← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 52

Sashe 3

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Se a lokacin kubra ta dawo daga garin tunanin data je.

Wata fajirarriyar dariya Boka RUBATSI ya fashe dashi tare da cewa

"Menene kuwa bazamu iya ba, wani aiki ne a doron duniya ze buwayi RUBATSI? Nine fa na gagari na gagari kowa,,, gagararren ma ni RUBATSI gagarar shi nake yi! A kashe,,,,a b'adda ,,,, a raba,,,,a yanka ashanye jini,,, gigitarwa ko hauka,,, wannan sune aiki mafi sauqi a wajen RUBATSI... Duk abunda kuke so Ku k'addara anyi an gama kawai"...

Cikin jin dad'i hajja Fati tace" ni fa aganina kawai boka a b'adda ta, ta yadda hatta mahaifiyar ta data haife ta bazata k'ara tunanin ta haifi me sunan taba. Kawai a jefa ta wata uwa duniya."

Kundin tsafi boka RUBATSI ya buga ,kafin Yace

"Wannan Abu ai me sauk'i ne da k'arfin tsafi." Hannu ya maida cikin kundin tsafin dake gaban shi ,tare da rufe ido ,se wasu sambatu yake yi irin nasu na guma-guman arna. Cikin mintin dabe Gaza sha biyar ba ,se ga aljani ya bayyana. A firgice kubra ta k'ank'ame hajja Fati, Dan kubra badai tsoro ba. Ita kanta hajja Fati dukda taurin rai irin nata ,ba k'aramin girgiza tayi ba.

Cikin wani harshe wanda ba wanda yake gane me suke cewa ,irin nasu na tsakanin Aljani da wakilin aljanin RUBATSI ke magana da wannan aljanin. Suna gama wa kuma b'at aka neme aljanin aka rasa, a wannan karon fitsari ne ya kusa tsiyayowa daga marar Kubra...

Boka RUBATSI Yace

"Wannan da kuka gani aljani SUFURSUNARI kenan. Cika aiki nake kiran shi. Kada Ku damu shine ya karb'i aikin Ku. Sedai ya buk'aci da akawo gashin kan wannan matar da aka d'aura auren ta da mijin ki ,da kuma d'ankwalin dake d'aure akan ta lokacin dazata shiga gidan. Ga wannan " ya mik'a musu wasu k'ullin magani da SUFURSUNARI yazo dashi. Yace "wannan Jan maganin ki tabbata Mijin ki yaci a abinci ko abun sha, sannan wannan bak'in kuma inaso kiyi girki ki had'a shi a ciki ,ki aikawa Amaryar. Wannan kenan ,na sallame Ku..."

Mak'udan kud'i Kubra ta Ciro ta zube su a gaban boka RUBATSI, sannan suka kama hanyar komawa gida.

B'angaren hajiyar Daddy kuma. Bayan sun kammala cin abinci da daddare ,tace "idan ka gama kazo d'aki inason ganin ka" ta fad'a tare da mik'ewa ta wuce gaba ,shi kuma daddy yana bin ta a baya, har suka shiga d'akin ta. Gefen gado ta zauna ,shi kuma ya samu guri a k'asa ya zauna. Hajiya ta kira sunan shi "Daddy!" Dan haka kowa ke kiran shi saboda sunan kakan shine yaci.

D'agowa yayi cikin ladaba Ya amsa da "na'am Hajiya!"

Ajiyan zuciya Hajiya ta sauke kafin ta soma masa magana cikin sigar lallashi

"Daddy sanin kan ka ne ,duk uwa baza yi abunda ze cutar da 'ya'yan ta ba koda kuwa 'ya'yan shegu ne balle na sunnah. Hak'ik'a rayuwar gidan ka kullum dashi nake kwana arai ,kwatakwata Allah be baka matar azziki ba, kubra mata ce da sedai ace Allah ya kyauta kawai, to na gaji da d'abi'un ta ,Sam baza'a ci gaba da tafiya haka ba. Saboda haka na binciko maka wata 'yar azzikin daga 'ya'yan qawaye na. Na shirya komai ,har ma an d'aura auren Ku d'azu da ranannan. Fatar zaka karb'a wannan auren hannu bibbiyu?"...

