← Book details Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 43

Sashe 19

Fini A Uba In Fiki A Miji Complete Hausa Novel · about 8 min read

ci ta duba taga saura dubu biyar da dari shida. Saboda dama tun da ta duba taga lissafin kudin sai ta daukarwa kanta, da safe ta sha ruwan bunu. Da rana ta ci a gidan su Fatu ko kuma ta karbi tuwon BabaLaure. Da daddare kuwa sai ta ci bread na sittin ta sha ruwa. Balle kuma dama ita gwanar azumin litinin da alhamis ce. Idan tayi bude baki sai ta sayo indomie super pack guda daya. Taci da magariba, sai ta rage kadan tayi sahur ta sha bakin shayi. Shike nan. Saboda ta fitar da shi kunya tayi abin da samari kance ‘a wajen gayu da girma ya fadi gara jari ya karye’. Itama haka tayi kuddumus mutuwar kazar kuku, ta dauki kudin nan. Ta sayo kazar ta guda daya ta dubu daya. Ta sayo mince meat rabin kilo da flour rabin kwano da kuma sauran kayan meatpie da samosa. Ta sayo lemon bawo na dari uku, sai man gyada rabin kwalba. Sai da ta kashe dubu uku da dari takwas. Ta duba taga abin da yai saura mata baifi dubu daya da dan wani abu ba. Amma a yau ba abin da ya dameta irin ta farantawa Al Bashir rai. Ta zauna ta murza meatpie.ga shi kwaben yayi kyau, sai da ta samu guda goma sha hudu. Samosa guda ashirin. Da ta ga man ba zai ishe ta suya ba. Sai ta gasa meatpie din a murhun gawayi saboda dan guntun gas din dake gidan kwanan su Momi biyar da tafiya ya kare. Itama kazar tayi musu gashi mai kyau da kuma dadi. Lemon kuwa barewa tayi ta nika ablender ta mai da shi juice. Kafin la’asar ta kammala komai. Ta samu plates masu kyau ta saka a ciki. Kazar kuma ta zuba aflask. Ta samu jug mai kyau ta zuba lemon. San nan ta debo ruwan sha a dispenser gidan ta sa a wani jug din. Komai dai can a can. Balle dake ta samu sake ba wanda zai hana ta daukar komai. Ta share verender bakin falon babansu. Ta dauko carpet ta shimfida. Bayan ta idar da sallar la’asar ta rangada wanka. Acikin kayan da Farida ta bata wadanda ta gyara, ta dauko riga da skirt na wani cotton lace mai kyau ta saka. Kayan suka yi mata cif kamar dama daidai jikinta aka dinka. Ita kanta ta yaba da kyan da tayi.san nan tabi jikinta ta feshe da turare. Tana jinkiran wayarsa ta yi murmushi ta saka hijabinta mai hannu ta nufi waje. Su hudu ta gani, har da shi. Har kasa ta durkusa yadda ta saba gaishe shi haka tayi musu. Suma cikin fara’a suka amsa mata. Tayi musu jagora har bakin falon. Sai da suka zauna ita kuma ta shiga cikin gida domin hado dan entertaimaent din da tayi musu. “where did you find this clean item” ? daya daga cikin su ya tambaya. “kyauta daga Allah” in ji AlBashir. “Amma fa mun wahala. “inji Mujib. “can you imagine we had to spend the whole day a kasuwar gwanjo. Ai I promise duk sai na kai ku kun ga wajen. It was just awful”. “For such classy babe I can spend ten years in prison”. Shi ma dayan ya fada. “Ina ga gwara in sallame ku, ba wani amfani da zaku yi mun anan” Al Bashir ya fada. Gaba daya dariya suka saka ganin kishinsa kiri kiri. Dayan zai bashi amsa Zainab ta fito hannunta dauke da katon tray. Shi ya tashi da hanzari ya karbeta yana fadin “putri salju ba sai ki kirani in dauka ba”. Ba ta bashi amsa ba sai dan murmushi da tayi. Sai da ta zuba musu ruwa da lemo kowanne san na aka sake sabuwar gaisuwa. Ya kuma nuna mata abokansa tare da introducing dinsu. Ya nuna na kusa da shi yace “wan nan shine Mustapah,ga kuma Sa’ad. Sai kuma”. Ta katse shi da fadin da cewa “ai shi na gane shi. Ba Ya Mujib bane”? “shine ashe kin gane shi”? Ba tayi Magana ba sai murmushi da ta dada yi. Mustapah na gutsirar meatpie yaji wani irin dadi ya ratsa shi. Bai sanda yace "Amma dai wan nan daga Madina aka kawo shi ko”? Gaba daya suka