Sashe 14
Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Abbu sameer lafiya kake kuwa ? Meya same ka? Meyasa bakwa kwana a gida ba jiya? Hankalin mu ya tashi sosai ,jiya ban iya yin bacci ba, gashi nata kiran wayar ka baka d'aga ba. Me yake faruwa ne??" Dika a lokaci d'aya ta shiga jero masa tambayoyi ba k'ak'k'autawa.
Wani irin lumshe ido Hajj Jamil yayi ,a lokaci d'aya kuma yadda Suxee ke masa magana yaso ya bashi dariya...
Jin yayi shiru yasa ta fara hawaye, a tunanin ta ko yana cikin matsala ne ,dama gata gwanar kuka ,Hausa wa suka ce _tusa hali balle anci wake_.
Jin da yayi alamar kamar ta fara kuka yasa ,yayi saurin amsa ta da cewa "A'ah Hajiya k'arama lafiya ta qalau ,wata 'yar matsala ce kawai ta hana ni dawo wa jiyan"
Har lokacin bata dena ruwan hawayen ba, cikin muryar kuka tace "kace lafiyar ka qalau ,kuma kace wata 'yar matsala ce ta hana ka dawo wa jiya ,alamaun kenan dai kana cikin matsala" ta k'arasa maganan tare da fashewa da wani sabon kuka kamar wacce aka daka
Dafe Kai Hajj Jamil yayi tare da cewa "wai ni Allah na ,Hajiya k'arama rigima. To tsaya in miki baya kiji ni dakyau... Wani aboki na ne aka kira ni ba yada lafiya shine dani da Daddy muka zo duba shi ,to ba d'an garin nan bane, ba yada kowa anan ,shiyasa ni nakwana dashi ,daddy kuma an kira shi za'a sauke masa wasu kaya yau a store shiyasa ya tafi aida shi zan bari ya kwana anan ni kuma in dawo wajen Ku."
Se a lokacin daya mata wannan bayanin ne tukunna ta samu kwanciyar hankali. Share hawayen ta tayi ,tare da cewa
"Allah sarki ,Allah ya bashi lafiya! Muna yi masa ya jiki"
Murmushi Hajj Jamil yayi tare da cewa "Ameen Hajiya ta. To kiyi dariya mana, bana son wannan k'ananan kukan".
Wani murmushi ne ya k'wace mata ba tare da tayi niyyan yi ba Wanda ke k'ara fito mata da asirin kyawun ta, daga b'angaren shima ,murmushin yayi kamar yana ganin ta tare da cewa
" Good gurl. Se anjima idan na kira ko?"
Gyad'a masa kai tayi kamar yana ganin ta ,se kuma tace "OK take care". Kafin suka aje wayar. Haajar tuni ta b'ace a wajen ,ta shiga hada-hadar girkin da zata kai. Dan gaba daya hankalin ta baya jikin ta ,burin ta kawai shine taje taga wani hali Daddy ke ciki...
Daga b'angaren Hajj Jamil kuwa ,bayan ya kashe wayar ,murmushi ne d'auke a fuskar shi ,cikin zuciyar shi yake raya stubbornness irin na Suxee, yarinyar na burge shi ,musamman yadda bata iya b'oye damuwar ta, kai tsaye ce ita. A fili kuma ya furta " Suxee rigima ".
Mamaki ne ya kamashi lokacin daya duba agogo yaga sha biyu saura na rana ,duban shi ya maida inda Daddy ke kwance akan gadon asibiti, se ya fara tunanin meya sa Daddy be farka ba har zuwa wannan lokacin??? Nan kuma hankalin shi ya sake tashi...
