Sashe 49
Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Da haka daddy ya fito sakamakon hajj jamil daya yi masa akan yana jiran shi. Sai da ya fara shiga ya gaisa da su Hajiya. Taubasan shi sai tsokanar shi suke yi. Sannan yayi ficewar shi. Kwalliya aka tsantsarawa Haajar ta shirya cikin atamfa super Holland launin d'orawa da fari, d'inkin riga da sket pisis, Kai idan ka ganta kace ma ita ce Amaryar Dan tsabar kwawun da tayi. Fitowar ta yayi daidai da zuwan masu kid'an k'waryan data gayyato. Har ma sun fara k'ida mutane na rawa. Sai cigiyar ta suke ta lasifika suna fad'in "ina uwar amarya uwar gida a gidan alhaji Misbahu?" Kowa yayi wanka ya shirya ,tare da Hajiya zaliha da muqaraban ta suka sauko. Nan aka fara fito da abinci da abun sha ana kakkaiwa jama'a ,abinci sai kalan Wanda kake so. Ta sa aka warewa Hajiya da muqarabanta na su daban aka kai musu. Seda ta tabbata komai na tafiya da daidai sannan taje ta tutse suxee taci abinci dak'yar sannan ta sake canzo kaya suka fita fage. Suna tattaka rawa ga ruwan liqi da dake tashi. Aifa nan biki ya dawo kan su ,tsakanin Haajar da su idan ba wai ka San su ba ba lallai bane ka iya tantance wacece Amaryar daga ciki. Awa d'aya da fara kid'an k'warya suka sake komawa suka canzo shiga suka dawo. Mutane sai ido suke bin su da shi. A aka har aka dawo d'aurin aure ,su daddy suka wuce walimar da suka shirya na bayan d'aurin aure, wanda ya tara dandazon al-ummah. Wasu ma sai a ranar suka san daddy nada budurwar 'ya mace. Anci an sha a wurin walimar,wanda Hajj jamil ne ya shirya komai ,shine kuma mai kula da bak'in su. Sai wuraren la'asar suka yo gidan daddy da gayyar su. Gidan cindim yake da jama'a Dan se ka yi da gaske ma kafin ka samu wurin da zaka wuce. Mamaki ne ya kama daddy lokacin daya hango Haajar a tsakar fili tana takawa. Ba k'aramin kyau tayi masa ba. Sab'ewa su hajj jamil yayi ya kutsa har tsakar filin ya shiga yi mata lik'i, nan fa kallo ya koma sama. Yana mata liqi tana masa. Abokan su daddy suka dinga tambayar hajj jamil ko ita ce 'yar daddy?. Hajj jamil yace musu a'ah Matar shi ce. Nan fa aka shiga aka dinga musu liqi. Kafin daga baya suka fito zuwa sashen Hajiya. Har yamma ana ta shan sha'ani. Sai shida na yamma Haajar ta sallami masu k'idan k'warya saboda za su fara shirye-shiyen zuwa wurin dinna bayan magriba.
Misalin k'arfe takwas suka gama shirin su na zuwa dinna. Amarya tasha kyau ita da angonta. Haajar ma sai da taja daddy ,Hajiya zaliha kuma tare da hajj jamil. Komai ya tafi gwanin sha'awa. Duk Wanda yaje sai ya fito da tsaraban kayan biki kama daga jaka ,memo ,ankicip, kofin tangaras nashan shayi, kayan mak'ulashe da sauran su, Wanda duk Haajar ce ta dau nauyin komai.
Abun yayi matuqar k'ayatarwa. An shash-sha hotuna. Haajar Sai da ta keb'e mai hoto d'aya dake ta faman d'aukar su hoto ida da daddy ba tare daya Sani ba. Misalin k'arfe goma sha d'aya na dare aka tashi daga dinner. Kai tsaye gida suka nufa. Suna isa 'yan biko na zuwa. Ruwan lallen da aka jik'awa suxee aka bata taje ya ti wanka. Sannan ta fito. Haajar da kanta ta shirya ta cikin wata exclusive atamfa sannan ta d'ora mata alkyabba akai. Sashen Hajiya aka kaita su ka yi Mata nasihohi sannan aka kaita wurin su daddy, hajj jamil ne ya mata fad'a sosai shi dai daddy tun da yace "Allah ya sanyawa auren albarka" bai sake cewa komai ba. Suxee ta yi kuka kamar ba gobe, Haajar ma hadda hawayen ta. Daga nan aka wuce da amarya gidan ta. Haajar ta wuce mata da duk wani abun da zata buqata kafin gobe. Ko da suka dawo kai amarya kusan d'aya saura na dare. Lokacin duk ana zaune ana dudduba hotunan dinnan wa'yanda suka d'ad'd'auko da waya.
