Sashe 32
Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haajar ta fara da cewa " daddy nasan za ka yi mamakin yadda aka yi na samu wannan akwatin? To ba abun mamaki bane ,ba kuma tantama wannan akwatin dukiyar ka ne Allah ya dawo maka da shi Wanda babu abunda ya samu matsala. Sai zan so Ku saurare ni Dan jin a inda na samo da kuma yadda aka yi na samu akwatin". Kowa natsuwa ya yi yana sauraron haajar. Wani ajiyan zuciya ta sauke kafin ta shiga ba su labari Tun daga lokacin da lubabatu ta turo musu 'yan fashi da makami akan azo aci zarafin su... Shirin ta akan sace akwatin dukiyar daddy da ta yi sannan ta k'ona d'akin saboda ta kauda hankalin kowa,,, da yadda ita haajar d'in ta wargaza wa lubabatu shiri ta hanyar canza akwatin da wasu takaddun na bugi,,, ta d'ora da cewa "Tun lokacin da marigayiya Haseena ta gaya mun cewa ba ta yadda da wannnan mutumin dake zuwa gidan nan a matsayin k'anin lubabatu ba ,na sanya ido akan su ,na ke kuma kula da shige da fitan su. Na dinga bibiyar ta ,har lokacin da suka shirya sace maka dukiya. A wannan Daren ta d'auki akwatin ta kai gidan gona ,ta yi rami mai zurfi ta saka a ciki ,ba tare da tunanin me ze ya dawo ba. Bayan tabar wurin na b'atar mata da hankali ta hanyar musaya akwatin da irin sa. A washe gari ta kunna wuta a d'akin sannan ta fito tana kururuwar a taimake ta. Wannan ta Ku da ta yi yasa tayi wasa da hankulan mu. Gobarar da ta sake tashi a b'angaren kubra ma duk ita ce ta haddsa shi. Saboda ta ji duk irin sab'anin da Khaltum da Kshri suka sa mu a lokacin da kubra ta je sashen khaltum suna maida wa juna magana..." Nan Haajar ta zayyana musu duk irin abun da ta ji na sab'anin da su kubra su ka sa mu ,Tun daga zuwan su Germany har dawowar su. Daga nan ta ci gaba da cewa "Bayan Khaltum ta ji komai ,daga wannan lokacin sai ta fara tunanin duk wata hanya da zata bi Dan d'aukar fansa akan kubra. A nan lubabatu ta yi amfani da damar ta ,ta zuba wa khaltum magani a abun sha ta kai mata ,sannan ta zayyana mata duk yadda zata yi Dan d'aukar fansa. Idon khaltum ya rufe a wannan lokacin saboda haka sai ta yi tunanin ko lubabatu na so ta taimaka mata ne ,ba tare da ta yi shawara da kowa ba ta je ta aiwatar da duk yadda lubabatu ta tsara. Dalilin faruwar gobar na biyu kenan, Wanda yaci rayuka ,amma khaltum ba ta mutu ba a yanzu haka tana babban asibiti ana kula da ita. A ranar da gobar zata shi, ba nida lafiya daddy yace in shirya ya kai ni asibiti. Allah ya jiqan haseena ita ta fara shiga band'aki ta ga ruwan famfun baya zuwa ,da ta gayamun sai na fito na zagaya ta baya da niyyar in duba. Bayan na duba ruwan zan koma ciki. A ta wajen ajiye motoci naga wannan mutumin da lubabatu ke kira da qanin ta ,ya karb'a k'yallen da baba lawan ke goge mota sannan ya aike shi ,bayan baba lawan ya tafi aiken da a yi masa. Se da ya waiga ya ga ba Wanda ke ganin sa ,ya zuqunna ya sacce d'an bakin wannan motar da baba lawan ke gogewa da alama yasan da ita za'a fita, ya na gama wa ya yi wa lubabatu waya ta fito ,duk ina tsaye da baya ba tare da sun ganni ba, bansan dai me suka tattauna ba amma na ga ta bashi wani envelop da alama kud'i ne a ciki ,daga nan kowannen su ya kama gaban shi. Ita ta koma ciki shi kuma yayi tafiyar shi. Yana fita na yiwa 'yan sanda waya tare da yi musu kwatancen shi suka kama shi da kuma abunda take k'ok'arin aikatawa suka ka ma shi. Da mu ka fito za mu fita ,na cewa daddy kar mu shiga wannan motar mu shiga d'ayan. Ya yi mamaki ,ya tambaye ni ko lafiya ,nace masa lafiya qalau kawai dai sanyin A/c nne ba na so. Duk da ba wata hujja na ba da ba daddy ya biye min a tunanin shi ko duk zafin zazzab'in ne. A wannan ranar shirin lubabatu na k'arshe shi ne ta salwantar da rayukan mu gaba d'aya. A d'ayan b'angaren kuma ga gobarar da za ta tashi za'a yi marus ,a wayi gari ba kowa a gidan sai ita. Daga nan ta shirya 'yar k'aramar wasa na akan idan komai ya wakana kamar yadda ta tsara ,za ta yi haukar k'arya Wanda mutane za su yi tunanin ko duk iftila'in da ya faru ne ya tab'a mata k'wak'wal. Da ga nan bayan ta warke komai na daddy zai zama na mallakin ta."... Kowa da ke wajen kusan daskarewa ya yi Dan jin wannan al-ajabi. "Abu sai kace shirin film cewar Hajiya...
