Sashe 19
Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan fa auta ta shiga rero kuka ba girma ba azziki ,kan kace me kukan har ya soma sakar mata zazzab'i. Da sauri Haajar ta janyo ta jikin ta "Na shiga aljannah na kasa fita ,Shukra Dan nace zan tafi shine kike wannan kukan?"
Gyad'a kai Auta tayi ido jawur. Haajar tace "to na fasa tafiya saboda ke ,idan ma zan tafi to tare zamu tafi kinji yarinyar kirki".
Rumgume Haajar Auta tayi tare da sakin wani ihu " Yeeeeeeeeeh! Anty Haajar tace tare zamu tafi" daga nan bata k'ara bi takan wasan ba ,zuwa tayi ta lafe kan cinyar Haajar ,Haajar d'in na bubbaga bayan ta kan kace me bacci ya kwashe ta ,se wani ajiyan zuciya take sauke wa ,kamar wacce akawa dukan tsiya. Mamaki ne ya kama daddy Dan shi be tab'a tsammanin Shak'uwar dake tsakanin Haajar da Auta yakai haka ba...
Tsabar takaici haseena tace "To wai daddy meze hana ka auri Anty Haajar d'in ta zauna damu, kana ganin dai abubuwan da take mana da kulawar da muke samu a wajen ta ,Wanda ko mahaifiyar da ta haife mu bata yi lokacin mu ba balle har mu samu wannan. Shine me kake tunani idan Anty Haajar ta tafi tabar mu? Ya kake tunanin auren da zakayi ze iya maye mana gurbin ta? ,nidai inaga gaskiya daddy ya kamata ka zauna kayi tunani akai. Nifa se nake ganin Anty Haajar d'in ce ma bata dace damu ba"... Haseena ta fad'a cike dajin haushin Daddy, Dan ita akan haajar gaba d'aya yanzu lefin shi take gani.
Kallon Suxee daddy yayi ,alamar kina jin abunda haseena ke fad'a? Gyad'a masa kai tayi tare da lumshe fararen idanuwan ta alamar gamsuwa da zantuttukan Haseena.
Kafin daddy yace wani Abu Haajar tayi saurin katse zancen da cewa " Dan Allah ka manta da maganganun su ,kasan har yanzu yara ne. Muna tayaka murnar auren da zakayi Daddy, Allah kuma ya tabbatar da alkhairi." Ta k'arashe maganar tare da mik'ewa tsaye ta ciccib'i Auta ta d'ora ta a kafad'ar ta, sannan tace masa "seda safe". Tana kai aya ,tayi ficewar ta.
Suxee da haseena ma tashi suka yi tare dayi masa seda safe suka bi bayan Haajar.
Kusan daddy sumar zaune yayi ,Dan gaba d'aya ya lura yaran shi sun fi damuwa da Haajar sama dashi ,sannan bawai son Haajar bane baya yi , A'ah kawai yana tunanin yadda ze tunkari Haajar ne da zancen so, zuciyar shi na raya mishi Haajar bazata tab'a son shi. Wani d'an siririn tsuki yayi tare da Furta wa a k'asan zuciyar shi "Suna gani ma har sun fi ni son ta ne ,duk son da suke mata be kai kwantankwacin Wanda nake mata ba ,balle har ya kamo k'afar shi"... Haka dai daddy ya koma kamar wani sabon zararre a wannan Daren ,kasa bacci yayi ,kwana yayi yana sak'e-sak'en yadda ze b'ullowa al-amarin, se wuraren asuba bacci yayi awon gaba dashi...
