← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 52

Sashe 37

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata d'aya da faruwar hakan ,Haajar ta sake samun juna biyu. Murna agun daddy ba ka ma hannun yaro. Tarairaya kuma Sai kalar Wanda ya manta. Haka hajiy ma ta ke kula da ita sosai. A gefe d'aya kuma soyayyar Suxee da Barr dad'a qarfi ta ke. A kwana a tashi cikin Haajar ya kai watanni ukku. Ta yi kyau sosai ta qara haske. Wata rana da daddare daddy yawo da rana ya taradda Haajar d'in na bacci. Ganin yadda take baccin hankali kwance yasa bai yi yunqurin tashin ta ba. Zuqunnawa ya yi Sai tin fuskar ta ya sumbaci gefen kuncin ta. Ya d'auki abunda zai d'auka sannan ya fice. Suxee ce ta nufo sashen da fara'a d'auke a fuskar ta. Ta zo ta ba Haajar labarin yadda ta yi da Barr akan yana so ya turo. Yanayin yadda taga Haajar d'in ya yi masifar tayar mata da hankali. A sume ta ga Haajar d'in dirsashen a k'asa ga jini na mata zuba ba girma ba azziki. Da gudu ta koma sashen Hajiya ta fad'o mata. Hankalin Hajiya idan ya yi dubu ya tashi, ba shiri ta biyo bayan suxee suka zo sashen Haajar d'in. Anan hankalin ta ya sake ta shi ganin yadda jini ke yiwa Haajar d'in zuba kai kace an yanka rago ne. Rud'ewa Hajiya ta yi nan da nan ta fara kuka ,tace wa suxee "ma za ki kira daddy ki sanar da shi halin da ake ciki. Suxee ita ma hawayen take ,da sauri ta d'aga waya ta kira daddy ta sanar da shi halin da ake ciki. Ba'a fi minti goma ba Sai ga shi ya iso hankalin shi a tashe. Haka ya ciccib'e ta ya sab'a ta a kafad'a ,jinin duk ya b'ata masa jiki yana gudu Hajiya na bin shi a baya. Mota ya bud'e ya saka ta gidan baya. Hajiya ta shiga tare da ita ,Sai addu'o'i ta ke tofawa Haajar d'in. Suxee na gida saboda auta shi yasa ba ta bi su ba ,Sai kuku take yi tana addu'ar Allah ya ta shi kafad'un Haajar. Dan gani take yi rasa Haajar d'in zata yi kamar yadda ta rasa 'yar uwar ta haseena. Ranar kasa cin komai ta yi ,Sai aikin hawaye da ta kasa tsayar da su. Ba jimawa Barr ya je gidan ,a nan suxee ke fad'a masa Haajar ba tada lafiya an kai ta asibiti. Tambayar ta ya yi a ina asibitin ya ke? Ta fad'a masa sunan asbitin da suke zuwa. Ko zama Barr bai yi ba ya ka ma hanyar zuwa asibitin.

A asitin kuwa, farkon abunda aka fara nema shi ne jini. Ba halin ibar jinin daddy Sobada jinin shi ya hau a wannan lokacin. Hajj jamil daddy ya kira Dan dama jinin su iri d'aya ne za kuma su iya ba ma kowa. Leda biyu aka d'iba daga jikin Hajj jamil, kuma ledan jini biyar ake da buqatar a saka wa Haajar a wannan lokacin. Barr na zuwa ya taradda halin da ake ciki. Yace shi ma zai bada jinin. Bayan an gwada shi aka ga cewar shi ma zai iya ba ma kowa jini ,aka kuma yi masa wani gwajin aka gane baya d'auke da wani cutar da ze hana d'aukar jini a jikin shi. Nan ya kwanta aka d'iba leda ukun da ake da buqata ,yayin da aka jona mata wancan na farkon nan da nan Leda biyun ta k'are. Kusan dikkan su anan suka kwana. Sai washe gari hajj jamil yace wa Hajiya ta koma gida ko Dan su suxee su tabar su anan. Ba Dan ta so ba haka Barr ya dawo da ita gida ,sannan shi kuma ya koma asibitin. Ganin da Hajj jamil ya yi na cewar akwai buqatar daddy yabar asibitin ,Dan shakka babu idan yana ganin Haajar a wannan halin babu abunda zai hana hawan jinin shi kaiwa 280. Saboda haka ya yanke shawarar yi kiran yayar shi da ke bin mishi a waya wacce ke jigawa Anty zuwaira ,da mijin ta ya rasu. Kud'in mota ya tura mata. Ba b'ata lokaci Anty zuwaira ta had'o inata-inata ta biyo hanya. Sai yamma liqis sannan ya iso. Hajj jamil da kan shi yaje ya d'auko ta a tasha ,ya wuce da ita gidan daddy wurin Hajiya ,da ma ya sanar wa Hajiya da zuwan ta. Bayan ta yi wanka ta yi sallah ta ci abinci ,ta shirya Hajj jamil ya dawo ya d'auke ta yakai ta asibitin. Ranar Anty zuwaira ce ta kwana da Haajar a asibiti. Yayin da daddy ko kad'an bai so hakan ba. Yasan ko ya tafi ba ze iya gudanar da komai ba. Abinci ma yaqi ci tun jiya. Haka dai Hajj jamil ya lallashe shi suka dawo gida. Yace wa Anty zuwaira idan akwai buqatar wani abun ta kira shi a waya. Tace masa "toh". Gaba d'aya yanayin yadda Anty zuwaira ta ga Haajar d'in ta ji abun duk ba dad'i. Yadda dai aka gaya mata ciwon kwana d'aya ne ,amma idan ka kalle ta sai ka zaci ko ta yi wata ta na jinya. Ta rame ta fed'e ta yi fari tass alamar rashin jini.