Darammm!!!Dasss!!! Gaban daddy yayi wani mummunan fad'uwa kamar an buga durom. Kasa cewa komai yayi se ma k'asa da yayi dakai.

Lura da yana yin daya shiga Hajiya tayi. Tace

"Daddy ko hakan me yi maka bane? Idan baka so base anje ko inaba se a warware auren ,tunda burin ka ka watsa min k'asa a ido, ka kuma nunawa duniya ban isa ba ,to ai shi kenan". Hajiya ta fad'a a fusace.

Cikin nuna damuwa daddy yace " Hajia kiyi hak'uri ,dama kubra nake tunani ,kar taga kamar ba'ayi mata adalci ba, sannan kinsan yadda zaman namu yake"

Jinjina kai Hajiya tayi kafin tace
"Naji kuma nasan komai ,sannan ka kwantar da hankalin ka ,wannan auren na maka shine dan ka samu kwanciyar hankali da nutsuwa a gidan ka. Kubra kuma bata isa tayi maka abunda Allah be nufa akan ka ba ,saboda haka ,muna nan mun sa rok'on Allah, komai kuma ze zo da sauk'i ,albarka ta na tare dakai. Allah yasan ya wa abun albarka"

"Ameen" daddy ya amsa. Kafin suka fara tsare-tsaren yadda komai ze kasance.

A washe gari ,a ranar ne daddy ze koma ,kuma lallai lallai Hajiya tace sedai ya wuce da Amaryar shi, ba yadda ya iya haka ya amince

Amarya kaltum ce a zaune taci ado ,ba lefi kuma tana da kyawun ta daidai misali daka ganta base an gaya maka kasan shuwa ce. Hajiya khairi itace mahaifiyar kaltum. Zaune suke tana gayawa kaltum yadda shirin su ze kasance

"Kaltum kin dai ga yadda nasha bak'ar wahala na kuma b'ata naira kafin na samu auren nan naki ya tabbata ko? To ba bacci zaki je yi ba ,tun wuri ya kamata ki San me kike yi ki kuma San gidan da zaki shiga. Kin dai ji abunda malam ya gaya mana ,matar shi kanta hatsabibiyar mata ce ,idan ba munyi da gaske ba zata ma iya kad'o ki... Ungo wannan" ta mik'a mata wasu qullolin magani tare da wata laya. Tace

"Wannan maganin ki tabbata dashi zaki rik'a masa girki ,wannan layar kuma a cikin filon da yake kwana akai anan zaki tsaga ki sake se ki d'inke da farin zare, daga nan magana ta k'are ,se na ji labari daga wajen ki."

"Karki damu hajiyar kaltum ,kisa aranki anyi an gama komai ,be matar shi kad'ai ba hatta hajiyar shi se ta dawo k'ark'ashin iko na"...cewar kaltum da kwatakwata ma idan ka ganta bazaka ce tana magana ba ,zubin ta irin zubin salihan matan nan ne ,sedai masifar dake cikin kaltum ya fita girma ,ita da kanta tsoron shu'umancin ta take yi...

Dariya suka fashe dashi tare da kashe hannu... Hajiyar kaltum ta dafa kaltum tare da cewa

" nasan ki sarai kaltum. Barewa bazayi gudu d'an ta yayi rarrafe ba. Fatar Nasara 'ya ta"...

Wani irin shu'umin murmushi kaltum tayi me k'ara wa fuskar ta kwarjini da haiba tare da lumshe manyan idanuwan ta ,tace

"Nagode Hajiya ta"...