Anan sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya suxee da Barr Kabir...
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[8/31, 3:27 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠
*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*
_BABI NA HAMSIN DA D'AYA_
*_____________________________*
Washe gari misalin qarfe goma na safe su Haajar su ka fara shirye-shiryen zuwa gidan amarya ,saboda walimar da za'a yi yau a can gidan amaryar sha biyu na rana, wanda karantarwa ta sunnah manzo S.A.W yazo mana da shi ,wato walima bayan aure. Daga gida suka yi komai da za'a rabawa 'yan walimar, sannan suka d'auki duk wani abunda yayi saura na amarya Dan awuce mata da shi. Misalin sha d'aya su Haajar suka fara wucewa kafin wasu 'yan uwa suka ce zasu biyo bayan su idan lokaci yayi. Koda suka je Barr Kabir baya nan ,suxee ce kawai. Ta gyara ko ina da ko ina a gidan ta sanya turaren wuta sai k'amshi ke tashi. Tana ganin su Haajar ta fara murna hadda guntun hawayen ta ,Dan daga jiya zuwa yau ji take kamar ta shekara ne bata gidan su, sosai take kewar kowa nata. Gaggaisawa suka shiga yi ,bayan sun zauna suxee taje ta kakkawo musu abun sha. Haajar ta wuce uwar d'aki ,suxee ba ganin haka tabi bayan ta. Yanayin tafiyar suxee kawai Haajar ta gani ta gano cewa wani abun ya faru. Ba tare da suxee ta kula ba Haajar ta kafe ta da ido ,suxee na ganowa ta fashe da kuka tare da rumgume Haajar. Tausayin suxee ne ya kama Haajar, ta shiga bubbuga bayan ta alamar lallashi. Cikin muryar kuka suxee tace "Anya Anty Haajar zan yi zaman aure kuwa? Ba kiji yadda nake ji ba ,duk abubuwan da nake yi k'arfin hali ne wallahi saboda abunda kika gayamin cewa kar in bari kowa ya gane abunda ya faru tsakani na da mijina. Amma Anty Haajar yadda nake jin labari ba haka na gani ba. Wasu daga cikin qawaye na sunce min sai bayan sati d'aya ko sati biyu da auren su mazajen su ke kusantar su ,amma ni duba ki gani fa jiya-jiya. Kika kuma cemin ba zafi bayan ba haka bane". Suxee ta qarashe maganan tare da fashewa da wani sabon kuku. Abun yaso ya bama Haajar dariya amma sai ta dake tare da ci gaba da bata hak'uri " Hajiya k'arama ki dena kukan nan, ko so kike wani ya shigo ya gane wani abun ya faru ,bakisan wannan sirrin ki bane? Ko ni bai kamata ki gayamun ba".
Girgiza kai suxee tayi tare da share hawayen ta sannan tace "A'ah Anty Haajar. Ni a matsayin mahaifiya na d'auke ki ,bana tunanin zan iya b'oye miki komai. To idan ban gaya miki ba wa kike so ingayawa damuwa ta?" Haajar tace "hakane! To amma ki dena kuka. Sannan da kike zancen wai qawayen ki na gaya mi sai anyi sati ko sati biyu kafin mazan su su kusance su, angaya miki hadisi ne ko ayar allah? Babu wani nafsi daya ce haka, hasalima a karantarwa ta sunnah anfi son randa aka kawo mace mijin ta ya kusance ta shine maqasudin wannan walimar ta bayan aure. Idan kika ga miji ya d'aga wa matar shi qafa wannan ra'ayin shine da ganin damar shi, saboda haka ya kamata ki lura dakyau"