Kusan kwanan Haajar hud'u bata farka ba. Kullum kuma su daddy Suna asibitin ba sa koma wa gida dai dare. Ranar da Haajar za ta farka ,ta farka a gigice duk Wanda zai tunkaro ta sai ka je tana fad'in "kar ki zo nan,,,mai nai miki?,,,Ku taimake ni" sambatu dai iri-iri Wanda kai da ka gani ka san ba na lafiya bane. Wannan Abu ya sake d'agawa su daddy hankali. Anty zuwaira ce ta yi wa Hajiya bayani akan lallai ya kamata a maida Haajar gida ,Dan ta fuskanci wannan ciwon ba na asibiti bane ,saboda wasu zantuttuka da Haajar d'in ke sakowa cikin dare. Hajiya tace itama gaskiya a yadda taga Haajar ta farka ta lura da hakan. Ta ma fi tunanin ko shafar aljannu ce. Duk yadda aka so a fahimtar da daddy ina ya kasa fahimtar su sai ma cewa da yake yi "Ni fa matata bata wani aljannu ,saboda me za Ku d'ora mata ciwon iska? Babu abunda ya had'a ta da iska. Kawai rashin lafiya ce. Kuma ko zan k'arar da dukiyata baki d'aya sai na nemo wa matata lafiya." Ganin kamar daddy ya hau da yawa yasa kowa ya zura masa ido. Kusan kwanan Haajar ashirin da d'aya a asibiti babu wani abun ci gaba. Kullum sai ruwa da jini da ake sanya mata, idan aka sanya mata jini yau ko da za'a duba gobe za'a ga kamar ba'a sanya ba. Su kan su malaman asibitin abun yana d'aure musu kai. Ga shi daddy ya k'i sauraren kowa akan a maida Haajar gida ayi na Hausa. Daga k'arshe Hajiya da ta abun na nema ya ci tura da kanta ta sa aka rubuta wa musu takaddar sallama. Da daddy zai yi magana tace masa "Kan naji kan na gani. Wannan umurni ne ba shawara ba". Ba Dan daddy ya so ba haka ya hak'ura aka maida Haajar d'in gida. Kwanan su biyu da komawa gida sai ga Abu na Nema ya fi na da. Dan Haajar matuqar aka bar ta ba kowa a kusa da ita to fa ta fara cin na kare kenan tana nema ta fita. Abun da ya sake K'ullewa ahalin gidan kai. Kowa abun da yake kawowa a ran shi Haajar ta had'u da shafar aljannu ne. Hajj jamil ya sake kiran Dr Imam mahaifin Haajar ya shaida masa halin da ake ciki. Ba Dan ya kammala abunda ya je yi a qasar da yaje ba ,haka yabar komai ya kamo hanyar dawowa gida Nigeria saboda yadda Hajj jamil ya zayyana masa ciwon babu sauqi sai a wurin Allah. Kwanan shi biyu kafin ya iso Nigeria ,sai da ya kwana a jigawa ya d'auko duk wani maganin da zai buqata, sannan ya hawo jirgi safe zuwa sakkwato.

Hajj jamil ne ya je ya d'auko shi ya kawo shi gidan daddy. A mutunce su ka gaggaisa. Babu Wanda bai yaba da dattakon Dr. Imam ba. Mutum ne mai matuqar karamci. Sai a yanzu Hajiya ta gane inda Haajar ta yi gadon mutunci. Sai da ya huta sannan aka kai shi sashen Haajar d'in. Ba qaramin tausaya mata ya yi ba. Ba dan ya na da qarfin hali ba, babu abunda zai hana bai yi mata kuka ba ,musamman yadda soyayyar Haajar take a cikin ran shi. Kaf a 'ya'yan shi babu Wanda yafi so sama da Haajar.

Hajiya ,hajj jamil ,Anty zuwaira ne a zazaune sun zuba wa sarautar Allah ido.

Daddy da ke gefe kamar a jikin shi ciwon yake Dr. Yace a d'aure masa ita da igiya. Kowa ya shiga zaro ido. Hajj jamil yace "Abbu Yusuf mai yasa ba za'a rik'e ta ba sai an d'aure ta?" Murmushi Dr. Iman ya yi tare da cewa "wannan aikin ba na mutum bane Jamilu. Kai dai Ku d'aure ta. Daddy ko motsi bai yi daga inda yake ba ,saboda tsabar tausayin Matar shi da yake ji. Ba Dan ma mahaifin ta bane shakka babu bazai bari a maida masa da mata kamar mahaukaciya ba. Da taimkon Dr. Imam hajj jamil ya samu nasarar d'aure Haajar d'in ,shi ma sai da ya zuba mata wani ruwan magani akai sannan. Sai wani zaro ido take yi tana fad'in " Kai kuma waye? Ka sake ni nace. Ba zaka sake ni ba? Sai na kashe ka mutumin banza". Sai kuma ta fashe da kuka tace "Me nayi miki? Kar ki kashe ni" can sai ka ji ta fashe da wani irin ihu Mara dad'in sauti...
Chapter 37 · 0% Book details