← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 52

Sashe 36

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama d'auke a bakunan su suka shiga parlour-n. Mutanen dake ciki suka amsa musu da "Wa'alaikumusallamu". Tun daga nisa Barr ke sakar wa Suxee murmushin qauna. Ita ma bata b'oye farin cikin ta na ganin shi ba. Da haka har suka k'araso suka zauna. Haajar tace " Lah Abbu sameer! Yaushe ka zo?" Hajiya tace "wa? Wai Jamilu? Ai ya dad'e anan muna ta hira abun mu". Haajar tace " shine baka kira mu munzo anyi da mu ba" Haajar ta fad'a cike da tsokana. Yace "Wa ke nan 'yan nan? Wannan hira ai ta girme ki ,Dan ta manya ce. D'a na ganawa da uwar shi, wa ya gayyato bare kuma?" Zaro ido Haajar d'in ta yi tare da cewa "Cabdi jam! Wai ma bare. To Allah yasan yanzu na fika fawa a wajen Hajiya." Hajj Jamil yace "haba wa yarinya ,tukunna dai. Sai dai ki fi daddy amma ba ni ba" cike da raha Haajar ta koma kan kujerar da Hajiyan ke zaune tana ta famar yi musu dariya ta maqalqale Hajiya tare da shagwab'ewa tana fad'in "wai Hajiya ta kin ji ya fi ni fawa?" Hajiya na dariya tace "k'yale shi 'ya ta ,yanzu kuma ai ke ce sarauniyar fadar sauran kuma sai dai su zo a fadawan ki". Cike da jin dad'i Haajar ta sake rumgume Hajiya tana fad'in " dakyau Hajiya ta. Allah ya qara lafiya da Nisan kwana. Ka dai ji ko Abbu sameer?" Hajj Jamil yace "ke Dan uban ki ni ki sake mana tsohuwar mu. Ji yadda ki ka maqalqale mana ita kamar za'a mai da ki ciki" Haajar sake mannewa Hajiya tayi. Hajj Jamil yace "au ba da Hausa nake magana ba". Ta sowa yake shirin yi yayo kanta, Hajiya tace " A'ah haba Jamilu. Ya zaka zo har gidan 'ya ta kana Neman ka takura mata? To ka fita mun a ido kaji na gaya maka. Idan ba haka kuma ka tashi ka tafi mun gode da ziyarar, da ma ai ka canza sheqa. Ina jin ma yau ma makuwa ka yi ba nan kaso zuwa ba". Dariya Haajar ta dinga yi wa hajj Jamil hadda su gwalo. Hajj Jamil yace "gaskiya sai na yi da gaske ,Dan baze yiwu ace wannan yarinyar mai kama da maqota na Neman k'wace mun fada ba". Hajiya tace " to sai ka bada himma". Dikkan su dake parlourn sai dariya suke musu. Sai a lokacin Haajar suka gaisa da Barr. Suxee kuma ta gaida hajj Jamil. Suna cikin haka daddy ya shigo. Ganin duk yadda suke raha yasa yace "Yau kuma wani albishir Ku ka samu ne haka?" Hajj yace "Ina fa albishir. Matar ka na Neman ta k'wace min fada a wurin Hajiya kuma bata isa ba." Daddy yace "yo isa kuma na nawa. Ni kaina nan inajin ka kusa jin ance Hajiya ta zane ni da bulala akan Haajar". Hajj Jamil yace " kace kai ma ba barin ka ta yi ba?" Daddy na dariya yace "Ai kuma sai kayi. Gata nan ka tambaye ta". Hajiya tace " kwayi kwa gaji Ku bari. 'Ya ta kuma li'ilafi quraishun." Hajj Jamil yace "lah! Ka ji Hajiya na Nema ta yi mana baki". Dikkan su suka saka dariya. Har kusan goma na dare su na nan su na ta shan hira cikin raha abun gwanin sha'awa ,Dan idan ka gan su a yadda su ke zaune ba zaka ce ba 'ya'yan Hajiya bane su.

Daddy ne ya fara miqewa yace shi dai zai shige Dan ya fara jin bacci. Da haka ya yi musu sallama ya yi ficewar shi. Matar shi na ganin haka itama ta miqe ta bi bayan shi. Ya rage daga Hajiya, Suxee, hajj Jamil sai kuma Barr, Dan auta ta dad'e da yin bacci tun shigowar hajj Jamil. Barr yau d'in gaba d'aya ji yake an takura masa ,ga shi dare ya yi amma bai samu damar ganawa da masoyiyar sa ba. Ganin lokacin tafiyar shi ya kusa ,kuma matuqar ba shi ne ya kira suxee ba yasan ba zuwa za ta yi ba. Miqewa ya yi tare da cewa " Hajiya ni ma fa jirgi na zai d'aga. Dan na fara jin bacci". Hajiya tace "gaskiya kam ya kamata kaje ka d'an huta. " sai da safe ya yi musu tare da miqewa hajj Jamil hannu suka yi saida safe. Sannan ya dubi suxee da ke zaune kamar babu ita a wajen yace "biyo ni ki amso wa Auta chocolate d'in da na siyo mata, da safe ki ba ta. Saura kuma ki sha mata Abu". Murmushi kawai suxee ta yi Dan ta San mai hakan ke nufi. Shi ya fara yin gaba sannan ta bi bayan shi sad'af-sad'af... Hajj Jamil sai bin su yake da ido ,Dan tun lokacin da Barr ya zo ,har ya kira suxee a waya ,ba jimawa sai ga ta tazo duk idon shi na kai. Ya kauda kai ne kawai ya yi kamar bai Su na yi ba. Gaba d'aya ya kasa samun sukuni Dan haka shi ma ya yi wa Hajiya saida safe ya fito. Waige waige ya shiga yi yaga ta inda zai hango su kamar ance ya waiga hagun shi ,ya hango Suxee a zaune cikin motar Barr mazaunin driver, ta sako qafafun ta a waje ,yayin da shi kuma Barr ke tsaye ya rik'e marfin k'ofar da suxee ke zaune. Kai da ka hango kasan suna cikin farin ciki da jin dad'in hirar su.

