Sashe 15
Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Abbu Sameer kayi k'ok'ari ka bashi yasha wannan ,ka rage kad'an ka shafe masa sauran a jiki ,tun daga tsakiyar kanshi har tafin k'afar shi. Gobe da safe ma haka ,se kayi amfani da na cikin goran, idan zan zo gobe zan zo da wani ,a k'alla a samu tsawon kwana uku ana masa haka ,da yaddan Allah koma wani irin ciwo ne ze samu waraka."
Cike dajin dad'i Hajj Jamil yasa hannu ya karb'a tare da ajiye wa a gefen sa. Haajar tace "yanzu fa zaka masa base anjima ma"
Yace "to ai kinga yanzu be farka ba ,na d'auka ko se idan ya farfad'o ne?" Girgiza kai Haajar tayi tare da cewa
"A'ah yanzu za'a yi ,ai ma ze taimaka wasa wajen farfad'owan ,shiyasa nace zamuyi kamar na kwana ukku haka ,kafin muga yadda jikin yayi".
Mik'e wa Hajj Jamil yayi ya fara k'ok'arin yin kamar yadda Haajar tace ,sedai ya kasa ma taya ze tsiyaya wa daddy ruwan a baki ,kasancewar bakin nashi a rufe yake. K'arasa wa Haajar tayi wurin gadon tana cewa
" Bari kaga in taimaka maka." Ruwan kofin ta karb'a ta rik'e sannan matse hancin Daddy. Mik'e wa Hajj Jamil ruwan tayi ,tace "kayi bismillah ka bashi."
Nan ya shiga tsiyaya wa daddy ruwan addu'an yana sha, seda taga yasha sosai ,sannan ta sake masa hanci tare sa cewa
"Ya isa haka ,ka shafe masa sauran a jiki."
D'an basu waje tayi ,saboda be halatta taga tsaraicin saba. Waje ta fita ,tace "Ina zuwa". Hajj Jamil yasan manufarta nayin haka ,murmushi kawai yayi sannan ya fara k'ok'arin shafe masa jikin sa. Tunda ya fara shafawa daddy ruwan Addu'an nan yake ta sauke ajiyan zuciya, Mamaki ne ya cika Hajj Jamil, Dan daddy yayi ajiyan zuciya kusan har so uku.
A hankali Daddy ya fara k'ok'arin bud'e idanuwan shi ,ya sauke su akan Hajj Jamil, shi kuma mamaki ne da tsoron Allah ya kama shi ,da sauri ya k'araso yana wa daddy sannu.
Daddy dake kwance ,ji yayi kamar an zare masa lakka ,ga kuma baya jin wani ciwo a tattare dashi ,se dai k'arfin jikin ne da kuzari babu.
Farkawar Daddy yayi daidai da shigowar Haajar ,Hajj Jamil yace " kinga zuwan ki ya zame mana alkhairi, gashi wallahi har ya bud'e ido"
Murmushi kawai Haajar tayi tare da cewa "Dama ze farka ,wuyar ta ayi ne dai kawai". Duban ta ta maida wurin Daddy tace " Sannu Daddy ya jikin naka?"
Murya can k'asa daddy ya amsa mata da "ALHAMDULILLAHI!"
Ta sake tambayar sa "kana jin wani Abu yanzu?"
Girgiza mata kai yayi alamar A'ah. Kallon Hajj Jamil tayi da ikon Allah ya hana shi magana tace "Abbu Sameer ,inaga ze buqaci zagawa bayan gida ,kad'an kama shi ka kaishi."
Kallon mamaki Hajj Jamil yake bin ta dashi ,yace "ta ina kuma ze iya wani zuwa toilet mutumin daya farka yanzu yanzu!"
A hankali ta lumshe matsakaitan idanuwan ta, tare da nad'e hannun ta a k'irji ,tace "ka kaishi ka gani".
Hajj Jamil be San ma'anar ta na cewa hakan ba ,amma ba yada wani zab'i daya wuce yayi yadda tace ,Dan Haajar d'in ce gaba d'aya ta rikid'e masa ,sanin daya mata Ashe ta wuce nan.