Washe gari da safe, Su Haajar basu zo breakfast a sashen daddy ba kamar yadda suka saba ,a gefen su sukayi ,sedai suxee ta kai masa nasa ,kuma koda taje ta tarar yana bacci ,bata yi k'ok'arin tashin shi ba ,ajiye masa kulolin abincin kawai tayi ta k'ara gaba. Daya fito, dukkan alamu sun nuna masa ba'a nan suka yi breakfast ba ,alama ta d'aya daya gane kuwa shine rashin jin k'amshi na tashi ,Dan 'ka'ida ne kafin su fara cin abinci se an gyara wurin ,k'amshin turaren wuta na tashi kamar baza'a mutu ba. Alama ta biyu kuma ganin kula biyu daya yi akan dinning yasan nashi ne kawai dan ba haka suka saba jera abincin ba... Ya kusa mintuna goma a tsaye yana k'are wa wurin kallo ,kafin daga bisani yaje ya zauna ya fara cin abincin, se dai kwatakwata baya jin gard'in a bakin sa ,haka yake cin abincin kamar yana tauna magani ,tsabar ba haka ta saba zama yaci abincin ba ,har cikin ranshi yake kewar rashin ganin su a yanzu, amma daya yi wani tunani ,se kawai ya dake ,tare da cewa "dani kuke zancen ,bazan tab'a Neman Ku ba ,Dan kanku zaku dawo"... Yana kammala cin abincin shi ,yayi ficewar shi zuwa sabgogin shi...
A ranar yasa aka gyara d'aya daga cikin sassan dake gidan ,tare da zuba duk wani abun buk'ata ,Dan ya musu waya akan kar su zo masa da komai, sedai sashen be kai girman nasu Kubra ba ,sannan shi iya na k'asa ne flat babu bene...
Da daddare aka kawo Amarya. Tun ranar da aka kawo amarya daddy be sake sa su Haajar a ido ba ,abincin ma da yake tunanin ko zasu aiko masa tun a ranar farko shima shiru babu alama ko samatan hakan.
Wani abun takaicin ma, duk hasashen da daddy ke yi shine za'a kawo masa amarya ya amayar da shak'uwar sa ,amma ina sedai hak'ar shi bata cimma ruwa ba...
_Ku biyo ni Dan jin dramar da daddy da lubabatu a ranar da aka kawo ta_😂👌🏻
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[8/2, 2:06 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠
*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*
_BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI_
*____________________________*
_A ranar da aka kawo lubabatu ,daddy na zaman jiran ta a sashen shi shiru har kusan biyu na dare bata ba labarin ta,,, daya kira ta a waya akan yana Neman ta ,se ce masa tayi shi me yake da baze zo inda take ba, hala be San gajiyar hidima bane, ai seda tace ya biya musu jirgi amma yak'i yace dole sedai ta mota ,to ita yanzu gaskiya ta gaji ,daga kan gado ma bazata iya sauka ba ,idan Abu me muhimmanci yake d'auke dashi yaje ya same ta...shirun da lubabatu taji daddy yayi yasa taja wani d'an siririn tsaki tana fad'in "naga alama ba abunda ke damun ka, saboda haka se da safe". Ta k'arasa maganan tare da yanke kiran_
_Washe gari da 'yan rakiyar amarya zasu koma ,da kanta taje ta sami daddy kwance akan gado yana bacci. Iskan bakin ta ta shiga hura masa a kunne daddy na k'ara bin gado, a tunanin shi ko iskan panka ne ,dadai yaji abun baze k'are ba ,bud'e lumsassun idanuwan shi yayi tare da zuba su akan lubabatu, murmushi ta sakar mishi cike da k'warewa tana fad'in_
" Ango kasha k'amshi! Wannan irin makara haka. To ka tashi kayi wanka ,muje mu samu bak'in mu ,Dan yau zasu tafi yanzu haka ma shirya-shiryen tafiyar suke yi ,gaka se a samu abunda za'a basu ,ina lefin wa'yanda suka yo tafiya fiye da kilomita 200 Dan su kawo maka amarya ,kai fa suka yiwa wannan k'ok'arin ,saboda haka Dan Allah idan zaka sallame su ai musu sallama me tsuko da za'a tabbatar da lallai cewa na zo _GIDAN MISBAHU_ ta k'arasa maganan tare da yin wani irin k'ara. Shidai daddy da ido ya bita ,a ranshi yake cewa wannan kuwa lafiyar ta? Kamar taji me yace tace "Lafiya dai?"
