Sashe 9
Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read
ce. Banda awara tana gyaran jiki da lalle tana kuma taba dinki. Amma ita Fatu kamar yadda suka fi kiranta da shi a gidan bata damu da ta koya ba. Kawancen su da Zainab ta fara tabawa saboda ganin ita Zainab din ta dage tana yi. To a wan nan rana itama ta ci kwalliyarta da kwancen da aka bata. Tana ta sauri ta biya ma Fatu su tafi tare. A barandar fita waje Momi ta hadu da ita. "Ina zaki je"? Ta tambayeta a wulakance. "Mh gidan party". Itama ta amsa mata a tsorace. "Idan kin tafi party uwar waye zata gyara gidan "? Shiru bata amsa mata ba. "Come on juya ki je ki tattare gidan nan kafin in hada miki gajiya". Kafin ma ta dire maganarta ta juya da sauri ta koma ciki. Kaf gidan nan sai da share kowanne daki ta goge ta kuma wanke ban dakinsa da falukan gidan. Ita kanta Baba Laure bata san Momi ta hana ta zuwa ba da kuwa ba za ta tafi a motar farko ba. To ita ta tsaya sai da ta yiwa sauran 'yan matan kwalliya san nan ta shirya. Bayan ta gama tattaro ciki ta dawo kicin shima ta gyara ko ina nasa san nan ta dumfari wanke wanke. Ta wanke plate da kofuna sama da dari biyar. Tun da farko tukwanen da akayi girki ta fara jikawa. Bayan ta goge plate da kofuna da kuma cokula ta maidasu ma zauninsu, sai ta dawo kan kuloli. Suma sun kai goma runduma runduma kamar za a sata a ciki. Haka ta wanke su ta kife. Ta dawo kan tukwane suma ta dirje su tas. Tun misali tara na dare tafara aikin nan har shabiyu saura kwata bata gama. Nan suka dawo suka tarar da ita tana kokarin share wajen da tayi wanke wanke. Suna shigowa suka ganta jakwane jakwane da ita sai Farisa ta tuntsire da dariya tana fadin "wu kallo ya bar wata yarinya. Mun je dinner mun more boyi boyi tana wanke wanke". Ita dai bata kula ta ba. Ganin ma zata takura mata data gama sai kawai ta dauki zanin baba laure dake rataye a igiya ta cire kayan jikinta ta shanya su ta lulluba da hijabinta tayi kwanciyarta a sito din kicin din. [8/6, 23:14] +234 814 948 5104: FINI A UBA👨👧👨👧IN FIKI A MIJI Page 10 BY HANNE ADO ABDULLAHI Washe garin biki aka kai amare. Bilki matar Sulaiman gidansu yana Ribado road. Yayin da anti Sakina ke karkasara. A tunanin Zainab raguwar yaran gidan zai sanya aiki ya ragar mata, amma ina sai ma kari data samu. Ga shi dai kowacce da mai aiki aka kaita, amma hakan bai sa sun rangwantawa Zainab ba. Kullum tana zaryar hanyar gidajensu. Daga baya ma Momi ta saka mata dokar idan gari ya waye ta yi kokari ta gama gyaran gidansu san nan ta wuce zuwa nasu gidajen ta zauna kar ta dawo sai biyar na yamma. Tayi kukan takaicin rasa karatun ta na islamiyya gashi sun shiga ajin sauka. Baba Laure ce ta kwantar mata da hankali akan tayi hakuri ta bi yadda aka sata. Allah yana tare da ita. Ta kuma karfafa mata gwuiwa da fadin idan ta dawo sai baba Maigadi ya dora mata. Allah cikin ikonsa sai ma kuma wani sauki ya billo mata. Ganin idan taje ma kusan kullum ta kan samu aunts din nata ba su tashi ba. Sai da daina zuwa sai ta tashi daga karatun safe wanda take tashi sha biyu. Daga nan sai ta hau dan sahu ta wuce karkasara. Za kuma tayi kokari duk abin da zatayi mata zata gama shi kafin karfe biyu. Tana yi azahar sai ta wuce gidan Bilki.Ita kuma idan tayi la'asar sai ta dawo gida ta fara hidimar abincin dare kafin masu gidan su dawo. Haka ta koma kullum tana hanya. Shi uncle Sulaiman da ya ke a kamfanin wani babban dan kasuwa yake aiki a matsayin accountant dinsa. Goma na safe ya ke fita ya dawo biyar na yamma. Da safe matar zata lallaba ta sama masa shayi da burodi. Amma abin mamaki idan ya dawo zai tarar da abinci mai rai da lafiya an ajiye na rana ga kuma na dare shima lafiyayye da shi. Bai kuma cika haduwa da ita a gidan ba. Saboda ranar jumma 'a ne kawai da yake dawowa zuwa masallaci ya kan hadu da ita. Shi kuwa mijin Sakina Kabir yana DPR. Shi ma dai bai san sirrin matarsa ba ya dauka ita ke zankado masa hadaddun delicious din da yake diba. Domin ko dakunan mazajensu sai ta zo zata gyara ta sa musu turaren wuta ta wanke bandakunan tas. Ga shi har injin wanki a saya musu amma sai dai ita ta hada wankin ta zuba masa ko kuma idan ta zo ta tafi da kayan gugarsu gida. Idan kuma an goge ta dawo dasu ta shirya kowanne a inda ya dace. Idan kuwa ba ita tayi ba, to kuwa sai dai kayan su zauna haka. 