← Book details Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 52

Sashe 50

Gidan Misbahu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nasihohi sosai Haajar ta sake yiwa Haajar kan yadda zata tafiyar da rayuwar auren ta ,musamman ta fannin shimfid'ar mijin ta ,dan abunda Haajar ta lura da shi a maganganun suxee alama ce ta Barr mai yawan buqatar mace ne ,musamman yadda ya jima be yi auren nan ba ,ga shi ta lura suxee nada raki Wanda ze iya kawo mata naqasu a zamantakewar ta da mijin ta. Fad'a tayi mata sosai ,sannan ta bata wasu abubuwan da zata yi amfani dasu , ta had'a mata ruwan magarya da sassak'en b'aure mai zafi ta zauna. So biyu tana canza mata ruwan sannan tace tayi wanka ta fito ta shirya ,lokacin wacce zata mata kwalliya ta Kira tana hanya. Masu sanya rumfar walimar kuma suna harabar gidan suna aikin su. Gyara mata ko ina Haajar tayi ,ta jera mata jayan ta a sip ,sannan duk wasu muhimman abubuwan da suxee zata buqata ta ajiye mata su a kusa-kusa kamar kayan hakin maye ,drowa d'aya ta mata. Seda akayi sallar azahar sannan me kwalliya tazo ,lokacin mutane sun fara taruwa. D'an light make-up aka yi wa suxee. Ta shirya cikin wani material purple mai kyau da tsada, tare da d'ora alkyabba akai. Bayan angama Haajar ta dube ta tare da cewa "kai masha Allah Mrs Kabir kinyi kyau sosai." Suxee tace "nagode Mrs Misbahu". Dariya suka sa. Suxee tace " to Anty Haajar kizo a miki kwalliyar mana" Haajar tace "wa ni? Ai Kema kinsan ban damu da irin kwalliyar nan ba ,nafi gane in Shafa hoda in mits-tsika mai a baki kawai ya ishe ni". Fanna mai kwalliya tace " ai kinsan su kyawawa daban suke ,kwalliya bata wani dame su ba." Dariya suka yi Haajar tace "kin dai ga kyawawan gaske nan a gaban ki" ta nuna suxee. Suxee tace "kai Anty Haajar abun hadda zolaya?" Dariya Haajar tayi tare da cewa "ai kowace mace ma kyakykyawa ce saidai idan bata samu gyara ba". Fanna tace " hakane kam". Se da suka yi sallan azahar sannan aka fara shirye-shiryen walima. Misalin k'arfe biyu na rana ancika. Malama khadija itace wacce zata gabatar da nasiha a walimar. Tana zuwa walima yakan kama. Nasihohi sosai malama khadija tayi tare da tsakuro musu wasu daga cikin magungunan da zasu iya had'a wa da kan su ba tare da sun cutata ba. Sannan tayi tsawatarwa game da wuta da aljannah. Haqiqa ta fad'akar ,kowa yaji dad'in zuwa walimar. Sai la'asar taron ya fara watsewa ,duk Wanda zai tafi kuma da tsaraba yake tafiya ,na turaren wuta, kayan snacks da abun sha Wanda Haajar ce duk tayi wannan hidimar. Bayan la'asar duk mutane sun gama watsewa sai su Haajar kad'ai suka rage. Sai da suka gyara mata duk inda aka b'ata suka baza turaren wuta. Haajar ta sake dafawa suxee ruwan sassaken b'aure ta zauna sannan tasa tayi wanka ta canza kaya ,wani had'ad'd'en gumba na aya Wanda yaji kwakwa ,da dabino Haajar ta had'a wa suxee da madara tace "maza ki kafa kai ki shanye".bayan ta shanye ta tsiyaya mata tsumi Kofi d'aya shima ta shanye ,sannan tace " ya isa haka. Karki dinga shan abubuwa ya miki yawa, Dan suna da k'arfi zaki iya buguwa idan kika cika". Suxee tace "ai naji Anty Haajar, Dan har yanzu ban dena jin shi a mak'oshi na ba." K'arfe biyar su Haajar suka yiwa suxee sallama suka koma gida...