Yak'e daddy ya mata tare da cewa "Bakomai" ,,,,daga haka be k'ara mata ba be rage mata ba ,ya tashi ya fad'a toilet ,wanka yayi tare da d'auro alwala. Towel ya fito dashi iya k'ugun shi... Har lokacin Lubabatu na zaune kan gado. Ko ta kanta be biba ,ya bud'e sif d'in shi tare da d'auko mayukan shafawan shi da turaruka...taso wa lubabatu tayi cike da k'ware wa ta k'araso har inda daddy ke zaune ,karb'an man shafawar tayi daga hannun shi ,ta shig Shafa masa tana wani irin salo me gigita tunanin d'an Adam,,, jin da daddy yayi kamar ze sauka a network yasa yayi saurin dawo wa hayyacin shi tare da mik'e wa zunb'ur ya Fara k'ok'arin saka kayan shi, har lokacin idanuwan lubabatu na kan shi ,se bin shi take da wani mayataccen kallo na k'urulla ,tana had'e yawu...
Daddy kauda kanshi yayi gaba d'aya daga gefen ta ya maida hankali gun saka kayan shi ,seda ya gama yazo ya wuce ta gaban ta ze fita, hannu lubabatu tasa tare da janyo shi baya ,tana fad'in "Haba ranka ya dad'e ,kafa San kai na tsaya jira ,daka gama ai se kace mun in taso muje ko?" Shidai daddy be ce mata ci kanki ba. Taso wa tayi ta sagala hannun ta cikin gurwar hannun shi a haka suka fito se surutai take masa ,wani yayi murmushi wani kuma ya share ta...
Fitowar su yayi daidai da dawowar su Haajar da alama siyayya suka fita yi ,Dan ko waccen su d'auke take da ladodi a hannuwan ta. Ganin su yasa ya k'ara fad'ad'a murmushin dake shimfid'e a fuskar shi...
A zaton shi ko zasu k'araso a gaisa ne ,se dai hasashen shi yasha banban ,Dan kuma gimtsewa suka yi gaba d'ayan su tare da d'auke kai kamar ma basu ganshi ba ,daga k'arshe ma suka canza hanya ,suka bi ta baya...
Wani iri daddy yaji a ranshi. Lubabatu dake ganin duk abunda ke faruwa ,cike da isa tace "Alhajin Allah wa'yancan ba 'ya'yanka bane?"
Gyad'a mata kai yayi alamar eh. Wani siririn tsaki taja tare da cewa "Dan wulaqanci tsabar sun raina mutane shine baza su iya zuwa su gaishe mu ba? Ko ba komai ai naci albarkacin uban su kai ko? Ga bak'in mu a cikin gidan nan ,yaran nan Dan fitsara basu je sun gaishe suba, me kake tunanin bak'in namu zasu d'auka ,ai gani zasuyi kamar yaran basu da tarbiya ,aje ana cewa 'ya'yan mijina basu da ta ido , aini zasu zubar wada daraja, da a gaban mutane sukayi haka me kake tunani ,lefin mu za'a gani ,gaskiya kayi musu magana Dan wannan raini ne"... Ta k'arasa maganan tana goge hawaye ,kona menene ohon mata.
Ai fa nan daddy ya k'ara harzuk'a ,Allah Allah yake yaje gama sallamar bak'in ya koma ta kan su, yaji dalilin su na son zubar masa da mutunci agaban matar data zo jiya-jiya. Sama sama ya gama sallamar bak'in se murna suke yi ,Dan kyauta daddy yayi musu na gasken gaske ba nida kyauta ba, ya kuma basu mota aka maida su har gida cike da abun alkhairi...