Sashe 39
Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
D'akin Hajiya aka maida Haajar d'in. Sai a lokacin kowa ya samu kwanciyar hankali. Hajj jamil jan Daddy ya yi suka tafi gidan shi ,a can suka yi bacci , ba su suka farka ba sai wuraren sha biyu na rana. Anty zuwaira ma zuwa tayi ta kwanta. Dr. Imam kuwa labari ya shiga baiwa Hajiya, kan abunda ya faru da kuma dalilin faruwar abun ,ya tabbatar mata cewa asalin tushen gurb'acewar rayuwar Kubra akwai sanya hannun mahaifiyar ta ,Wanda tun farko aka gina rayukkan akan b'ata da sagba ta miyagun jinnu, Wanda shi ne dalilin da yasa ko bayan ta mutu ta dawo a matsayin kuruwa. Wannan kundin kuma da aka k'ona shi ne asalin rayuwar Kubra... Ya faffad'awa Hajiya maganganu da dama na firgi ,al-ajabi da kuma ban tsoro. Hajiya ta yi ta mamakin dama hakan na faruwa a wannan duniyar ta mu? Dr. Imam ya tabbatar mata da akwai abunda ma ya fi wannan d'aure kai idan ta ji shi... Kusan kwanan Haajar uku ,ko k'wak'k'waran motsi ba ta yi ba. Wanda kowa ya damu da hakan. A gefe d'aya kuma mahaifin ta na ci gaba da yi mata addu'o'i da taimakon magungunan musulunci da yake da k'warewa akan su. Sai a rana ta biyar sannan Allah ya yi mata farkawa. Farin ciki ya dawo sabo. Kar ma daddy ka ji labari, Dan har rumgume ta ya yi Dan murna, ya ma manta cewar akwai mahaifiyar shi da mahaifin Haajar d'in a wurin. Nasihohi sosai Dr. Imam ya yi musu. Ya kuma ba da magungunan da Haajar d'in za ta ci gaba da amfani da su. Washe gari Dr. Imam ya yi musu sallama ya tafi. Haajar hadda kukan ta ,Dan sosai take kewar mahaifin na ta. Ya sha gaya mata a baya cewa duk soyayyar nan da yake mata ,za'a yi wani lokacin da wani ko wasu sun fi shi buqatar ta'. Shakka ba bu wannan lokacin ne. Bai tafi ba sai da ya yi mata nasihohi sosai itama, ya kuma k'ara gaya mata yadda mijin ta da ahalin shi ke matuqar Kaunar ta. Gargad'i Dr.Imam ya yi mata akan komai wuya wannan ahali sune abokan rayuwar tana duniya...
Kusan har aka yi sati Haajar bata gama dawowa yadda take ba, gaba d'aya jin ta take kamar ba ita ba. Daddy musamman ya shirya walima Dan yiwa Allah godia. Satin Anty zuwaira biyu ,ta koma gida jigawa a inda daddy da Hajiya suka cika ta da tarin abun alkhairi... Bayan wata d'aya. Komai ya lafa ,rayuwa ta dawo musu sabuwa. Haajar ta sake samun wani cikin. Kowa sai murna ya ke yi. A b'angaren d'aya kuma an so a saka ranar bikin Suxee da Barr Kabir ,duba da yadda soyayyar su tayi k'arfi. Haajar ta nema alfarman da a bari idan Allah ya sauke ta lafiya. Hajiya tace "duk yadda take so hakan za'ayi. Dan itace uwar amarya kuma uwar biki". Wannan batu ya yiwa Haajar d'in dad'i. Sannu da hankali cikin ta sai girma yake yi. Ta k'ara kyau ta yi haske gwanin sha'awa. Kulawa da tarairaya kuwa daga wurin daddy sai Wanda ya manta ,wannan ne ya k'ara bata damar murje gwad'arta take zuba masa zallar shagwab'a tare da nuna masa so da qauna a koda yaushe.
A b'angaren d'aya kuma Matar hajj jamil Hajiya zaliha ta dawo daga wurin aikin ta da take yi a wata qasa, Bayan tafiya na dogon zango da ta yi na tsawon watanni tara zuwa goma. Wanda a Qa'ida duk bayan wata biyar ta ke dagowa gida, tare da d'anta d'aya mai suna SAMEER. Abun ya yi matuqar d'aure Mata kai yadda ta dawo wannan karon Hajj jamil baya d'aukin ta ko kad'an kamar yadda ya saba. Hasalima ko kad'an bai nuna alamun jin dad'in ganin ta ba. A tunanin ta ko dad'ewar da ta yi ne bata dawo ba ya sanya ya ke fushi da ita, bata San abunda ya ishe shi bane ya ishe shi. Shi damuwar shi d'aya ne akan auren Suxee da Barr Kabir. Hajiya zaliha mace ce ta tsara daidai gwargwado da ta San abunda ya kamata ,tana da duk wani kwalitis d'in da namiji ke buqata, amma a zahiri bansan mai yasa ta fifita aikin ta sama da bautar auren ta ba, aikin ma a wata uwa duniya. Ta yi ta k'ok'arin ganin ta tambayi hajj jamil abunda ke damun shi. Hajj jamil mutum ne da baya tab'a iya b'oye damuwar sa idan ka tambaye shi. Ko kalma d'aya bai rage mata ba akan yadda yake matuqar son Suxee ,farin cikin shi shine ya ga ya auro ta tazo gidan shi a matsayin Matar shi ta sunnah. Hajiya zaliha ba ta gane wacce suxeen yake magana akai ba ,sai da ta sake tambayar shi, ya tabbatar ma ta da Suxee 'yar daddy da ta sa ni. Iya tashin hankali Hajiya zaliha ta shiga tashin hankali, Dan bata tab'a tunanin irin rana mai kama wannan zai zo mata ba. Ta yi kuka kamar ba gobe musamman yadda ta ga mijin ta ya susuce akan son 'yar aminin shi. 'Yar da idan da kara yace ya ba da ita ,ta badu kenan. Sosai tayi kaico da irin halin da ta sanya mijin ta a ciki ,ta yadda duk wani abun da zai je ya dawo laifin ta ne. Ta San bata kyauta wa mijin ta, d'anta da rayuwar auren ta ba ,kai hadda rayuwar ta kacokam. Ta yi matuqar tausaya wa mijin na ta da ita kanta. Gafarar ubangiji ta shiga nema ba dare ba rana ,Dan tasan matuqar ta mutu a haka ta shakka babu aljannah ko a gidan ubanta ake raba ta sai dai a raba babu ita. Da yake tana da rabo, watsar da duk wani rud'in duniya ta yi ,aikin ma tace ta aje ,ta dawo ta rumgumi auren da mijin ta hannu bibbiyu. Ta fara basa kulawar da a da can bata basa makamancin sa ba. Ta je ta cire tsarin iyalin da ta yi, a cewar ta bata son haihuwa da yawa ,Dan idan ta tara 'ya'ya za su hana ta aiki.. Ita dai aiki... Sosai ta ke iya bakin k'ok'arin ta na ganin ta kula da mijin ta. Hajj jamil ya ji dad'i sosai yadda Hajiya zaliha ta sauya lokaci d'aya, sai dai fa a gefe wutar son Haajar ne kawai ke dad'a ruruwa a zuciyar shi.