← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 52

Sashe 17

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aikam dai" Haseena ta fad'a tana jinjina kai.

Auta aka fara zuba wa ,tana fad'in "yeeh Yaya haseena ni aka fara zuba mawa" ta k'arasa maganan tana mata gwalo. Kowa se dariya yake mata ,banda Haseena data cika tayi fam Dan kwatakwata ita ba tada hak'uri ne.

Seda ta gama serving d'in kowa sannan ,taji da Daddy da ke cewa "Ai na d'auka 'ya'yan ki kad'ai kika sani ,saura kad'an Gidan Abinci yayi bak'o." Dariya dikkan su suka saka, seda daddy ya saki zancen sannan yama fara wai me nace ma? cewa fa nayi 'ya'yan ta ,kar yarinyar nan ta gano wani Abu a tattare dani fa, gaskiya ba k'aramar kwab'a nayi ba. Seda ya kalli kowa yaga hankalin sa baya kan shi ,kamar ma basu ji meya fad'a sosai ba da farko. Wani ajiyan zuciya ya sauke ,tare da furta Alhmdllh' a k'asan zuciyar shi, Dan shi Daddy Gaba d'aya ganin Haajar yake kamar matar shi ,musamman yadda suka zauna haka ,se yake ayyana inama ita kad'ai ce matar shi kuma uwar yaran shi ,lallai da yafi ko wani namiji alfahari da samun nagartacciyar iyali... Murmushi kawai yayi sannan yayi bismillah tare da kai abinci bakin shi.

Duk wani motsin da yake be San a idon Haajar yake yin sa ba ,kawai dai ta share ne tayi kamar hankalin ta bata wajen shi.

Cikin k'ank'anin lokaci daddy ya kauda abincin dake plate d'in shi ,dama ba wani da yawa ta zuba masa ba, ganin yana k'ok'arin bud'e kula ya k'ara ,Haajar tayi saurin taron hanzarin shi da cewa

"Bari in k'ara maka ,murmushin jin dad'i yayi ,tare da cewa

" Nagode? "

Wani kulan daban Haajar ta bud'e ta zuba masa abincin dake ciki. Nan danan Daddy ya fara auna shi ciki,,,, sedai dak'yar ya k'arasa had'iye abincin bakin shi ,wani irin kallon menene wannan? Yake bin Haajar d'in dashi. Gira ta d'aga mai alamar akwai matsala ne?

Daddy yace "Anya wannan abinci na ne kuwa?"

"Me ka gani?" Haajar ta tambaya kamar bata San komai ba

Yace "Naji abincin ne ba kamar irin Wanda na gama ci ba, kamar ma fa ba'asa gishiri ba ,ko me agwagi ne ake kiran sama na kasa ganewa!"

Dariya dikkan su suka fashe dashi, haseena tace "Daddy me zabo ake cewa ,ba me agwagi ba".

" komai dai menene Ku kuka San shi ,nida ba shiga kitchen nake ba ,taya zan wani San sunayen maggi?"

Haajar ajiye cokalin hannun ta tayi ,tare da nad'e hannaye a k'irji tace "Wannan abincin daga yau irin shi zaka dinga ci ,saboda tsaro"

Daddy wani zaro iro ya shiga yi tare da cewa " ni d'in kuma? Wai saboda me?"

Haajar tace "ka manta masu rashin lafiyar hawan jini abincin su daban ne? To abincin ka kenan har se an gwada ka an tabbatar mana da baka tare wannan ciwon kuma, idan ka bani had'in kai ,wata d'aya yayi yawa kaga komai ya wuce ,ka fara cin abinci kamar namu?"

Shiru Daddy yayi ,har cikin zuciyar shi yayi matuqar jin dad'in yadda Haajar take nuna damuwa da ciwon shi ,Dan shi yanzu har manta wa yake wai yana da hawan jini. Murmushin k'asan zuci yayi , a fili kuma ,had'e girar sama Dana k'asa yayi ,tare da cewa

"Ba wani wata d'aya da zanyi ina cin wannan abincin gaskiya ,kuma bari ki gani"

Basarwa Haajar tayi tare da cewa "OK fine".

