tace ga wa sauran 'yan uwa ga ankon data sanya a d'inka musu riga da sket na kwaddebuwa atamfa mai kyau da tsada. Kowa ya gwada Wanda ze yi daidai da jikin shi. Ai fa nan parlour ya kwacema da murna. Nan fa aka shiga gwaje-gwajen kaya ,sai godia suke mata da San barka. Tace duk Wanda basu samu ba su jira zuwa da safe za'a kawo wasu kayan, Dan tela biyu ta baiwa d'inkunan Dan a samu a gama cikin lokaci. Wannan abu yaiwa kowa dad'i musamman wa'yanda basu saka da kan su a lissafi ba ,sai suka ga Haajar bata ware su ba. Washe gari musamman Haajar ta d'auko mai kwalliya ta biyata dan a fito da amarya. Da safe misalin k'arfe takwas amarya tayi wankan ta na farko ,dama gashi tasha lalle da kitso. Ta fito cikin wata atamfa ruwan ganye mai ratsin fari, a inda takalmin k'afar ta da pos d'in hannun ta had'ida mayafin ta duk ya zama fari. Sarka da d'ankunnen dake wayar ta had'ida awarwaro da zobban dake hannun ta duk na gwal ne da Barr Kabir ya sanyo mata a lefe. Ba k'aramin kyau tayi ba duk inda ta wurga sai d'aukar ido take yi tana zuba wani mayataccen k'amshi. Guda kake ji ya kace ma ko ina da ko ina. Ga mak'awan gargajiya da suka doko sammako daga can wajen shigowa gida ,ganga suka shiga kid'awa suna wake daddy da kuma Haajar sai kace su ake yi wa biki. Sai da Haajar ta aiko tace amarya za su wak'e mata sannan suka canza salon gagangar su.

Zuwa sha biyu amarya ta sake canza kala inda ta fito cikin wata dakakkiyar shada mai tsada d'inkin doguwar riga daya amshi jikin ta. Haajar ba ta yi wanka ba sai da ta tabbatar ta gama shirya komai ,masu abinci sun gama sun kawo tare da ma'aikatan su da za su yi aikin zuba abincin. D'aki daya aka ware sai da aka cika shi da ruwa da kuma lemummuka. Sai da Haajar ta yi sallar azahar lokacin ana shirye-shiryen zuwa d'aurin aure sannan ta yi wanka. Ganin lokaci na k'urewa yasa tabar na ta shirin taje Dan ta shirya mijinta. Cikin wata arniyar farar shadda daddy ya shirya d'inkin babban riga wanda anko ne suka yi shida aminin shi hajj jamil. Misalta muku irin kyawun da daddy yayi b'ata lokaci ne Dan wallahi idan ka gan shi a wannan rana kai ka zata shi za'a je d'aurowa auren. Haajar ma saida tace "kai masha Allah! Ashe dai mijina kyakykyawan gaske ne? Wannan haka haka sai kace Kaine angon" daddy na dariya yace "to aini kullum ma ango na Dan yanzu ma da za'a bani dama Dana tabbatar miki da hakan" Haajar tace "to ank'i a baka daman" dariya yasa tare da cewa "matsoraciya" itama dariyar take yi tace "na dai ji". Nan fa soyayya ta dawo sabuwa Dan gaba d'aya Haajar ji take yi kamar kar daddy ya fita ya zauna tayi ta kallon shi ,ta kasa d'auke idon shi akanta. Yace " malama wannan kallon fa? Duk salon ki shanye dad'in gani na Amaryar da zan kawo ta rasa gane komai ko? Kinfa San ni mijin mace hud'u ne?" Haajar na dariya tace "Ah haba ai kuma Matan ka na aljannah d'an birni". Yace " allah ko?" Tace "yo wace zata wani so ka duk ka tsofe ka yi laushi ,me zata tadda ni din dai". Dariya dikkan su saka daddy yace " zaki yi baya ni ne ai idan na dawo ja'ira".
Chapter 48 · 0% Book details