Ran hajj Jamil ne ya b'aci over. Wani irin haushi da takaici ya tokare masa maqoshi. Tunanin yadda zai b'ata musu wannan zaman ya fara yi. K'arasawa ya yi har inda suke tsaye. Suxee na ganin shi ta miqe da sauri tare da duqar da kanta k'asa. Barr yace "Ah kai ma ka fito kenan?" Hajj da yake jin kamar zai yi aman zuciya yace "Eh wallahi." Barr yace "To Allah ya ba mu alkhairi" wani baqin cikin ne ya qara taruwa ya tsaya masa a qahon zuci. Kamar kar yace komai sai kuma yace "Dama cewa na yi ko za ka d'an ajiye ni idan ba damuwa. Motar tawa ce tad'an samu matsala dak'yar na samu na qaraso nan yau. Sai gobe zan turo bakanike yazo ya duba". Ba tare da Barr ya kawo komai a ransa ba yace " To ba damuwa". Sannan ya maida duban shi wurin suxee yace "muje in raka ki ciki'". Ba musu ta shige gaba shi kuma yana biye da ita a baya a haka har sai da ya kaita k'ofar sashen Hajiya da ya San shiga kawai zata yi yace " saida safe ko?" Tace "Allah ya kaimu". Kiss ya yi a tafin hannun shi tare da aikata mata. Da sauri suxee ta shige ciki cike da jin kunya.

Duk abun nan da suke Hajj Jamil na kallon su ba tare da sun Sani ba. Ran shi yayi qololuwan b'aci. Dan ko da Barr ya aje shi ko godia bai iya masa ba. Kawai shigewar sa ya yi gida...

Daren ranar Haajar ta yi wani mummanan mafarki akan Kubra. Wai ga su nan a jeji tana gudu kubra na bin ta da gudu da wani mummunan siffa. Addu'o'i ta dinga jerowa sai kalan Wanda ta manta, daga haka Kubran ta b'ace bata sake bin ta ba.

Wannan mafarki ya yi matuqar firgita Kubra. Daddy da ke kwance a kusa da ita da sauri ya tashi yana k'ok'arin kunna wutar d'akin. A firgice Haajar ta farka ,duk ta yi zufa. Tsanan tashin hankalin da ta shiga ya haifar mata da gocewar jini.

A Daren daddy ya kaita asibiti ba tare da ya gayawa kowa ba. Sai dai kafin ma su kai asibitin Allah ya yi na shi ikon ,Dan kuwa cikin da ke jikin Haajar ya zube...

MUJE ZUWA💃

TAKU HAR KULLUM

SIDIYA...✍️
[8/23, 6:58 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠

*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)

*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*

_BABI NA ARBA'IN DA BIYAR_

*____________________________*

Wannan al-amari bai yiwa daddy dad'i ba ko kad'an ,dan kusan har ya fi Haajar d'in damuwa. Yadda daddy ya shiga tashin hankali kai idan ka gani za ka d'auka wannan shine karo na farko da za'a yi masa haihuwa, badan komai ba Sai saboda tsananin Kaunar da yake yi wa Haajar d'in. Haajar ta sha wahala sosai. Ta zubarda jini matuqa ,wannan ne yasa aka buqaci da dole Sai an yi Mata k'arin jini, banda wankin Mara da aka yi mata. Jinin daddy aka iba aka sa ma ta. Hajiya ce ta koma asibitin tana kula da ita ,kwanan su hud'u ta ji sauqi Alhamdulillahi ,aka sallame su suka dawo gida. Mutanen azziki Sai zuwa yi mata sannu suke yi. Hajj jamil ma ya zo gaishe ta ,bayan sun samu sarari ne Haajar ke fad'a masa irin mafarkin da ya yi. Ya jima yana jimanta abun kafin ya yi Mata addu'an Allah ya tsare gaba ,yace kuma ta qara dagewa da addu'o'i. Bayan hajj jamil ya koma gidan shi ya kira yayan shi mahaifin Haajar ya shaida masa abubuwan da suke faruwa ,Sai dai an yi rashin sa'a mahaifin Haajar d'in baya qasar gaba d'aya yaje taron qaddamar da wata gidauniya ta taimakawa nakasassu kan harkan lafiya. Ya kuma shaida masa zai d'an d'auki lokaci a can d'in ,a qalla wata biyar ko shida. Hajj jamil bai ji dad'i ba ,Dan yasan da ace yayan na shi na qasar ,to shakka babu zai bada gudunmawar shi ,musamman da Allah ya yi shi mai tarin baiwa da hikimomi iri daban-daban. Ya na da k'warewa akan duk wata harka na jinnu da sauran su. Wannan ne yasa hajj jamil ya haqura ya bari har Sai ya dawo. Dan babu abunda za su iya babu shi.
Chapter 36 · 0% Book details