Auta ce tace " Anty Haajar nima a k'ara mun, amma ba irin na Daddy ba.

"Oh no my baby girl! Ai bama zaki ci irin na Daddy ba , bari in k'ara miki kinji"

Dariya sosai Auta ke yi , da gudu ta zagaye ta kujeran da daddy ke zaune ta rad'a masa a kunne "Daddy kaga na sake yiwa Anty Haajar wayo ko? Kamar yadda na mata wayo tazo gidan mu. Kaima ka dinga mata mayo irin nawa"

Kusan dariya maganar Autan yaso yaba Daddy, shima rad'a ya mata kamar yadda tayi masa yace "Kice dama wayo kika mata ta biyo ki? To amma me kika ce mata?"

With full confidence Auta tace "daddy ce mata nayi fa idan bata zo gidan muba ,kuka zan dinga yi kuma bazan sake zuwa makaranta ba, to shine ita kuma bata so inyi kuka kuma bata so in dena zuwa makaranta ,shine fa ta biyo mu"..

Dariyar abun Daddy ya dinga yi ,tare da cewa " give me 5" bashi hannu Auta tayi suka kashe ,yace "Good girl ,u make it,,, maza je kici abincin ki kar Antyn ki ta gano kin gaya mun wayon da kika mata"...

Da sauri Auta ta koma kujeran ta ta zauna tana dariya. Haseena tasowa tayi tazo wuce wa tace " Daddy inji abincin ka" wani irin Harara ya watsa mata ,daya sa tayi saurin rufe bakin ta tabar wurin tana dariya. Kallon Haajar yayi data gimtse dariyar ta yace

"Kinga abunda kika janyo mun ko?" Tashi tayi itama tabar wurin tana masa dariya ,ba tare da ta amsa shiba. Parlour suka dawo suka zauna suna kallo cike da raha ,har kusan sha biyu na dare kafin suka koma sashen Kubra...

*____________________________*

Garin kano,,,, a kwana a tashi bikin Daddy da lubabutu ya rage saura sati biyu currrr! Shi Daddy Sam yama manta da zancen wani biki...

MUJE ZUWA💃

TAKU HAR KULLUM

SIDIYA...✍️
[7/30, 1:42 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠

*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)

*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*

_BABI NA ASHIRIN DA BIYAR_

*___________________________*

_Hajiyar Daddy tayi iya bakin k'ok'arin ta wajen ganin ta binciko halayen Lubabatu Dana iyayen ta ,amma duk Wanda tasa binciken amsar guda d'aya ce ,cewar su d'in Mutanen kirki ne ,sedai lubabatun bazawara ce ta tab'a aure ,shekaran su biyu Allah ya yiwa mijin rasuwa. Wannan shine kad'ai abunda ta iya gano wa ,gashi tayi binciken yafi sau a k'irga amma bayan yabon lubabatu da iyayen ta ba abunda ke zuwa kunnen ta. Ita dai Hajiya hankalin ta be kwanta da hakan ba ,amma ba yadda ta iya dole ta koyarwa zuciyar ta natsuwa da kuma son wannan auren ,Dan sau tari ma idan ta zauna se tayi ta tunanin anya badan bata son auren bane yasa take kawo shakku da kokonto, wata zuciyar kuma tace mata ,duk wani abunda ze fito indai ta b'angaren Hajiya Gwaggo ne to babu alkhairi a cikin sa ,daga k'arshe dai wani sashen zuciyar nata yake ayyana mata cewar 'suwaiba ba yadda zaki yi kuma ba kida abun yi ,daya wuce ki mik'awa Allah wannan al-amarin sannan kuma ki dage da Addu'a tare da nema wa MISBAHU zab'in Allah da alkhairi a cikin wannan auren ,ki kuma ci Gaba da saka mishi albarka ,saboda Addu'ar uwa mace tamkar taki ne tsiro take. Wannan shine kad'ai mafita a wajen ki'... Wani ajiyan zuciya Hajiya ta sauke tare da furta "Allah ya maka jagoranchi acikin al-amurran ka MISBAHU... Wani iska ta furzar tare da tashi taci gaba da ayyukan ta nayau da kullum..._