Ta ku Haajar ta yi har inda lubabatu ke tsaye rik'e a hannun matakan tsaro tace "Wannan wasar ya k'are daga yau. Cin mutuncin da kike ganin kin mun kuma dama a wurin ki yake haka. A zahiri kuma ni matar daddy kamar yadda kike matar shi ,a yanzu haka kuma ina d'auke da cikin shi sanadiyyar abun da ya faru. Ke kuwa kina ji kina gani za'a fitar da ke daga cikin gidan nan, ba ma cikin gidan daddy kadai ba hatta rayuwar shi kin fita kenan fitar da babu dawowa har abada da yaddar Allah..." Mai da duban ta tayi gun Barr tace "za Ku iya tafi da ita. Idan wancan case din ba bamu da masaniya akai tuhuma ce to ga Wanda kuke da tabbaci akai".
Ihu lubabatu ta shiga kurmawa ba qaqqautawa ,tana fadin " Wallahi sharri take mun ban aikata ba ,wannan kawai an hada ne Dan a rabani da mijina saboda anga yana so na.
Barr dake tsaye yace "wancan ma ba tuhuma bane ,saboda yanzu mun kai shekara goma muna cigiyar ta Allah be sa mun gan ta ba sai yau. Muna kuma da izinin kamata mu danqa ta hannun hukuma duk lokacin da muka yi ido hudu da ita. Zamu tafi ita, idan komai ya daidaita zan dawo Ku ji komai". Barr yace wa matakan tsaro Ku tafi da ita.
Ihu lubabatu ke yi tana fadin " Ku taimake in. Na shiga uku tun ban mutu ba ga matambaya sun iso min. Alhaji kana gani za'a tafi dani ka yi musu magana kar ka bari su tafi dani". Jin zata Tara musu jama'a yasa su ka rufe mata baki da wani k'yalle tare da ficewa da ita...
Suxee da hajiya sai kuka su ke yi. Suxee na kukan rashin 'yar uwar ta haseena da baqin cikin irin mutuwar da tayi. A b'angare daya kuma tana takaicin irin turbar da mahaifiyar su ta mutu a kai. Gaba daya tausayin kan su ya kama ta a lokaci daya taji son Haajar ya qara shigar ta. Hajiya ita ma kukan rashin jikar ta take ,da tausayin d'an ta irin jarabtar da Allah ya yi masa na mata ,ace mata uku babu ta Allah a cikin su. Da badan Allah ya kawo musu Haajar a rayuwar su ba da yanzu labari ya sauya. Duk da wannan shi ne karo na farko da hajiya ta ga Haajar ba k'aramin kwanta mata ta yi ba ,musamman yanzu da ta ji irin tarin alkhairan da ta yi a d'an zaman ta a gidan yasa ta ji ta a ran ta fiye da yadda ya ji son ta a farko.
Hajj Jamil dake gefe mamakin duniya ya hana shi magana. Duk wani abunda Haajar ke yi tana sanar mishi amma Sam ba yada masaniya akan abubuwan da ta zayyana a yanzu. "wato Haajar ta wuce duk yadda nake tunani?"" Ya fad'a a k'asan ran shi ,a fili kuma ajiyan zuciya ya sauke tare da cewa "Godia ya kama ta mu yi wa Allah ,ga me faruwar wa'yannan abubuwa. Abunda ya faru ya riga ya faru ba ma fatar makamancin wannan ya sake faruwa ,sai dai mu ce Allah ya tsare gaba ya kuma k'ara tsare mana imanin mu... Zuwa yanzu komai ya faru ya wuce ,mun ji komai. Abu daya da ya rage shine misbahu in gabatar maka da Haajar a matsayin matar ka. Tun lokacin da ka kwanta a asibiti ,na fad'a mata komai a kan ka saboda yadda naga ta damu dakai, ta kuma amince akan tana son ka zata aure ka. Daga wannan lokacin naje na nema maka auren ta a wajen mahaifin ta yaya na Dr. Sheikh Imam Ali asadussunnah, ya kuma amince da duk baya nan dana Je masa da shi. Ban baro jigawa ba sai da aka d'aura auren ka da ita. Tun lokacin Haajar ta dawo gidan nan da zama ,ta zo ne a matsayin matar ka. Kuma ita ta buqaci da a b'oye maka har zuwa wani lokaci saboda a samu daidaito, saboda kuma ka nemi soyayyar ta da kan ka ,ba Dan wani ko wata ya had'a Ku ba. Kamar yadda ka ji ta fad'a a yanzu cewa tana da juna biyu ,haka zancen yake.
Duk abunda ya faru bana qasa a guiwa wajen sanar da hajiya. Tasan komai akan auren ka da Haajar, Dan har ma na tab'a had'a su a waya suka gaisa. Ko ba haka ba hajiya?"
Hajiya ta amsa da "wannan haka yake"
Daddy da tsoron Allah ya taru ya tsaya masa a zuci ,mamaki ,tsoro da alajabi ne ya hana shi furta ko da kalma daya. Jinjina kai ya shiga yi a hankali ya furta "Ikon Allah"...