← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 52

Sashe 24

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Suxee na kuka nan ta gaya masa duk wani abun da ya faru a Daren jiya har kawo zuwan su asibiti. Wani irin imani ne da tsoron Allah ya cika zuciyar Hajj Jamil ,a lokaci d'aya wani tsoro ya dad'a mamaye masa k'irji_

Be iya cewa komai ba se "Yanzu ina daddy yake?"

A tare suka shiga inda wani d'aki na kwanan likitoci da Dr. Zaidu yakai daddy dan ya huta ya kuma samu kwanciyar hankali. Hannu biyu daddy yasa ya rik'e hab'a ,idon shi a lumshe kamar me bacci ,a zahiri kuma kwanto yayi ba bacci ba. Auta ce kan gado daga gefen shi tana rankon baccin wahala.

Wani irin tausayin daddy ne ya k'ara kama Haj Jamil. K'araso yayi har inda daddy ke zaune ya dafa kafad'ar shi ,tare da kiran sunan shi a sanyaye

D'agowa daddy yayi yana duban shi ,ba tare da ya sani ba wasu siraren hawayen suka fara gangaro masa. Zuciyar hajj Jamil ce ta sake karaya. Girgiza masa kai yayi alamar hakan be kamata ba, tare da nuna masa Suxee dake gefe itama tana aikin zubarda k'walla tun Daren jiya

Hannun daddy ya rik'o suka fito waje. Ya dubi suxee yace ki zauna muna zuwa ,kuma ki dena wannan kukan bana so. Kai kawai ta iya gyad'a masa ba tare da ta iya tare hawayen dake ambaliya a fuskar taba.

Mota suka shiga ,Haj Jamil ya data motar. Gidan shi suka nufa. Seda ya tabbata daddy yayi wanka ya kawo masa Abu me sanyi ,dan yasan shine kad'ai abunda daddy ze iya sha a wannan lokacin...

Bayan ya huta sannan Haj Jamil ya fara tausasan daddy da duk wani Kalma na lallashi daya sani a duniya ,tare da k'ara ankarar dashi game da 'yar taqaitaccen nasiha akan qaddara ta alkhairi data sharri. Ya k'arasa maganan tare da cewa "MISBAHU bawai dan kace kayi imani bane kawai yasa Allah ze barka baze jarrabe ka ba. Cewa kayi imani bashi ya nuna Allah baze yi maka gwaji yaga shin lallai imanin nan da kace kayi da gaske ne ko be kai zuciya ba. Saboda haka duk ka d'auki wannan a matsayin jarabawa daga Allah, kowa da tasa kalan qaddarar wani idan kaji nashi zaka ce naka ba komai bane ,saboda duk yadda kam cikin masifa wallahi wani ya fika ,haka duk yadda kake cikin jin dad'i wani ya fika. To Dan haka ka d'auka wannan shine kalar taka qaddarar kuma ka gode wa Allah da abun ya tsaya iya nan"...

Har cikin ran dad'i yaji dad'in maganganun Haj Jamil ya kuma San gaskiya yake gaya masa amma wani b'angare na zuciyar tashi na k'aryata hakan. A hankali ya sauke ajiyan zuciya tare da cewa " Haj Jamil yanzu har kana ganin akwai Wanda ya kaini shiga masifa balle har ya fini??"

Murmushi Haj Jamil yayi tare da cewa "wani tunda aka haife shi a masifa ya fad'a a haka kuma yake ci gaba da rayuwar shi, kai kuwa se da kayi auren farko tukunna kasan menene matsalar rayuwa ,Ashe ma ubangiji nason ka...yanzu kai idan baka Bawa zuciyar ka hak'uri ba ,taya zaka iya rarrashin yaran nan?"

Sauke numfashi daddy yayi kafin yace "Hakane! Amma Haa.." Be k'arasa kiran sunan Haajar ba Hajj Jamil yace "mu bar wannan maganar yanzu ,zamu tattauna akai wani lokacin"...

Da haka dai Hajj Jamil yaci gaba daba daddy baki har ya samu kanshi. Seda ya tabbatar ya samu nutsuwa sannan suka koma asibitin. A hanyar su ta koma wa asibitin suka tsaya suka siyawa suxee da auta abinci, duk da daddy yasan halin suxee sarai da qawa zuci ba lallai ta iya sawa bakin ta wani abun ba saboda har yanzu ba'a hayyacin ta take ba...

A b'angaren su Hajja Kubra kuwa ,an dawo daga Germany ,sun k'ara gogewa sun yi kyau abun su iskanci da rashin mutunci kuwa se abunda ya qaru. Wanda yasan su da idan ya gansu yanzu ze tabbatar da akwai tarin canje-canje.

Da dawowar su ko wacce sashen ta ta nufa, kubra bata lura da sauye-sauyen dake sashen taba ,kai tsaye wanka ta fad'a ta sakarwa kanta ruwa ,ta dad'e a band'aki kafin ta fito ,rigar bacci kawai ta iya saka wa ta kwanta nan da nan bacci ya kwashe ta ,ba ita ta farka ba se yamma...

Bayan ta tashi ne take tunanin ko ina su auta suka je ne ,Dan taji bata jiyo motsin suba. Tab'e baki tayi tare da cewa "k'ila kuma ya kai su kano".. Da haka taci gaba da gudanar da al-amuran ta...

A b'angaren Khaltum kuwa ta kammala duk wani shirin ta tsaf na karb'ar girki a Daren ranar, a yayin da kubra ita ma ta gama shirin ta na zuwa tunkarar daddy duk da cewar ita ba girkin take da niyyar karb'a ba amma kuma tana kewar mijin ta ,tana so ta gan shi...