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[7/26, 2:26 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠
*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*
_BABI NA ASHIRIN DA D'AYA_
*____________________________*
_Har ya yanke shawaran yaje ya sanar da Dr.Zaidu, se kuma ya tuna maganar da Dr Zaidun ya gaya masa jiya ,akan an masa allurorin bacci masu k'arfi ,amma ze iya farkawa a koda yaushe,,,,, 'to amma me yasa be farka ba har yanzu?' Hajj Jamil ya tambayi kan shi..._
_Sallar azahar ma kasa fita yayi ,anan cikin d'akin ya sake yin sallah ,Dan gaba d'aya jikin shi ya soma yin sanyi. Wuraren k'arfe uku na rana Haajar ta masa waya akan gata tazo asibitin, ya gaya mata suna Amenity room3. Bata wani sha wahala ba ta gane d'akin ,knocking ta masa ya bata izinin ta shigo, tura k'ofar tayi ta shiga bakin ta d'auke da sallama._
_Gaishe da Hajj Jamil tayi cike da girmamawa ,kafin ta ajiye basket d'in data zo dashi na abinci ,taja kujeran dake gefen gadon ta zauna._
_Ido ta zubawa Daddy nad'an wani lokaci, Gaba d'aya se da ta k'are masa kallo ,se taga kamar ba daddyn data Sani bane a kwanaki bakwai dasuka wuce ,ganin duk yabi ya rame yayi bak'i, tausayin shine ya k'ara kamata ,dukda bata San menene ainahin abunda ke damun shi ba,,, duban ta ta maida ga Hajj Jamil Wanda badan Daddy bane a kwance ,zaka d'auka shine Mara lafiyan, duk yabi yayi wani zuru-zuru. Fasa maganan da zata yi tayi._
_tashi tayi ta nufi basket d'in da tazo dashi. Flask ta Ciro ta aje gefe sannan ta d'auko cup da k'aramin spoon na shan tea. Tea ta had'a me kauri sosai Wanda ruwan zafin yaji kayan k'amshi ,sannan ta zuba doya da sauce d'in k'wai a plate ta kai gaban Hajj Jamil inda yake zaune kan sallaya ,ta aje masa, Dan base ta tambaya ba daga ganin shi akwai yunwa a tattare dashi. Ai Hajj Jamil kamar yana jira ,Kofin tean ya d'auka tare dakai wa bakin shi ,duk da irin zafi da tean yake dashi ,kurb'a ukku yayi sedai ya aje kofi, kan kace me zufa ya fara karyo masa ,Dan idan be manta ba rabon shi da abinci ,tun jiya war haka, A hankali ya fara cin doyan ,seda yaci sosai sannan yayi hamdala tareda ajiye cokalin me yatsu. Ruwan roba me sanyi ta sake kai masa ,ya karb'a yasha. Se a lokacin yaji kuzarin shi ya fara dawowa ba._
"Ya kika baro su Auta?" Ya tambaye ta.
Tace "Lafiyan su qalau ,dak'yar ma na sab'e mata ai ,seda na had'a ta da chocolate sannan ta banni na fito. Su suxee kuma na gaya musu zanje duba abokin ka da aka kwantar a asibiti, Hajiya k'arama taso ta biyo ni ,Dan ita gaba d'aya jikin ta yak'i ya bata, gani take yi kamar Kaine ba kada lafiya! Se da nayi ta bata baki tare da cewa ta d'ora mana girkin dare kafin in dawo ,shine fa ta hak'ura da zuwan."
Murmushi Hajj Jamil yayi Dan yasan Dole za'a zo wajen. Wani murmushin ya sake yi a Karo na biyu ,sedai wannan kaida ka gani kasan na k'unci ne sa takaici. Yace
"Ki duba ki gani ,sun damu dani fiye da yadda bakya tunani ,suna mun kallo d'aya da mahaifin su kuma saboda shi. Yanzu ki qaddara sun samu labarin mahaifin nasu ne a kwance , me kike tunanin ze faru?"
Jinjina kai Haajar tayi ,tare da cewa "hakane kam! Suna da nuna damuwa da mutum sosai ,kuma kamar yadda la lura akwai shak'uwa me tsanani a tsakanin su"...