A hankali Ya taimakawa Daddy ya tashi, toilet d'in cikin d'akin ya kaishi ,a mamakin shi suna shiga kamar Daddy na jira ,wani irin fitsari jawur kamar jini ,ga yawa ,sun kusa mintuna talatin a band'aki. Ruwa daddy ya shiga antaya wa tun daga saman kanshi ,sakamakon wani zafi daya ji yana taso masa ,had'i da kuskure bakin sa ,kafin nan suka fito.
Ko kafin su fito ,Haajar ta had'a wa Daddy tea me kauri ,sedai bata saka Sikari a ciki ba. Koda suka fito ,ba lefi ya samu kuzari ba kamar yadda suka shiga ba ,Dan har tafiya yake da k'afar shi ,iya gefen shi kawai Hajj Jamil ya rik'o. Seda ya zaunar dashi ,sannan Haajar ta mik'a masa kofin tea-n.
Hankali a kwance daddy ke kurb'an shayin sa, sedai wani d'an karan zufa daya shiga anbaliya yana wanke masa tun daga fuskar shi har zuwa cikin shi ,kamar an kwara masa ruwa. Duk Sanyin dake tashi ,be hana tsufan ci gaba da tsats-tsago masa ba.
Hajj Jamil kallon Haajar yayi ,data ke tsaye ta had'a hannuwa biyu tana ta faman aikin murmushi
A sanyaye ta furta "ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN! Sauqi ya samu...
MUJE ZUWA💃
TAKU HAR KULLUM
SIDIYA...✍️
[7/27, 9:15 PM] SIDIYA...✍️: 🏠🏠 *GIDAN MISBAHU*🏠🏠
🏠🏠🏠🏠🏠🏠
🏠🏠🏠🏠
🏠🏠
🏠
*_🏠(base on true life story)_*🏠
*_🏠INTELLIGENT WRITERS ASSO📚_*
(On ward together)
*MALLAKAR:*
*SADIYA SIDI SAID (SIDIYA)✍️*
_BABI NA ASHIRIN DA UKU_
*___________________________*
_Sosai jikin Daddy ya fara warewa ,har d'an hira suke tab'a wa sama-sama, se wuraren bayan magrib Hajj Jamil ya kira driven shi yazo ya maida Haajar gida. Washe gari tun da wuri ta fara shirin koma wa asibitin dan dubo jikin Daddy, tuwan semo tayi masa da miyar kub'ewa d'anye Wanda yaji bushash-shen kifi ,se Farfesun kayan jiki daya ji kayan k'amshi, har ta kusa kammala wa ta tuno da bata d'ora ruwan zafin tea ba ,da sauri ta kunna d'an k'aramin gas d'in da ba komai akai ta d'ora tare da saka kayan k'amshi,,,, duk d'ora da saukewan nan da Haajar ke yi, ba abunda ta dafa ba tare da ta tsiyaya MA'UL WARDI (ROSE WATER) a ciki ba, musamman a ruwan shayin ,se da ta kusa juye Rabin kwalbar MA'UL WARDIN, seda ta kammala komai sannan ta gasa musu bredi Wanda yaji butter ,k'wai dafaffe da kayan miya, wannan kuma tayi ne Dan Neman sauyi ,amaimakon takai bredin gayan shi ,se tada'an masa mahad'i..._
_Cikin lokaci ta kammala komai da komai ,ta jera a kwando ,fridge d'in kitchen d'in ta bud'e tare da d'auko wani d'an madaidaicin bowl me marfi ,fruit ne a ciki ya kuwa yi sanyi. K'arfe Tara na safe ,drivern Hajj yazo yana jiran ta. Bata yi k'ok'arin tashin su suxee ba ganin suna bacci ,sedai ta ajiye musu nasu breakfast din kan dinning yadda idan suka tashi base sun wahala ba ,ci kawai zasu yi._
_Ruwa ta sake watsawa ,bata wani b'ata lokaci ba ta shirya cikin atamfa d'in kin Riga da sket Wanda yabi jikin ta, mai kawai ta Shafa se madaran turare na jiki me sanyin k'amshi, sanin data yi na Haramun ne mace ta fita tana k'amshi yasa ,bata fesa turare a kayan ta, tana k'amshi amma ba me tashi sosai d'in nan ba ,k'amshi irin se Wanda ke kusa da ita sosai ze iya jiyo shi,,, Abaya ta d'ora akan kayan tare da yin rolling da mayafin. Duk da ba wani kwalliya tayi sosai ba amma kuma tayi matuqar yin kyau. Kwandon kayan abincin ta rik'o da hannu d'aya, d'ayan hannun ta kuma tana rik'e da wayar ta._
_Kamilu na ganin ta fito da sauri ya k'araso Dan ya karb'a kayan hannun ta. Fuskar Haajar d'auke da fara'a tace_
"Lah! A'ah Allah malam kamilu dama ka barshi ,muyi sauri mu tafi dai ,lokaci na k'ure wa."
