Sashe 20
Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga nan kai tsaye sashen kubra ya nufa ,d'akin su suxee ya wuce kai tsaye ,yana zuwa ya banka d'akin tare da fara sauke musu ruwan jaraba
" Yanzu Ku har kunyi girman da zaku nemi Ku zubar mana da k'ima da daraja a idon mutane ,me kukayi kenan, kunzo kun wuce ta gaban mutane Baku san Ku gaishe su ba ,wani irin hali ne wannan? To bari kuji Sam Sam bazan d'auki wannan sabon iskancin Baku ba ,waji bane idan kuka tashi kuje da safe Ku gaida mutane"...
Haka dai daddy ke ta zuba ruwan bala'i ba girma ba azziki kamar Wanda aka yiwa abunda yafi haka.
Ga baki d'ayan su ba Wanda yace masa uffan har Auta dake zaune kan centre carpet tana shan ice-cream abun ta. Tab'e baki haseena tayi tare da cewa
"Cabd'i jamm!!! Ita kuma wannan da haka tazo? To Allah ya kawo sauqi"...
Daddy da kamar dama a jiraye yake, tasss!!! Kake ji ya d'auke haseena da wani irin zafaffen mari...
Gaba d'ayan su kamar an musu shock ,Suxee har da dafe kuncin ta ,Dan gaba d'aya ji tayi kamar a fuskar ta aka sauke wannan marin... Zaro ido suka shiga yi fuskar kowa d'auke da mamaki... Hatta auta seda ta razana Dan garin firgita har seda ta b'arar da roban ice-cream d'in ta ,kuka ta fara yi Dan ta tsorata ,da gudu tazo ta fad'a kan Haajar ,Haajar d'in ta rumgume ta tana bubbuga bayan ta alamar rarrashi...
Hannu ya shiga nuna musu tare da cewa " how dare u! Ina magana kina magana ,wacece ke. U better watch ur actions nonsense"... Yana gama fad'in haka yayi ficewar shi kamar Wanda ze tashi sama...
Haseena dafe ta kunci tana k'ara hakaito abunda ya faru kamar a mafarki ,Suxee rik'e da hab'a tana mamakin ikon Allah, Haajar kuwa rumgume da auta dake ta faman sauke ajiyan zuciya...
Suxee tace "Allah gamu gare ka ,jiya jiya daga zuwan ta, a kwana daya hakan ya fara faruwa ,me kuke tunani idan wannan takai wata d'aya a gidan nan? Ya kamata musan abun yi fa. Baku ga wani irin kallo data ke bin mu dashi d'azu ba?".. Cewar suxee
Wani irin murmushin mugunta haseena tayi kamar ba ita aka sauke wa mari yanzu ba tace " Ku banni da ita ,idan tasan wata ai batasan wata ba. Mummy zan kira duk inda suka je su dawo ,Dan sune kad'ai zasu mana maganin wannan me d'anyen kan, mu da muke da Hajiya kubra har za'a zo a nuna mana bariki?"...
Maganar seda taso taba Haajar dariya ,amma ta basar. Tunanin mafita take yi ,kafin daga baya ta sauke ajiyan zuciya alamar ta gano abun yi...
_kudan yi hak'uri da wannan. Kunsan hidimar sallah ,har yanzu ban gama samun kaina bane, amma Dana warware zaku jini insha Allahu. One luv💖🥰🥰.