Sai da akayi sati sannan Haajar ta dena aikawa su suxee abinci. Bayan sati d'aya aka kai hajiya gidan suxee ta wuni mata ,sai yamma daddy ya tura driver ya d'auko ta. Bayan sati biyu da zuwan hajiya suxee da Barr Kabir suka kawo ziyara gidan daddy. Kowa yayi murnan ganin su ,suxee tayi kyau abunda ya k'ara haske tayi 'yar k'iba ,haka shima Barr. Tun rana sai dare suka musu sallama suka tafi. Tun bayan biki Hajiya zaliha Matar hajj jamil bata sake komawa gidan Haajar ba ,Haajar ce ma suna hira da daddy wata rana da daddare take cewa ya kamata taje ta dubo maman sameer gobe. Washe gari da daddy zai fita ya aijye ta a gidan ,yace idan ya dawo da yamma zai biyo ya d'auke ta. Hajiya zaliha tayi murna sosai da ganin Haajar. Haajar tace "ya naga duk kin rame lafiya kuwa?" Hajiya zaliha tace "ina fa lafiya ,tun bayan biki nake nan banda lafiya" Haajar tace "ya salama! Ko ince ,amma wllh banda labari kuma Abbu sameer na zuwa gidan mu amma ban ji a bakin shi ba" Hajiya zaliha tace "aikin San halin shi ko yasan Abu indai ba tambayar shi kayi ba ,ba lallai ya fad'i ba." Haajar tace "to amma meyake damun ki haka? Kin rame sosai, Kodai ta samu ne?" Haajar ta fad'a cike da tsokana. Hajiya zaliha tace "kedai bari. Shi d'in ne fa, sai wahalar dani yake yi". Murna sosai Haajar tayi tare da yiwa Allah hamdala. Tace " Ashe dai biki bai qare mana ba? Kai amma naji dad'i sosai. Allah ya raba lafiya, ya bada rayayye ko rayayye mai albarka". Hajiya zaliha ta amsa da "ameen". Kusan Haajar ce tayi mata aikin gidan ranar. Sun sha hira sosai ,sai yamma liqis an ma kusa kiran sallan magrib daddy yazo d'aukan ta. A mota take bashi labarin Hajiya zaliha nada juna biyu ,shima daddy yayi murna sosai kai kace Matar shi ce aka ce tana d'auke da cikin. Tsokanar Haajar ya shiga yi akan cewa suma ya kamata ace sun d'au harman na biyu. Haajar tace " haba dai! Dan Allah kayi hak'uri ranka ya dad'e. Su Hassan fa ko yaye su ban yi ba" daddy yace "to idan kuma Allah ya kawo kuma fa?" Haajar tace "wannan kuma ba yadda zan yi" yace "to Dan haka wannan ma ba yadda zaki yi da shi na jikin ki" zaro ido Haajar ta shiga yi tare da cewa "menene kuma a jikin nawa daddy?" Dariyar mugunta daddy ya mata tare da cewa "ciki mana" Haajar tace "na shiga uku. Dama ina da wani cikin bayan na cin tuwo ne?" Ganin duk yadda ta rud'e yasa daddy cewa "ke wasa nake miki fa ,duk kin bi kin wani firgice. Da akwai keda yake jikin ki ai zaki sani" ajiyar zuciya Haajar ta sauke tare da dafe k'irji tace "haba! Yanzu naji zance". Dariya daddy ya shiga yi mata. Nan suka saki zancen suka d'auko wani, a haka har suka k'arasa gida.