'Yan boko ne na karshe amma fa ba abinda suka iya a domestic responsibilities dinsu. Su kuwa sauran kannenta ko da sun kaiwa aunties nasu ziyara su tarar aiki kamar zai kasheta to ba abin da zasu kama mata da dashi. Haka nan ta zama kamar machine kullum cikin hidimar kannen mominta take. Gwanda ma anti Bilki ita da mijinta suna da kirki. Amma Anti Sakina ba abin da ta rage na wulakanci da kuma toxarta Zainab. Ga mijin nata wani irin wawa mai barin zance. Haka nan tana ji tana gani sauran 'yan ajinsu sukayi sauka banda ita. Saboda tana zuwa normal lesson amma karatun rana na mura'ja ar saukar bata zuwa saboda hidimar amare da ta hau kanta. Da suka samu ciki kuwa sai komai ya dada kacame mata. Hidimar ta karu mata. Hakan kuma bai sanya Momi ta rage mata hidimar gidansu ba. Dole tayi na safe ta kuma gyara gida. San nan ta tafi wajen su Sakina. Suna da masu aiki amma ba za su iya tsayawaa a kansu su yi abin da ya kamata ba. That is idan ma sun san abin da ya kamata su yi din su da kansu. Sai Zainab tazo. Anti Sakina ce ta fara haihuwa. Saboda haka kacokam Zainab ta koma gidan da zama. Saboda kusan kowa na gidansu a nan yake yini. Amma fa ba abin da suke yi sai dai zaman hira da kuma zan ci kaza zan sha kaza. Ita kuwa tayi ta fama da dafawa da kaiwa da kwashe kayan da aka yi smfsni da su. Wata rana tana tsaka da wankin toilet din Uncle KB ashe ya shigo gida bata sani ba. Hijabinta na rataye kan murfin kofa jikinta sanya da skirt da riga sun yi mata das a figure 8 dinta kawai taji an banko kofar tailet din. A tsorace ta juyo domin ganin waye. Tana ganin Kb ta dafe kirjinta cikin sakin ajiyar zuciya tace "wai uncle ka bani tsoro". Wani irin yawu ya hadiya makwat san nan yace "amma an dade ana boye kyawawan kaya a nan. Dama haka kike da kyau shine kike nade jikinki a wan nan yadi marar kyan gani. Bala'i gaskiya an zuba kyau a anan". Bata rai tayi ta sha kumu. A iya saninta babu wasa tsakaninsu tunda ita ba kanwar matarsa bace. Hannun ta mika zata jawo hijabinta yayi saurin dauke shi yana fadin "kin ci karya yarinya. Ai ba zan sake yarda ki rufe min wan nan blockbusyer din da na samu an yi realeasing dinsa a yau ba". Kamar zata yi kuka take masa magiyar ya bata hijabinta. Ya nade shi a hannunsa sai ma matarsa da ya shiga kira. "Sakina zo ki gani". Da sauri ta karaso inda suke. Ganin su a haka ya sa taji ranta ya baci saboda macece mai tsananin kishi. Ga mijin nata kuma da shegen son mata. Muryarsa ce ta katse ta yana fadin "taimaka min ki bani 'yarki in aura ni kuwa na yi miki alkawarin na daina zuwa ko ina daga wajenki sai nata". "Kaga Kb bana son irin wadan nan stuid jokes din naka". "You think iam jocking. Ai ba namiin da zai yi wasa a neman mace irin Zainab. Da gaske na ke yi miki. Kin ga kin huta da yawona ni kuma in huta da mitar ki na ina neman matan banza". "Ke get out of here kafin in babbalaki" ta fadawa Zainab cike da bacin rai. Da dan gudunta ta fito daga cikin taoilet tare da rakiyar wani uban fito da Kb ya saki, mai nuna alamun yabawa da abin da ya dada gani. Bai daddara ba ya sake mai da hankalinsa wajen matarsa yace "yaya do we have a deal? Kara min da ita ni kuma na miki alkawarin na daina yawo". Bata bashi amsa ba sai ma fizge hijabin da ta yi daga hannunsa ta fita a fusace. A kicin ta samu Zainab tana tsaye cike da rudani ta wurga mata hijabin ta. "Don ubanki kama hanya ki bar min gida kafin in canza miki halitta yanzu yanzun nan". Jiki na bari ta karba ta saka ba tare da tace komai ba. A kafa ta taka tun daga karkasara har NNDC quarters na Hotoro inda gidansu yake.