Kad'a kai kawai Hajj Jamil yayi tare da cewa "Shine farin cikin su ,kuma shima sune kad'ai yake duba yaji sanyi a rayuwar shi. Akwai shak'uwa tsakanin su fiye da yadda tunanin ki ke baki"
Gyara zama Haajar tayi kafin tace "To amma meke damun shi ne haka ,wani irin ciwo ne wannan ,kuma menene dalilin ciwon?" Ta jero masa tambayoyin Jere da juna.
"Heart failure ,da hawan jini ke damun shi".. Ya bata amsa a tak'aice.
Zaro ido Haajar ta shiga yi tare da maimaita maganan " Heart failure da hawan jini??" Idon ta takai inda Daddy ke kwance cike da tausayin shi ta furta _"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un "_...
" Amma taya akayi wannan gagaruman ciwon ya had'u masa waje d'aya kuma a lokaci guda?"
"Iyalan shi ne sanadi!" Hajj Jamil ya bata amsa.
Da mamaki take bin shi da kallo ,alamar bata gane me yake cewa ba, tare da cewa "Amma taya ya iyalan sa zasu zama sune sanadiyyar nakasa masa rayuwa?"
"Eh iyalan sa!" Ya sake maimaita mata. Ya d'ora da cewa "ko kina mamaki ne?"
"Abun ne ai akwai mamaki. Iyalan sa fa?" Haajar ta maimaita.
Be jira ta sake wurgo masa wani tambayar ba ,ya fara bata labarin Daddy ,tun daga farko har k'arshe ,be rage mata komai ba dan gane da rayuwar Daddy...
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[7/26, 9:36 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠
*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*
_BABI NA ASHIRIN DA BIYU_
*____________________________*
_Gaba d'aya jikin Haajar ne yayi sanyi matuqa, girgiza kai ta shiga yi a lokaci d'aya wasu hawayen tausayin Daddy na sauko wa daga idanuwan ta. Tun da take a rayuwar ta bata tab'a cin karo da wani labari me kama da wanda taji yanzu ba balle makamancin shi, da wani ne yake bata wannan labarin ba qanin mahaifin taba ,shakka babu ba zata gasgata wannan batu ba ,ta kuma San a tsakanin ta da Hajj Jamil akwai wasa amma ba irin wannan ba._
_Haajar mace ce me tausayi da saurin karaya. share hawayen ta tayi a hankali ta furta "Abbu Sameer!" ,,,, d'ago ido Hajj Jamil yayi yana kallon ta. Tashi tayi daga inda take zaune ,ta koma gefen Hajj Jamil daidai inda yake zaune akan sallaya ta samu guri itama ta zauna._
_Magana ta fara yi masa k'asa-k'asa kamar me rad'a, ta yadda ba Wanda ze iya jiyo me suke fad'a, sun d'au sama da awa d'aya suna magana, daga k'arshe Hajj Jamil yace_
"To shikenan ,ni nasan abunda zanyi. Allah ya taimake mu baki d'aya".
Haajar ta amsa da " Ameen". Sannan ta d'ora da cewa "to yanzu Abbu Sameer me ake ciki game da rashin lafiyar Daddy? Naga tunda na shigo be farka ba?"
Hajj Jamil yace "Yadda kika ganshi haka ,haka yake tun Daren jiya, ni kaina abun ya soma damuna".
Shiru ne ya biyo baya nad'an wani lokaci, kafin Haajar ta mik'e tsaye. Basket d'in da tazo dashi ta nufa, ruwan zam-zam ta d'auko had'e da kofi, dawowa tayi ta zauna ,tare da tsiyaya ruwan zam-zam d'in gaba d'aya a kofin kasancewar ruwan Nada yawa kuma kofin ma Nada d'an girma. _SURATUL FATIHA_ ta tofa k'afa bakwai kowacce da bismillan ta, tsiyaye wa tayi cikin gora, ta rage saura a kofin, sannan ta mik'awa Hajj Jamil tare da cewa