← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 52

Sashe 21

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*

_BABI NA ASHIRIN DA TARA_

*___________________________*

_A Daren ranar Lubabatu tayi wani mugun mafarki akan Haajar. Mafarkin da yayi masifar firgita ta ,lokacin data farko ko ba'a ce maka a tsorace ta farka ba yanayin ta ze tabbatar maka da hakan ,Dan kuwa jik'ewa tayi sharkaf da gumi kamar wacce yaje jihadi da zuciya d'aya. Abun yayi matuqar gigita ta da d'aure mata kai ,Dan wannan kusan shine karo na ukku tana munanan mafarkai akan Haajar, kwatakwata yarinyar bata gaban ta ,amma tun da ta fara mafarkin ta ta tabbatar akwai wani abun a k'asa Wanda bata San dashi ba ,tayi iya dabarar da zatayi wajen tambayar daddy game da Haajar amma ce mata yake 'yar sa ce. A wannan karon data sake tambayar shi game da ita tare da shigar d k'orafin ta akan lallai lallai sedai yasa haajar tabar gidan wanda shine karo na uku...
Cike da masifa daddy yace "So nawa zan gaya miki Haajar 'yata ce ,me yasa kika damu akan ta yarinyar da bata damu da sabgogin kiba? 'Yar Aminina ce Hajj Jamil. Daga yau se yau kuma bana so in sake jin kinyi magana akan ta,,,, maganan Haajar tabar gidan nan Dan wata biyan buqatar kanki kuma be ko taso ba ,Dan kuwa kamar yadda ko inada rai ko bana Raye Hajj Jamil nada ikon rik'e 'ya'yana ,to haka nima nake da iko akan nashi 'ya'yan. Idan kuma baka sani ba yau zan gaya miki ,ita d'in wata rashe ce daga cikin rassan gida na ,kuma bango ce daga jikin katangar gida na ,saboda haka ki iya bakin ki akanta ,ki kuma sake takun ki. So nawa kina bijiromun da batu akan ta ina share wa ,har takai ta kawo yau seda kika kaini qul, to kinji Ina fatar kuma zaki kiyaye..." Daddy na gama fad'a mata haka ya tashi ya fice._

_Lubabatu dake nan gumi na tsats-tsafo mata tace "Ni nasani ,nasan za'azo wajen, nasan tunda nake ta yawan mugayen mafarkai akan ta dole d'in ita wata ce amma ba zata zama 'yarka ta cikin kaba. Kuma nayi nayi tabar gidan nan amma kak'i ,k'arshe ma duk lokacin dazan maka magana akan ta se rigima ya had'a mu. To lallai MISBAHU ka d'ebo ruwan dafa kanka ,naso mu zauna lafiya amma tunda kace babban maqiyinka kenan lafiyar yanzu zan fito maka da ainahin wacece ni ,zaka San wacece lubabatu Dan iya dad'i ne kasani baka San d'aci na ba ,gaba na kake gani ba baya na ba, yau zaka tabbatar da sahun giwa ya taka na rak'umi..."_

Tana gama fad'ar hakan ta tashi daga kan gadon ,wayar ta ta nemo tare da Dan nawa D'AN QANI kira... Bugu d'aya biyu ya d'auka " Ka same ni yanzu yanzu a gida " shine kawai abunda naji lubabatu ta fad'a tare da yanke kiran...

Safa da marwa ta shiga yi a tsakar parloun, takai ta kawo tare cije hannu biyu shine kad'ai aikin da take yi. Ba ita taji sanyin rai ba har seda D'AN QANI ya kira ta ya sheda mata gashi nan ya iso ,tace ya shigo ya same ta a parlou. Ajiye wayar tayi ta fad'a wanka.

Ruwa ta sakar wa kanta daga sama har k'asa. Koda ta fito a bakin gado taga daddy yana duba wasu takaddu. A zato na ko zata firgita na shigo wada daddy wani datayi har cikin gida duk da bansan ko waye ba ,sedai bansan lubabatu ba ,a mamaki na k'arasawa tayi ta zauna tare da kauda kan ta gefe. Daddy ne yace "haba yanzu tsakani da Allah kinsan yaron nan BASHAR yazo shine kika barshi a zaune shi kad'ai ,ai da se ki bari ki bashi ko abun sha ne kafin ki shiga wanka."

"Naji"... Shine iya amsar da lubabatu taba daddy tare da zura doguwar rigar ta tabar masa d'akin. Daddy ko a jikin shi Dan inda sabo yaci ace ya saba da halin mata ,be k'ara bi ta kanta ba ,ya d'auki takaddun daze d'auka ya fice abun shi...

Maganganu sosai Lubabatu ta tattauna da Wanda daddy kira da BASHAR ,sun kusa awa uku suna magana kafin daga baya ta rako sa suka fito haraba ze tafi...

A lokacin da lubabatu suka fito ,su Haajar na garden dama fakon ta suke yi Dan akwai abunda zasu yi...

Haseena ce tace " shi kuma wancan waye? Dan ni kwatakwata gayen be mun ba, sannan wannan shine gani na uku Dana masa a gidan nan suna fitowa tare da waccan matar ,ranar ma tare da daddy suka fito su uku har kud'i naga ya bashi"...

Suxee tace "gaskiya bansan shiba ,Dan ni yau na fara ganin sa ,dukda nima be kwanta mun ba ,amma yana da kyau mu dinga kyautatawa mutum zato"...

"Wannan haka yake" cewar Haajar ,ta fad'a dukda itama wani b'angare na zuciyar ta na sak'a mata ba dad'i game da gayen...