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[8/2, 9:17 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠
*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*
_BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS_
*____________________________*
_Satin Lubabatu d'aya gaba d'aya Daddy ya rikirkice ya susu ce ,saboda ya samu kan zaran ,ga daddy mutum ne me tsananin son shan d'umin mace kawai Dan baya samu ne ,kuma gashi shiba ma'aboci Neman mata bane, Allah be tab'a d'ora mishi son bin matan banza ba. Har ya fara manta yadda ake kwanciya da mace tsabar an dad'e ba'a had'u ba ,se ga lubabatu, ita ma se da yayi kamar yanayi tukunna ya samu kanta ,bayan d'an k'aran wahalar data bashi. Dan a ranar farko daze kusance ta ita ta fara tsokano shi ,seda ta bari yawun shi ya tsinke yana gab ,sannan ta fara wani salon iya shege ,wai "Haba Alhajin Allah! Fisabilillahi haka ake wa amarya dama ,ranar da zaka fara kusantar matar ka ce ba wani kyautata wa se kace dai ba auren soyayya ba". Duk yadda daddy yayi k'i lubabatu tayi ,kud'i take so daddy ya bata gashi ranar ba kash a hannun shi ,yace ya mata transfer tace ita bata yadda ba. Sha biyu na dare daddy ya fito zuwa ATM Ciro kud'i ,se bayan ya dawo ya tuna da akwai ma kud'i a motar shi ,kwasa yayi dika ya had'a mata ,kud'i ya bata tsabar su Wanda ko shi be San ko nawa bane... Ai fa Lubabatu wasai, a Daren seda ta kusa mantar da daddy kowa nashi ,Dan seda ta tabbatar masa yayi aure, a wannan Daren daddy seda yayi d'an k'aramin hauka Dan tsabar kad'ewa da zautuwa ,sosai lubabatu ta bashi had'in kai ya murje ta son ranshi... Tun da lubabatu ta gano logon daddy ,shi kenan abun nema ya samu ,ta fara masa yawo da hankali ,idan ya matsa mata se ta nemi wani abun me tsoka Wanda daddy baya iya cewa A'ah._
_Tunda daddy ya gane shima ,se ya sakewa lubabatu bakin aljihun shi ,ya take mata kan maciji tana wasa da wutsiya. Wata sabuwar rayuwa suke bud'e ,aiki in baka yi bani wuri. Koda yaushe lubabatu na mak'ale da daddy tana masa kissa da kisisina ,shagwab'a da karairaya se Wanda ta manta._
Tun su Haajar suna tunanin ko daddy ze neme su ,shiru suke ji babu alamar hakan ,Dan gaba d'aya daddy mantawa yake dasu ,baya ta tasu ,ina ya fito lubabatu ina zashi lubabatu...
Wata safiyar asabar su suxee na zaune suna tattauna matsalolin gidan, Haajar ke cewa "Ni fa se nake ganin kamar bamuyi aiki da tunani ba, gaba d'aya mun yi wawanci wallahi ,ko Abbu Sameer daba fad'a masa fad'a yayi ta mun akan bamu kyauta ba ,to taya ma zamu ci ribar abun matuqar ba muna gano meke tafiya a can d'in ba. Ina ganin ya kamata mu sake taku"... Haajar ta fad'a ,amma a cikin zuciyar ta ita kad'ai tasan me take shirya wa...
Sauke ajiyan zuciya Suxee tayi kafin tace "nima fa abun ya soma damuna wllh Anty Haajar, idan zan iya tuna wa rabon mu da daddy tun randa ya shigo ya bud'e mana wuta ,washe garin kawo Amaryar sa kenan, yau gashi ana Neman wata kwatakwata daddy baya Neman mu ,kamar ma babu mu a gidan se sha'anin gaban shi kawai yake yi. Kuna gani fa kullum da yamma d'aukar matar nan yake suna fita kuma timing d'in su basa dawowa gidan se dare, ni wallahi ina jiyewa daddy tsoron kar yaje ya sakewa matar nan da yawa tazo ta ruzga dashi. Ga dai shi yanzu komai na tafiya daidai da alama tana kula dashi ,Dan ni nasan da akasin haka ne da tuni daddy ya neme mu, amma shirun yayi yawa ya kamata mu saka ido sosai"...
Murmushi Haajar kawai tayi Dan ita tuni tasan duk abunda ke guda na , kawai tana jira lokaci yayi ne.