Gidan baya ta bud'e ta aje kwandon ,sannan ta bud'e gidan gaba ta shiga.
Cikin mintunan da basu gaza goma zuwa sha biyar ba ,suka isa asibitin. Tura k'ofar d'akin tayi ta shiga tare da sallama. Ba kowa a d'akin ,D'aga idon da zatayi ta hango Daddy a zaune akan sallaya ,da alama ramakon salloli yake yi ,motsin ruwan data jiyo a bayi ya tabbatar Mata da Hajj Jamil ne a ciki. Cike da farin ciki ta samu guri ta zauna ,tana d'an danna wayar ta ,a hankali kuma tana d'agowa tana duba Daddy taga ko ya idar da sallan. Hajj Jamil na fitowa ya ganta ,k'ara fad'ad'a murmushin dake fuskar shi yayi ,yana fad'in
"A'ah har kin zo kenan ?"
Tace "Allah ya nufa Abbu Sameer. An tashi lafiya?"
"Lafiya qlau, Alhamdulillah. Ya su Auta?"
Tace "lafiyan su qlau ,ai basu ma San na fito ba ,Dan bacci suke yi koda na fito ,ni kuma bana so in tashe su shiyasa".
Hajj Jamil yace " Ah hakan ma yayi kyau"
"Abbu Sameer yame jiki?" Haajar ta tambaya cike da kulawa
Yace "Alhamdulillahi Haajr ,Jiki da sauqi sosai ,gashi nan ma yana sallah. Ai ke da kin gani kin San jiki yayi kyau".
Murmushi sosai Haajar ke yi Wanda yayi sanadiyyar bayyanar fararen hak'oran ta ,tare da cewa " gaskiya kam jiki yayi kyau. Allah yasa kaffara ne" Bayan Daddy ya idar da sallah ,Haajar ta masa ya jiki ,har cikin zuciyar shi yake jin dad'in yadda take nuna damuwa akan shi da 'ya'yan shi.
Addu'a tayi masa Wanda Manzon Allah s.a.w ya koyar damu idan ka ziyarci Mara lafiya ,ka karanta:
" لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللَّهُ
Laa ba'sa tahoorun 'inshaa'Allaah.
: أَسْأَلُ اللَّهَ الْعَظِيمَ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيَكَ
'As'alullaahal-'Adheema Rabbal-'Arshil-'Adheemi 'an yashfiyaka.( k'afa bakwai)...
Daddy jin yayi Haajar ta k'ara kwanta masa arai ,komai nata cikin hankali da nutsuwa take gudanar dashi. Da kanta tayi serving d'in su ,Tas daddy ya cinye har da Neman k'ari ,ga uban santi daya ke ta zuba wa, Hajj Jamil da Haajar se dariya suke masa ,Dan Daddy badai barkwanci ba ,haka yayi ta basu dariya, se dai be jima da gaba cin abincin ba ,Se wani amai ya taso masa ,da sauri ya tashi ya nufi toilet ,har saura kad'an ya fad'i, wani irin amai bak'ik'irin ya shiga kwararawa ba girma ba azziki kamar Wanda yaci guba, ba shiri Hajj Jamil ya aje plate d'in da yake cin abinci ya tashi ze nufi toilet d'in. Haajar tace
"Abbu sameer ka bash-shi yayi aman shine samun sauk'in shi ,dama nasan dole zeyi aman saboda da MA'UL WARDI na dafa masa ruwan shayi ,kuma shi dama MA'UL WARDI haka yake ,indai kana tunanin ko an yiwa mutum sihiri ne ,zaka saka a abinci mutum yaci ,ko kuma ma kaba mutum shi zallah yasha ,tare da tofa wasu Addu'o'i karya sihiri na sirri, saboda haka karka wani tashi hankalin ka ,ka duba kaga ni idan ya gama seka taimaka masa ya wanke jikin sa.