"Koma dai menene zan binciki me gadi game dashi idan suka fita. Ku kuje kuyi abunda zaku yi ni zan tsaya anan in kula da komai" inji haseena Dan gaba d'aya ta fisu zafin nama...

Ba musu haajar da suxee suka koma ciki da sauri ,Suxee ce ta shiga ta d'auko wani bokiti me marfi ,ta k'araso inda Haajar ke tsaye tana jiran ta. Gaba d'aya daka gan su kai kaga tafiyar marasa gaskiya ,dan kuwa Tafiya suke suna waigen bayan su ,a haka har suka k'arasa ta baya ,mahad'in tankin dake kai ruwa band'akin daddy yake.

Da sauri Haajar ta bud'e tankin tare da zura tiyo ta ciki ruwan ya dinga kwaranya cikin fulawowin sashen, manufar su shine su rage ruwan kafin su zuba ruwan maganin dake d'auke a bokiti me marfin da suka zo dashi.

Allah Allah suke ruwan ya gama raguwa ,amma ina saboda ruwan Nada d'an yawa ,dukda cewa na band'akin daddy kad'ai ne amma masu aikin kula da ruwan se sun tabbatar dasun cika tankin kafin suke kashe ruwan...

Duk dad'ewar da lubabatu tayi a waje tana magana da wannan gayen su Haajar basu samu damar kammala abunda suke ba, Dan iya kwance marfin tankin ma wani aiki ne me zaman kanshi ,dak'yar Haajar tayi nasaran kwanto shi shima da taimakon suxee...

Gashi har lubabatu ta shigo cikin gida. Tafiya take zuciyar ta na mata sak'e-sak'e iri daban daban, a haka har takai sashen daddy zata shiga...

Marfin tankin dake hannun suxee ne ya fad'o k'asa a bisa kuskure tare da gangaro wa har inda me tahowa ze iya hango shi.

Da sauri Suxee taso ta d'auko amma Haajar ta janyo ta tare da rufe mata baki ,sannan ta mata rad'a a kunne cewar tana jin alamar kamar akwai wani a wajen...

Mamaki ne ya kama lubabatu ta yadda akayi marfin tanki ya fad'o bayan a datse yake, gashi ta duba ba iska ake yi ba balle ko ace iske ne ya yaddo shi, kai iskan ma se me k'arfi ne kad'ai zeyi nasarar yaddo da wannan marfin ,Dan ba wawan d'auri aka asa ba... "Kai sedai idan wani ne a wurin" Lubabatu ta fad'a ,tare da nufar wurin cikin takun ta na k'asaita.

Har ta isa wajen ta zuk'unna zata d'auka... Wanda kuma zata iya nasarar hango su Haajar dake lab'e a bayan tankin ,duk sun sun tsorata ,fatar su shine kada Allah yaba lubabatu damar ganin su ko kuma Allah ya kawo musu wani d'aukin daga gefe ,Dan kuwa idan ta gansu wani sabon shafin dramma za'a bud'e, gashi basu zuba ruwan maganin da suke ta k'ok'arin zuba wa ba....

_Kuyi hak'uri da wannan jikin ne nawa har yanzu be ida warware ba. Nagode sa Addu'o'inku Allah yabar zumunci_

MUJE ZUWA💃

TAKU HAR KULLUM

SIDIYA...✍️
[8/6, 7:00 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠

*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)

*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*

_BABI NA TALATIN_

*_____________________*

Abunda ke d'auke a bokitin dasu Haajar ke d'auke dashi ruwan magani ne da Haajar ta had'a na K'AIK'AYI KOMA KAN MASHEK'IYA DA FARFATSIN MAK'ARE... Wanda keda matuqar muhimmanci ta tasiri ga duk Wanda ake tunanin akwai sihiri a jikin shi ,hassada ko Abu me kama da wannan.

Ga yadda yake;

HANYA MAFI SAUKI TA WARWARE SIHIRI KO KARYA SAMMU KO JIFA KO RUGUJE TASIRIN MAHASSADA DA MASHARRANTA DA MAQIYA
*_____________________________*

A nemi:
- Kaikayi Koma kan mashekiya
- Farfatsin Mak'era

Kaikayi Koma kan mashekiya Ciyawace ana samunta a gun yan ganye ko masu sai da ganyayyaki na magungunan gargajiya .
Farfatsin makera
Ana samunsa ne shi kuma a makera. In aka ce Farfatsin makera shine lokacin da aka saka karfe a wuta yayi Jah, Yayin da ake dukansa domin mayar dashi wani Abu toh a lokacin da ake dukansa yana fitar da wani B'awo-b'awo fari, toh Wannan sabon b'awon shine Farfatsin makera, shi Farfatsin makera ba baki bane fari ne, kuma Bashi da Karfi Sosai, kuma ba baki bane farine Kamar dalma, amma banda Farfatsin dalmar tukunyar karfe... Farfatsin makera na Asalin bakin karfe.

A hada wadannan abubuwa Guda biyu waje daya a dakesu su dawo gari, adadinsu Ya zama daya, sai a zuba a cikin wani bokiti ko roba ko mazubi me kyau, sai a zuba ruwa a ciki, sai a barshi Ya kwana, washe gari sai a tofa suratul tafiha k'afa bakwai a ciki, a dinga sha da tafin hannun dama sau uku, sai kuma a yi wanka, haka za a dinga yi na kwana uku ko kwanaki bakwai a jere ba a tsallakewa.
Chapter 21 · 0% Book details