Sashe 6
Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kyau iya kyau daddy kyaky-kyawan gaske ne ,duk macen data kalle shi babu kissa tasan ya had'u ,ya kuma cika duk wani sharud'd'a da tsari na jarumin namiji tsaye dakyau zaune dakyau. Wata bugaggiyar gizna Shadda ce sanye a jikin shi kalar ruwan ganye ,Wanda taji aikin wuta daga tsakiya ,d'inkin two buttons ne tazarce ,hular kanshi kalar shaddar dake jikin shice ,me ratsen brown daga tsakiya ,ba kad'an ba shigar ta amshi jikin shi. Agogon hannu ya d'aura bak'i a tsintsiyar hannun shi na hagu ,sannan ta taje sajen da ke zagaye da fuskar shi Wanda ya had'e da d'an madaidaicin gemun shi bak'i sid'if. Gilashin idon shi se yayi kala da hadarin damuna, takalmin k'afar shi black cover ne Wanda yaji Polish me walk'iya, a tak'aice dai Wanka yabi jiki musamman gashi fari , faffad'a ga tsawo ga zati...
Gaban madubin bedroom d'in shi ya tsaye ,yana feshe jikin shi da turaruka masu matuqar k'amshi da tsada. Wallet d'in shi da wayoyin shi ya kwasa tare da saka wa a aljihu. Murd'o k'ofar d'akin da akayi yasa ya maida duban shi gun k'ofar Dan ganin waye me shigo wa...
Kubra ya gani ,tun daga nisa ya fara sakar mata murmushi, itama maida mishi tayi ,Dan ba kad'an ba taji yayi masifar burge ta... Gaishe shi tayi kamar da gaske ,ya amsa mata fuskar shi a sake ,tare da tambayar yadda ta kwana.
"Daddy wannan kyalliyar haka se ina kuma?" Kubra ta tambaye shi kamar bata masa bin k'wak'waf.
Murmushi Daddy yayi tare da cewa
"Kaji ki wai kwalliya, ina wani kwalliya anan? Tafiya fama zanyi zuwa kano, Hajiya Gwaggo ce ke nema na, so I think ma k'ila inyi kwana d'aya ko biyu"...
" Dama ka dena wahalar da kan ka da yimun bayani ,babu wani Abu da zakayi Wanda bansani ba dahar nake Neman k'arin bayani" kubra ta furta aranta ,a fili kuma tace
"Ohkkk! Anyway! Ni daman kud'in hannuna ne ya k'are shiyasa nace bari inji ko zan samu chicken change a wajen ka" ,ta fad'a cike da gadara ,kamar irin ta bashi ajiyar nan.
Ajiyar zuciya daddy ya sauke ,sannan yace
"Ba damuwa zan miki transfer".
" OK to" shine amsar da kubra ta bashi sannan tayi ficewar ta.
Shima daddy be wani b'ata lokaci ba sanin da yayi su suxee nacan na jiran shi suyi breakfast, gashi flight d'in k'arfe sha d'aya na safe ze bi. Sashen kubra ya nufa , ta parloun k'asa yabi ,koda ya shiga a zazzaune ya same su , alamar shi suke jira. Tun kafin ya k'araso yake annashuwan ganin su ,suma cikin tsananin k'auna suka gaishe shi ,fuska a sake ya amsa ,sannan ya samu guri ya zauna , cikin farin ciki suka cin abincin su ,bayan sun gama yake sanar dasu tafiyar daze yi ,Addu'a sosai yaran suka mishi ,yaji dad'i har cikin ranshi.
A tare suka nufi sashen shi ya d'auko jakar shi ,sannan suka fito zuwa parking space ,rakiya suka masa har airport ,seda jirgin shi ya tashi sannan driver ya dawo dasu gida.
