← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 52

Sashe 33

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba tare da ya sake cewa komai ba ,Dan shi gaba d'aya ganin abubuwan da suka faru yake kamar a mafarki. Ba tare da ya sake furta kalma d'aya ba hajj jamil ya rufe taron da addu'a. Hajiya ma addu'a tayi musu sosai na samun zaman lafiya mai d'aure wa a rayuwar auren su. A gefe d'aya kuma ta yi Haajar godia bi sa namijin k'ok'arin da tayi ,a cewar hajiya ba mace ko namiji yayi irin wannan k'ok'arin yaci a jinjina mishi. Suxee in banda kuka ba abunda take yi. Hajiya da Haajar sai aikin lallashin ta suke yi. Sai da Hajj jamil ya saka baki kafin ta sassauta kukan da take yi...

Da daddare Hajj jamil ya yo musu take away gaba d'ayan su.A ranar Hajiya tare suka kwana ,ita Haajar, auta da kuma suxee.

Bayan sati d'aya...

MUJE ZUWA💃🏻

TAKU HAR KULLUM

SIDIYA...✍️
[8/18, 9:58 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠

*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)

*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*

_BABI NA ARBA'IN DA BIYU_

*____________________________*

Bayan sati d'aya... Komai ya fara daidai ta. _GIDAN MISBAHU_ ya fara farfad'o wa daga dogon hutun da ya je na farin ciki da kwanciyar hankali. Sosai Haajar ta samu karb'uwa a wajen daddy, ta kuma ba shi had'in kai wajen gudanar da rayuwa mai inganci. Hajiyar daddy ta so ta koma ,amma Haajar ta yi ta lallashin ta akan ta hak'ura ta zauna tare da su a garin sakkwato. Ba Dan Hajiya ta so ba amma Dan dole ta hak'ura ta zauna ,saboda kwarjini da kuma k'imar Haajar da take gani ,a cewar ta kuma babu abunda Haajar zata ne ma a wajen ta ta gaza yi mata shi matuqar abun nan bai fi k'arfin ta ba. Sashen bak'i aka gyara wa Hajiya. Ita kuma Haajar aka gyara mata sashen da ke gefen sashen da hajiya ke ciki. Sosai Haajar ke kula da duk wani buqatun hajiya da ma na gidan gaba d'aya. Ko da yaushe indai daddy ya fita to dikkan su suna tare da hajiya ana hirarrakin barkwanci ,wannan yasa Haajar ta k'ara samun karb'uwa a wajen hajiya ,take kuma yi mata gata irin na uwa da 'ya ,musamman da ta samu labarin cewa mahaifiyar Haajar d'in ta rasu. Hasalima ba ta wani San dad'in uwa ba ,tun tana k'arama Allah ya yiwa mahaifiyar ta ta rasuwa. Sashen kubra da Khaltum kuwa rushe su daddy yasa akayi Dan baya son yana gani ko tuno duk wani abunda ya dangance su.

A gefe d'aya kuma yana matuqar kewar kubra. Dan duk wani abunda take yi masa ,sanyin halin shi da hak'urin shi bai sa ya manta da zamantakewar su ba ,duk da ko bai tab'a jin dad'in zama da ita ba koda na sakan d'aya. Amma duk lokacin daya kalli Suxee da Auta ,fuskar kubra yake gani k'arara a tare da su. Wannan yasa ya ka sa mantawa da ita gaba d'aya, amma Dan ta khaltum da lubabatu da ma ba zab'in ran shi bane ,Dan haka baya wani tuna cewa zamantakewa ta aure ta tab'a had'a su.

A b'angaren lubabatu kuwa ,tun lokacin da ta shiga hannun hukuma take cin bak'ar wuya. Dan safe ,rana, dare azabtar da ita suke yi har lokacin da ta amsa lefin ta. Saboda an same ta dumu-dumu da laifin kashe mijin ta Alh sambo. Alh sambo shine mijin lubabatu na farko. Mutum ne hamshak'i mai azziki, Wanda ya tara 'ya'ya tsakanin maza da mata har su goma sha tara. Bayan mahaifiyar su ta rasu ya auri lubabatu. A wannan lokacin ita kuma lubabatu bata son shi ,Dan haka Bayan an yi auren ta koma juya shi ta yadda ran ta ke so, shi kuwa ya dinga biye mata a duk yadda tace to hakan za'ayi ,saboda son da yake mata. Wata rana ta sa Allh sambo ya tattara 'ya'yan nan nashi su goma sha Tara ya kai su kotu akan ai masa farar takadda da su ,babu shi babu su shi ba uban su bane. Wannan al-amari ba kad'an ba ya d'aga wa mutane hankali ,Dan duk Wanda ya ji ma cewa yake ba'a hayyacin shi yake ba. Inda Allah ma ya taimaki 'ya'yan ba yara bane. Daga chairman na lokal gobmen se 'yan kasuwa da sauran su. Autar cikin su itace sa'ar lubabatun wannan ze tabbatar wa mai karatu Alh sambo dattijo ne mai tarin 'ya'ya da jikoki. Bayan wannan al-amari ya faru kwatam wata rana aka wayi gari lubabatu ta kashe zuba wa Alh sambo guba a fura ya sha ya mutu, ta kuma tattara dukiyar shi gaba d'aya ta gudu, bata tsaya ko ina ba sai k'asar Ghana...