Bayan sati biyu da zuwan Haajar gidan Hajj jamil. Take cewa daddy tana so taje asibiti a duba ta. Daddy yace mata saboda me? Dan shi dai lafiya qalau ya ganta. Tace masa baccin da take yi ne yayi yawa ,ko da yaushe bacci kamar 'yar k'waya, se yawan kasala da take fama da shi. Daddy k'in yadda yayi aje asibitin ,haka ya dinga mata kwana-kwana ,har sai da cikin ya kai wata uku lokacin ya fara fitowa. A lokacin ba yadda Haajar ta iya amma kuma bata murna da cikin saboda a cewaf ta su Hassan ba suyi k'waren dahar zata yi musu qanne ba. Tunda Hajiya ta sani sai tace Haajar ta dinga basu nono so d'aya a rana ,dama ba wani damuwa sukayi da nonon ba sosai ,da haka har suka dena sha suka koma shan madara zallah. A b'angaren suxee ma tana can d'auke da ciki wata biyu. Murna a wurin su Haajar ba kama hannun yaro. Allah ya taimaki Haajar ko kafin watan haihuwar ta ya tsaya su Hassan sun iya tafiya suna gudun su ko ina ,ga yaran da jikin girma Dan idan ba an gaya maka cewar basu shekara biyu ba ba ganewa zaka yi ba, baki ne dai babu. Matar hajj jamil ce ta fara haihuwa ,ta samu mace ,murna a wurin daddy da hajj jamil abun sai Wanda ya gani. Daddy ne yayi komai na sha'anin suna, ranar suna yarinyar taci sunan Hajiyar daddy wato suwaiba ,ana mata laqani da Aslamiyya ,duk da shi hajj jamil suxee yayi wa kara ba Hajiya ba ,saboda qaunar da yake mata har yanzu babu abunda ya ragu. Kowa yaji dad'in karar da yiwa Hajiya ,Hajiya ma ta taka rawar gani sosai Dan ita aka yiwa takwara.

Da farko ma ta d'auka ko sunan mahaifiyar shi zai saka, da ta yi masa magana sai yake ce mata ,ba yada ra'ayin hakan ne kawai ,iyayen ma da ba sanin su yayi ba ,Dan an haife shi da kwana tara mahaifiyar shi ta rasu a wurin dangin ta ya taso ,shekarar shi biyu da wata shida kuma Allah ya yiwa mahaifin shi rasuwa ,a wurin kakannin shi ya taso ,bayan sun rasu ne ya dawo hannun kawun shi da zama. Kunga kuwa ina wata shaquwa? Hajiya ce take zuwa gidan hajj jamil tana yiwa Hajiya zaliha duk wani abunda ya kamata har bayan suna ,Dan Haajar kam tayi nauyi ,ranar suna ma dak'yar ta samu taje ,shima tana zaune wuri d'aya bata iya tab'uka komai ba. Wata d'aya da haihuwan Hajiya zaliha Haajar ita ma ta haihu inda aka sake samun 'yan biyu ,sai dai wannan karon duk mata ne. Ranar suna Hassana taci sunan mahaifiyar Haajar Halimatus sa'adiya ana mata laqani da Ummi ,hussaina kuma taci sunan Kubra ana mata laqani da Amna. Haajar tayi hakan ne saboda suxee. Dukda daddy bai so ba ,amma ta nuna masa bata yadda za'ayi ya k'yamaci Kubra Dan ko duk yadda yaki yaso jinin ta na yawo a jinin shi ,ga kuma 'ya'yan ta nan na ci gaba da rayuwa a doron duniya. Ba Dan yaso ba haka ya hak'ura, Dan Haajar ba dai iya magana cikin hikima ba ,Hajiya ma taji dad'in abunda Haajar tayi sosai ,suxee ko hadda kukan ta da taji an saka sunan mahaifiyar ta.

Cikin suxee ya girma ,wannan ne yasa aka tura mata auta Dan ta taya ta wasu aikace-aikacen ,tunda daddy yace kar ta dawo gida har sai Allah ya sauke ta lafiya...

Kwana arba'in da biyar tsakinin haihuwar Haajar. Suxee itama Allah ya sauke ta lafiya ya bata santalelen d'an ta namiji mai kama da Barr Kabir Sak kamar an tsaga kara. Ranar suna yaro yaci suna Mahmud. Kusan tare Haajar da suxee suka yi jego...

MUJE ZUWA 💃

TAKU HAR KULLUM
Chapter 50 · 0% Book details