MUJE ZUWA💃

TAKU HAR KULLUM

SIDIYA...✍️
[7/14, 6:32 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠

*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)

*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*

_BABI NA BIYAR_

*_____________________*

_GARIN SAKWKWATO_

_Tun kafin su k'araso, daddy yasa aka gyara d'aya daga cikin sassan dake gidan shi ,sashen dake tsakanin na kubra Dana shi ,nan yasa aka gyara wa Khaltum._ _Duk wani abunda ake buk'ata kama daga ,kayan d'aki Dana kitchen da duk wani abunda yasan ana zuba wa a d'akin amarya seda yasa aka zuba wa khaltum su, kaya masu kyau da tsada na zamani ,duk daddy yasa an zuba su a sashen Khaltum._

_Tun da aka wangale musu gate suka shigo ,khaltum ke santin gidan ,komai na gidan me tsari ne ,bata gasgata maganar hajiyar taba ,seda suka shiga harabar gidan anan ta gane wa idanuwan ta aljannar duniya._ _shiru ita dai ta kasa cewa komai. Bayan driver yayi parking ne ,daddy yace wa suxee_

"Yauwa Hajiya k'arama (sunan dayake kiran ta dashi kenan ,kasancewar sunan hajiyar shi ya saka mata). Kije ki nuna wa Antyn Ku sashen ta ,na gaya miki ai shine na tsakayi ko?"

Suxee k'ara fad'ad'a murmushin dake fuskar ta tayi ,Dan ita tun lokacin da daddy ya sanar musu auren ,dad'i taji mishi sosai ta kuma taya shi murna ,Haseena ce dai ke aikin kumbure-kumburen ta ,da k'ananan maganganun ta ,a cewar ta ,suna fama da kubra ,shine za'a tashi a k'ara musu wani jangwam d'in. Seda suxee tayi da gaske ,sannan haseena ta sassauto. Amsa masa tayi da

"To daddy"! Sannan ta kalli haseena tace " Haseena ke kuma kid'an taya mu d'aukan kayan zuwa ciki"

Yatsine fuska haseena tayi ,kafin tace

"Nifa Yaya suxee gaba d'aya na gama gajiya ne ,ga baba lawali nan kisa ya shiga muku dasu" tana gama fad'in haka ,anan tabar su ,tayi wuce war ta.

Murmushi daddy yayi ,shida kanshi shakkar haseena yake yi ,Dan haseena badai masifa ba kam ,ita bata iya Abu da zuciya biyu ba ,ko ya maka dad'i ko karya maka ,idan gaskiya yazo zata fad'eta. Magana yawa baba lawali akan ya taya su suxee shiga da kayan ciki. Suxee ce ta fara yin gaba d'auke da jakar kayan Khaltum ,ita kuma tana biye da ita a baya sad'af sad'af kamar wacce tayi k'arya.

Da talatu suka fara cin karo a sashen khaltum, gaishe su tayi sannan tace wa suxee

"Hajiya k'arama Dama Alh ne yayi waya akan mu gyara wannan sashen za'ayi bak'i ,sannan yace daga yanzu ni zan ci gaba da kula da sashen".

" good" suxee ta fad'a, kafin taci gaba da cewa "to bak'i dai gasu sun zo ,kuma ba masu tafiya bane ,masu zama ne insha Allah" a zuciyar khaltum kuwa cewa tayi zama daram-dam ma kuwa. Suxee nuna khaltum tayi tare da cewa

"Talatu wannan da kike gani ba bak'uwa bace ,Amaryar daddy ce ,da fatar zaki yi mata biyayya kamar yadda kike wa sauran manyan gidan?"...

Washe baki talatu tayi tana fad'in " Ah Ah! Kice Alh aure ya k'ara? To ubangiji Allah ya basu zaman lafiya."

"Ameen " suxee da khaltum suka amsa dashi ,kafin ta mik'a wa talatu jakar kayan khaltum, tare da cewa

"Anty Amarya muje ciki in nunna miki yadda gurin yake kafin in k'arasa cikin gida ko?"

Ba musu khaltum tabi bayan ta ,talatu kuma na biye dasu a baya. Wani had'iyar yawu khaltum tayi lokacin da taga irin dukiyar da aka narka a sashen ta. Komai na garin me tsari ne. Babban parlour ne a k'asa Wanda ke zagaye da d'akuna uku kowanne da toilet d'in shi a ciki. kitchen had'e da store a ciki ,se dining area daga cikin parloun. Yadda k'asan yake haka saman yake sedai shi d'aki biyu ne ,da babban parlour. Komai a tsare yake gwanin ban sha'awa.

Da murmushi shimfid'e akan fuskar suxee tace
Chapter 3 · 0% Book details