Haseena tace " maganan ki gaskiya ne Yaya suxee, ni kaina abun ya fara d'aure mun kai ,amma ya kamata muyi wa toka hanci... Anan dai suka gama shirin su akan zasu je sashen daddy da daddare suga wainar da ake toya wa ,bayan Haajar ta jawa haseena kunne akan duk abunda zata gani kar ta yadda ta maganta ,Dan tasan halin ta bata gani bata tanka ba ,bata bi takan Suxee ba Dan ita bata fiye magana ba mace ce me zurfin ciki da qawaci ,duk abunda zesa kaga suxee tayi magana to ba kad'an bane...
Girki sukayi kamar yadda suka saba ,kowaccen su tasha doguwar Riga har Auta kamar masu shirin fita ,sashen daddy suka nufa kowaccen su da abunda take sak'awa a ranta...
Da sallama suka tura k'ofar parlourn suka shiga. Tsakar parloun kan carpet suka hango daddy da lubabatu cikin shigar k'ananan kaya ,daddy na bata abinci a baki ,ita ko lubabatu se zuba masa ruwan shagwab'a take yi ,gaba d'aya daddy yabi ya susuce se biye Mata take ,Dan duk wani abun da lubabatu zata yi burge shi take yi ,baya son jin lefin ta ko abun da ya tab'a ta. Ze kuma iya rufe ido ya ciwa ko waye mutunci akan ta...
Kallon kallon su Haajar suka shiga yiwa junan su. Sun kusa mintuna goma a tsaye ,sallama kuwa sun yi tafi a k'irga amma ba alamar an San da zuwan su balle a musu izinin shigo wa...
"Tofa! Wani sabon salo wai biredi a lefe. Kuga ikon Allah fa. Dole ya manta damu ai" cewar Haseena. Wani d'an guntun tsaki taja tana k'ok'arin fita Haajar ta dakatar da ita. Kallon tsaf Haajar tayi musu kafin ta k'arasa ciki tare da cewa su suxee "kuzo muje" ba musu suka bi bayan ta...
Fuska a sake Haajar ta fara gaida daddy sauran ma suka gaishe shi. Ba tare da ya d'ago ya dubi d'aya daga cikin suba ya amsa musu da "lafiya".
Gaida Amaryar sukayi ,sedai ita ba kamar daddy ba ,ta amsa su ba yabo ba fallasa. Sun d'an dad'e a zaune ba Wanda yace musu uffan kafin lubabatu tace
" Ku se yau kuka ga damar zuwa gaishe da sabuwar uwar taku?"
Suxee da haseena kallon junan su sukayi kafin suka maida duban su gun lubabatu. Haseena har ta bud'e baki zata yi magana Haajar ta kitse mata hanzari da cewa
"Ayi hak'uri. Dama mun d'an bar Ku ne Ku samu Hutu shiyasa bamu lek'o kuba ,amma ayi mana afuwa".
Tab'e baki lubabatu tayi kafin tace " Ba damuwa mun gode da ziyara. Alhajin Allah tashi mu shiga daga ciki na fara jin bacci" lubabatu ta fad'a cikin kissa tana duban daddy.
Ba musu daddy ya tashi ya shige gaba ita kuma tana bite dashi a baya. Kayan kallo ta kashe ,har takai k'ofar shiga bedroom ta jiyo tace
"Idan kun fita ,Ku d'an ja mana k'ofar. Seda safen Ku"... Ta k'arasa maganan tare murd'a k'ofa ta shige. Shigar ta ba dad'e wa ka fara jiyo muryoyin su daddy na mata wasa tana fashewa da dariya...
Su Suxee jiki ba k'wari suka kwashi jiki da kulolin da suka shigo dashi suka koma sashen Ku. A ranar kwana tattaunawa sukayi yadda zasu b'ullowa wannan rikitaccen al-amarin...
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[8/6, 7:00 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