Wannan Abu shi ne sanadiyyar daya haddasawa mahaifin lubabatu ciwon sashe ,Wanda har sai da ya zama ajalin shi. Mahaifiyar ta kuwa bak'in ciki ya sa ta tattara kayan ta tabar k'asar. Duk irin abubuwan da suka yi ta faruwa lubabatu ba ta sake waiwayo gida ba sama da shekaru goma. A can k'asar Ghana ta sake yin wani aure ,inda ta auri wani bawan Allah mai suna malam Alasan. Ko da aure shi yana da matar shi d'aya mai suna Wasila da 'ya'yan su bakwai. Wata rana 'yar hatsaniya ta had'u da malam Alasan. Lubabatu ta faki dare dama ranar girkin ta ne ,ta kwankwantse masa Al'aura, ta haura ta bar k'asar. Daga nan ta dad'e ba ta sake waiwayo gidan Nigeria ba ,sai bayan wani lokaci ta dawo kano da zama. Inda take zaune tare da wasu dattijawa ,bayan k'aryar da ta shata musu na cewa ta yi hatsari ne ta manta komai na rayuwar ta. Tun da suka ji haka suka rik'i lubabatu tamkar 'yar da suka Haifa ,da ma ba suba haihuwa ba. Daga wannan lokacin lubabatu ta zama tamkar 'ya a wurin wa'yannan bawan Allah. Inda anan ne Hajiya Gwaggo ta gan ta taji kuma ta kwanta mata ,har ta yi sha'awar ta had'a auren su Daddy.

Lokacin da Hajiya khairi mahaifiyar Khaltum ta ji abun da ya faru da 'yar ta tilo, ba kad'an ba ta yi kukan bak'in ciki da nadamar irin turbar da ta d'ora 'yar ta ta akai ba ,mugun hali irin na ta ya sa mahaifin Khaltum ya ji ba zai iya ci gaba da zama da ita ba tun a wancan lokacin ya rabu da ita. Ya so ya karb'i Khaltum amma hajiya khairi ta hana shi saboda ita kad'ai ce 'yar shi a duniya k'arshe ma daya matsa kotu ta doka shi inda ta zuba kud'i aka mata farar takadda da mahaifin Khaltum akan babu shi babu Khaltum sakamakon sharrin da Hajiya khairi ta yi masa akan yana Neman ran su ne ita da 'yar ta. Tun daga wannan lokacin bai sake Neman su ba ,ya dad'e yana jinya sakamakon abun da ya faru da kuma irin son da yake wa Hajiya khairi da 'yar shi Khaltum. Sai da dangin shi suka yi da gaske kafin ya samu abun ya fita a ran shi ,daga baya ya sake aure ,ya kuma ta ra zuri'a da wannan matar da ya sake aure. Ko so d'aya kuma Hajiya khairi bata tab'a tunanin tura Khaltum wajen mahaifin ta ba. Yanzu da wannan al-amarin ya faru Hajiya khairi ta yi nadama iya nadama ,in da ta d'ora wa kan ta laifin duk wani abun da ya faru da Khaltum a rayuwa. Lokacin da labarin wannan abun ya isa wajen dangin mahaifin Khaltum iya Allah wadai sun yi da halayen Hajiya khairi ,a gefe d'aya kuma suna tausayin Khaltum dan duk wani abunda take yi mahaifiyar ta ce ke sanya ta. A yanzu haka ita ke zaune da Khaltum a babban asibiti Wanda iya wuya ne ace Khaltum zata sake wata rayuwar a wannan duniyar. Sakamakon k'onewar da tayi ,abun har ya tab'a k'wak'walwar ta dan kusan bata iya gane waye a kan ta. Sai dai da yake rayuwar a hannun ubangiji ta ke takan yu Allah ya yi ikon shi akan ta.

Ranar da daddare Haajar da daddy suna zaune a sashen shi. Take masa magana akan ya kamata su je su gano Khaltum. Wannan batu yayi matuqar b'ata ran daddy. Ya nuna akan ba inda za su. Washe gari Haajar ta samu Hajiya ta ke fad'a mata akan ta yi wa daddy magana kan ya kamata su je su gano jikin Khaltum. Ta nuna wa hajiya akan har yanzu khaltum matar daddy ce tun da bai sake ta ba, saboda haka bai kamata ya manta da haqqin ta dake rataye a wuyan shi ba. Ba ta kuma so allah ya kama shi da wannan laigin. Jin haka yasa Hajiya ta k'ara yabawa Haajar tare da qara tabbatar da Lallai yanzu daddy ya yi aure. Hajiya ta yi wa daddy fad'a akan batun ta kuma nuna masa hakkin Khaltum dake kan shi ,sarai daddy yasan wannan aikin Haajar ne ,badan ya so ba haka ya hak'ura akan su je d'in.

Washe gari gaba d'ayan su suka shirya dan zuwa dubo Khaltum. Wanda a ranar mahaifin khaltum shi da iyalan shi suma suka zo duba khaltum d'in. Dak'yar aka bari su daddy suka shiga inda Khaltum take. Mahaifiyar ta na kan dadduma tana Neman gafarar Allah kan abubuwan da ta aikata. Lokacin da hajiya khairi ta gan su ba kad'an ba ta ji kunyar had'a ido da su. Musamman hajiya da ta yadda da ita fiye da tunanin mai karatu ,Wanda yaddar da ta yi mata ne yasa har ta yi sha'awar su had'a jini. Shine lokacin da Hajiya ta had'a auren daddy da Khaltum d'in.

Duk Wanda yaga Khaltum a wannan halin da ta take ciki a yanzu sai ya tausaya mata matuqa. Ga ta a kwance da ita da gawa ba su da banbanci ,ba um ba u'um.
Chapter 33 · 0% Book details