A garden suka yada zango har Auta se hira sauke abun su gwanin sha'awa ,suna nan suka hango wuce war motan kubra. Tab'e baki Haseena tayi ,a ranta tace "kifi jirgi gudu ,ruwa izo hadda matuk'a jirgi" a fili kuma tace
"Duba kiga mummy Yaya suxee daddy na fita itama ta fice"
Murmushin takaici suxee tayi tare da cewa
"Hmm Haseena kenan! To Allah na tuba mummy ko daddy na nan tana fasa fita ne? Ai sema abunda yayi gaba. Ki duba lokacin dayayi rashin lafiyan hawan jini ,kamar daddy baze yi rai ba ,amma a ranar me kika ga tayi ,Dubai fa ta wuce wajen birthday d'in k'awarta, kuma ita ta shirya komai. Tunda mummy bata zauna a wancan lokacin da daddy yafi buqatar taba ,to banga dalilin daze sata ta zauna ba"...
" hakane kuma fa! Allah dai ya kyauta " haseena ta fad'a cike da takaici...
Suna nan suna hira, khaltum ta fito kamar wata gigitacciya ,se waige waige take kamar me Neman wani Abu...
Kamar ance ta duba ta garden ta hango su suxee zaune kan lilo ,da gudu ta k'araso wajen tana tambayar daddy fa? A lokacin suxee waya take yi dan haka bata lura da ita ba, Haseena kuma yi tayi kamar bata ma San da ita ba
"Ba tambayar Ku nake ba? Ina ubqn Ku? " cike da mamaki suxee tace
"Haba Anty Amarya, ina uban mu kuma? Ina lefin kice mana ina daddy? To bayanan yayi tafiya"
Wani gigitaccen mari suxee taji khaltum ta d'auke ta dashi. Aiko kamar daga sama ,itama khaltum d'in taji an wanke ta da mari...A hasale haseena ta furta
"Ke har kin isa?"...
Tofa! Jama'a Dan jin meke shirin kunno kai ,se kuci gaba da bibiyar wannan k'ayataccen labarin...
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[7/17, 7:33 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠
*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*
_BABI NA TARA_
*_____________________*
Tsabar a rud'e khaltum take bata ko bi takan Marin da haseena ta sharara mata ba. Had'a hannaye biyu tayi alamar pleading tana cewa "Dan Allah Ku gayamun ina daddyn Ku yake?"
Da mamaki suke binta da ido "na rok'e Ku Ku gayamun" khaltum ta sake maimaitawa.
"K'arya kike nufin zamu miki? To bayanan ,yanzu haka yana cikin kano" haseena ta bata amsa a d'an tsawace...
Ihu khaltum ta fasa ,da gudu ta koma cikin gida. Tana shiga d'akin ta ta fara Neman waya ,Hajiya khairi ta danna wa Kira ,daga b'angaren Hajiya khairi kuwa tana d'aga wa tambayar ta tayi "khaltum Yaya?"
"Wallahi Hajiya ban same shi ba ,na tambayi yaran shi ,sunce wai ya tafi kano ,gashi a jirgi ya tafi ,zancen Dana ke miki ma yanzu haka yana kano"... Khaltum ta fad'a cike da tashin hankali.
" Aiko an yanka ta tashi ,Dan malam ya tabbatar mun lallai duk yadda za'ayi a hana shi tafiyan nan ,idan kuwa ya tafi to labari ze sauya" cewar Hajiya khairi ,ta fad'a cike da takaici
Cikin tsananin tashin hankali khaltum tace "to yanzu Hajiya ya za'ayi kenan? Sannan me malam ya fad'a miki ze faru idan daddy yakai kano" khaltum ta tambaya
Hajiya khairi tace" gaskiya be sanar dani ba ,a iya dube duben shi kuma ,k'asa bata bashi izinin sanin meze faru ba ,amma lallai ya tabbatar mun da akwai matsala, Wanda har idan bamu yi da gaske ba ,matsalar ze iya zama sanadiyyar auren ki"
Hannu khaltum ta d'ora akai tana fad'in "na shiga uku Hajiya ,meke shirin faruwa dani?"
Cikin lallashi Hajiya khairi tace "ki kwantar da hankalin ki ,yanzu abunda nake buqata dake shine ,duk yadda za'ayi ki samo kud'i yau d'in nan ba se gobe ba ki turomin, ni kuma zan wuce Jibiya ,insakar wa malam kud'i Dan yaji dad'in baza mana aiki"...