Da daddare Lubabatu na zaune a parloun daddy tana kallo ,khaltum ta banko k'ofar ta shiga. Lubabatu dake zaune taso wa tayi a tunanin ta ko daddy ne amma se taga akasin hakan.

Da wani irin d'an iskan kallo khaltum tabi Lubabatu ,yayin da itama take maida mata da martanin ke kuma daga ina???

Cike da tsiwa Lubabatu tace " Ke kuma malama daga ina? Kin shigo wa mutane ba sallama ba komai ko an gaya miki nan choci ce?""

Wani irin azababben mari khaltum ta kwasawa Lubabatu tare da cewa "Ni sa'ar kice daza ki dinga gaya mun duk kalamin daya zo bakin ki? Ko kuwa ba'a koya miki tarbiyya da iya magana bane daga gida? Banza shashasha. Ni ba wurin ki nazo ba wajen me gidan nazo, ki bari zan dawo ta kan ki".. Khaltum na gama fad'ar haka taja wani dogon tsaki tare da nufar hanyar bedroom d'in daddy ,shiga tayi ta dudduba seda ta tabbatar lallai baya nan sannan tazo ta wuce Lubabatu dake tsaye tare da banka k'ofar...

Wani irin shu'umin murmushi Lubabatu tayi tare da cewa " lallai kuwa wannan matar baki San wa kika Mara ba ,Ashe kuwa zaki yi Dana sanin mari na da kika yi a yau ,Dan ni Lubabatu kabewar kan dutse ce ban fito ba seda na shirya. Wi k'aramar kura a kashe ki a d'au alhaki ,a barki ki girma ki kar mutum. Wannan duk kirari na ne, Bana barin bashi. Amma muje zuwa da sannu zan sa ki kwashe kashin ki a hannu. Banza sakariya kawai"... Wani gajeran tsaki taja sannan ta koma ta zauna ta had'e k'afa d'aya kan d'aya tana girza kai tare yin k'wafa...

Kai tsaye Khaltum sashen Kubra ta wuce a kan stairs taci karo da kubran tana sauko wa. Kubra ganin data yi ran Khaltum a b'ace yasa ta tambaye ta "Yaya?" Nan Khaltum ke sheda mata duk yadda suka yi da Lubabatu a k'arshe ta k'ara da cewa "Har cewa tayi ba ni ba ko ke baki isa ba"...

Wani d'an tak'aitaccen murmushin gefen baki kubra tayi ,tare da cewa " Ina ba dai ni ba. Ta dai yi dake Dan inaga kun fi zama kai d'aya "

Da mamaki Khaltum tace "Ban gane me kike nufi ba?".

Kubra tace " zaki gane a gaba".

Wasa-wasa kusan kwana ukku daddy be koma gida ba ,yana asibiti tare da yaran shi yana kula dasu. Babu yadda Haj Jamil beyi akan ya koma gida ba amma yak'i.

Ganin har kusan rana na hud'u daddy be dawo ba yasa kubra ta kira shi a waya, amma be d'aga ba, Khaltum ma ta kira shi yafi sau nawa amma yak'i d'auka...

A washe gari ne Haajar ta farfad'o ,dan seda aka mata d'inki tsabar k'aruwan data yi. Amma Haseena kam se abunda Allah yayi...

MUJE ZUWA💃

TAKU HAR KULLUM

SIDIYA...✍️
[8/10, 8:13 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠

*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)

*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*

_BABI NA TALATIN DA HUD'U_

*___________________________*

_Alhamdulillahi Haajar ta samu sauqi sosai ,dan kusan Yanzu ita ke kula da Haseena. Tun bayan abunda ya faru Haajar ta d'auke wa Daddy ,bata wani yi masa magana sosai se can baka rasa Ba, shima se idan maganar ta kama na dole ne kawai take yi masa. Ba kad'an ba hakan ya damu daddy ,gashi Hajj Jamil ma kwana biyu be zo asibitin ba balle daddy ya samu damar sanar dashi halin da ake ciki. Wasa wasa har kusan sati biyu Hajj Jamil be shigo ba ,tun abun baya damun daddy har ya soma hasashen abubuwa da dama. Dan Yanzu ya gano dalilin daya sa Haajar take share shi da kuma rashin zuwan Hajj Jamil, tabbas akan abunda ya faru ne ,yasan abun da d'aci ,amma ya kamata su gane ba yada lefi a ciki, shima ba'a son ranshi hakan ya faru ba, Dan shi da anbi ta tashi tun a wancan lokacin sedai idan b'arayin kashe shi zasu yi su kashe shi ,amma baze tab'a yiwa 'yar mutane fyad'e ba._

Sosai daddy ya shiga damuwa ,Dan ko kiran Hajj Jamil yayi a waya baya d'auka. Idan ma ya matsa masa da kira se dai ya turo masa message akan cewa 'yana aiki daga baya ze kira shi' kuma baze kira d'in ba. Daddy yayi ta k'ok'arin zuwa gida Neman sa a gida amma baya samun sa ,duk zuwan daze yi sedai Tukur me gadi yace masa yanzu ya fita ko ya dad'e da fita. Haka dai daddy yaci gaba da bibiyar Hajj Jamil. Gashi a Yanzu ba yada wani buri daya wuce yaga ya auri Haajar ,kuma hajj Jamil shine kad'ai Wanda ze taimaka masa ya samu auren Haajar cikin sauqi ,sedai baya tunanin hakan ze yiwu musamman da wannan abun ya faru tsakanin shi da Haajar...
Chapter 24 · 0% Book details