_Hajiya Gwaggo duk yadda taso ayi cakwaikwaiwa a wannan bikin ya faskara ,saboda lubabatu ta hana ,a cewar ta ita batason bidi'a ,bayan walima babu abunda za'ayi shima se idan an d'aure aure ,yinin biki ma bayi zatayi ba ,saboda bata son duk wani abunda ze tab'arb'are albarkar auren ta ,riya da bidi'a kuma na d'aya daga cikin rukuni na farko dake hana albarkan aure. Badan Hajiya Gwaggo taso ba amma haka ta hak'ura Dan Dole ,Dan gaba d'aya se ma fara jin haushin Lubabatun tayi, a haka dai biki keta k'aratowa ,babu wani alama daga b'angarorin guda biyu da zaka gane cewa hidimar aure ake yi ,aure ne dai gashi nan yadda kasan ma auren na dole ne ,Dan komai a kaffa-kaffa da nuk'u-nuk'u ake yin shi ,ba kowa ne yasan da zancen sha'anin ba ,se na jikin su..._

*______________________*

Ranar asabar ,ya kamata daddy na gida yinin ranar be lek'a koda k'ofar gida ba ,tun bayan daya dawo sallar asuba ,Dan kusan yanzu jam'i baya wucewa shi ,saboda akwai agogo me tunatar dashi koda ya shafa'a wato Haajar.

Bayan ya dawo sallar azahar ,Gaba d'aya dashi dasu Haajar suka d'unguma zuwa gidan gonar shi ,dake ta bayan gidan shi ,Wanda akwai gate da za'a iya shiga kai tsaye ta cikin gidan shi ,tsabar tsafta da kula da wurin ke samu ba dare ba rana yasa idan ba ance maka da akwai gidan gona a wajen ba ,Abu ne me matuqar wuya ga iya ganewa sab'anin sauran gidan gonakin ,sedai d'an abunda ba'a rasa ba na yanayin dabbobi.

Tun daga bakin gate Ma'aikatan wurin keta murna da zuwan daddy, duk Wanda ya gansu da sauri yake k'arasowa yana kwasar gaisuwa da mamakin ganin daddy a wannan lokacin ,bayan lokaci me tsawo daya d'auka baya kawowa wurin ziyara ,yau kuma se gashi.

Sannu a hankali suka shiga zaga wajen suna d'an tab'a hirar yadda abubuwa suka k'ara bunk'asa a wajen , nau'i-nau'i na dabbobi indai naci ne a gida gasu nan barkatai ,kusan cikin wurin ma gaba d'aya ya yiwa wasu dabbobin kad'an dole seda aka killace wasu daga waje.

A cikin hirar da suke yi ne jifa-jifa ,Haajar ke cewa " Ni kuwa Daddy wai kana fitar da zakkah kuwa?"

Dariya maganar taba wa daddy, maimaitawa yayi "wai ma ina fitar da zakkah? To amma me kika gani?"

Itama dariya taba kanta tace "Ah to eh mana, naga gidan gonar nan cike yake da albarkatun dabbobi ,amma banga alamar ana fitar da d'aya daga ciki ba ,Banga kuma alamar ana saida wa ba. Sannan ni a ganina iya wannan ma zaka iya fitar da zakka dashi ba ,ba Dole saka d'iba wani b'angare daga cikin dukiyar kaba".
Chapter 17 · 0% Book details