Cikin sassark'ewar murya khaltum tace " To...to.. Shi kenan yanzu base anjima ba ,zan turo da kud'in ,Dan Allah Hajiya ayi duk wani abunda ya kamata!"
"Karki damu gudan jini ta, sena jiki".
Khaltum na ajiye wayar ,sashen Daddy ta nufa ,dube dube ta farayi ta inda zata ga kud'i, aikuwa kamar ance ta bud'e drawer ,se ga kud'i ta gani ,ta kuma yi sa'a be saka key ba ,bata wani b'ata lokaci ba ,ta fara jidan kud'in, kud'i khaltum ta iba ,ba nida kud'i ba ,Dan ko ita kanta bazata ce ga adadin abunda ta d'auka ba.
Sashen ta ta koma, ta shirya kud'in a wata madaidaiciyar jaka, sannan ta yafa mayafi ,tare da d'aukan makullin motan da daddy ya bata shekaran jiya ,A gigice taja motan ,tabar haraban gidan... Su dai su suxee ikon Allah ne ya hana su magana ,dak'yar suxee ta bud'e baki ta iya cewa
" ita kuwa Anty Amarya meke damun ta ne yau?"
"Me kuwa yake damun ta? In banda shashanci ,keda kin gani kinsan ai wata katamarmarar take k'ullawa, kuma da ikon Allah kan ta ze k'are".. Haseena ta fad'a tana wani yatsina fuska
" To Allah ya sawwaqe!" Inji suxee. Sun d'an jima suna tattauna lamarin kafin daga baya ,suka koma cikin gida.
Wuraren bayan magrib ,kubra ta dawo ,a daidai lokacin da khaltum ke shigowa itama. A tare sukayi parking ,kubra ta ce ta fara fitowa ,kafin khaltum ta bud'e marfin motar ta ,sedai bata kai ga fitowa ba.
Tsaya wa kubra tayi ta k'are wa khaltum kallo ,sannan ta wani irin fashewa da dariya ,k'arasowa kubran tayi har inda khaltum tayi parking d'in motar ta.
"Khaltum kenan" kubra ta kira sunan ta ,wanda yasa khaltum d'agowa a d'an tsorace.
Kubra tace "da zaki dena wahalar da kanki da kin sauqaqa wa rayuwar ki ki kuma hutar da zuciyar ki, ni banga abun d'aga hankali ba. Nasan duk iya k'warewar malamin ki da iya binciken shi baze tab'a gano miki meke shirin faruwa ba ,to base kin bama kanki wahala ba wajen tunanin meze faru, ni da kinyi shawara dani ma base kin yi wahalar turawa da kud'in kiba. Daddy dai kamar yadda na tab'a gaya miki ze k'ara aure kul bad'ad'e kul bajima ,to lokacin ne yazo ,aure ba fashi , ke baki isa ki hana wannan auren ba, idan kuma kinji zaki iya to ga hanya nan.
Ke duk ni fa da hatsabibanci na to wacce za'a kawo ta yaga wa tunani na. Kuma kamar yadda aka gaya miki muddin bakiyi da gaske ba ,auren ta kamar k'arewar auren kine a gidan nan.
Cikin tsananin tashin hankali khaltum ta fito a mota ,rirrik'e kubra tayi tare da fad'in
"Dan Allah kubra ki gaya mun to yanzu menene mafita? Wallahi na sadu da ,nabi Allah na biki"
Sake fashewa da wani dariyan kubra tayi tare da cewa
"Haba da wuri haka? Aina d'auka bazaki iya zubarda makaman yak'in ki cikin sauqi haka ba? Ke Nifa da nice ke ,tun farko bazan tsaya b'ata wa kaina lokaci ba ,mantawa zanyi da komai da kowa , Neman gindin zama kawai zan yi, amma da kika shigo ,se kike k'ok'arin shiga gonar daba naki ba"
Wani irin marayan kuka khaltum ta saki ,tana fad'in