tuntsire da dariya. Ita dai bata shiga cikin zancen zolayar da sukewa junansu ba. Sun taba hira kadan duk da dai ita bata cika sa musu baki ba. Balle lokuta da dama da turanci suke Magana. Duk da bata ji duka ba, amma tana fahimtar wasu zantukan nasu. Da ace tana da exposure, to da kuwa ta lura da yanayi jikinsu da kuma suturar da ke sanye a jikinsu da ta gane masu kudi ne na gaske. Amma bata da wan nan ilmin. Sai da sukaci suka koshi domin kuwa sun cinye kusan komai data kawo musu. Mustapha ne ya sanya hannu a aljihunsa da niyyar debo kudi. Idon Al Bashir kir a kan aljihunsa ya ganshi yana kokarin zaro dollars daga aljihunsa. Da sauri yace “chill bro. the case is low profile”. “but the object is classy and worth it. It is supposed to be a high profile case”. Inji Sa’ad. “forget it it’s a long story. Thats why we had to spend a day at bend down and pick boutique”. Duk iya kokarinta bata fahimci zancensu ba. Ta dai dauki sabbin kalmomi a kanta da niyyar idan sun kebe ta tambaye shi fassararrsu. Ita tana tunaninta su kuma suka ci gaba da tattauna maganganansu. “amma duk da haka we cant leave with out giving any percuma for her” “Yeh a I agree but make it kacik”. Sa’ad ne ya ciro dubu goma daga aljihunsa ya ajiye mata. Suka mike tare da yi mata sallama.shima ya mike domin rakasu. “Putri ina zuwa”. Tare suka fita. Sai da sukaje yaga wata katuwar thundra a fake a kofar gidan kusa da mashin dinsa. Yace dasu. “Amma you guys almost flop my plan. Data fito ta gan ku da wan nan motar fa. Me zaku ce “? “very simple sai ince ni driver ne a wani gida na dauko motar gidan na fito raka abokina zance.” Mustafa ya amsa musu. Dariya suka saka duk kansu. Sai da suka shiga zasu tafi Sa’ad ya leko yace “When you are done, call us so that we can come and pick you”. “kar ku damu. Sai na dawo I will call you back”. Inda ya tafi anan ya tarar da ita zaune a gefen verender. Shima gefenta ya zauna a gefen carpet din da ta shimfida. Suna hada ido dukkansu murmushi ya subuce a fuskarsu. Shi yasa hannu inda kudin suke ajiye ya dauko yace “ga sakonki, ko kin bani”. “da kai kaya duk mallakar wuya ne”. “Kin san me ina jin dadin duk sanda kika nuna min I have right over you dadi nake ji”. “Ni kuma yin hakan shine babban burina a rayuwa”. Zai yi magana tace me ake nufi da profile. Na san dai high sama ke nan. Amma ban san fassarar case da profile ba”. A dan firgice ya juya ya kalleta. Amma sai ya dake yace “forget it. Amma a ina kika sayo snacks din nan ba karamin dadi suka yi ba. Kina ganin mun yi abin kunya, sude kwano a gidan surukai harda tauna kashi”. “Na ji dadi da kunyi enjoying abin da na kawo muku. Amma ai snacks a gidan nan ake yinsu, saboda Momi tana na sayarwa. Kusan kullum sai nayi”. “amma naga bata nan” ya fada cikin dan bacin rai”. “Eh ai ko bata nan ana placing order kuma tun da dama ni nake yi, duk da haka anayi tun da dama……” sai kuma ta kasa karasa abin data fara fada. “Tun da dama ke kike yi. Ke ba kya gajiya ne na lura kullum cikin hidima kike”. “Lah a ai bashi da wuya. Don dai in yi samosa da spring rolls guda five hundred kowanne in a day”. Bai ce mata komai, saboda ji yake ransa na suya. Ita ‘ya’yanta na karatu ta maida ta wata baiwa. Bai dai ce komai ba, sai ma kudin ta da ya mika mata. Fir taki karba, sai da ya nace san nan ta zari guda biyu daga ciki, san nan tace “rike sauran a wajenka”. “Kyauta ko ajiya” “kayan Allah ai na Annabi ne ko kuwa”. “naji na yarda,amma please ki karbi kudin nan”. “kayi hakuri ba na son in na maka musu, amma ka taimaka ka ajiye su a wajenka. Washe gari kuwa wani mutum yazo akan yana sallama da ita. Bayan sun gaisa ya fada mata cewa maigidansa ne ya aiko shi sayen snacks a wajenta. Da sauri ta gaya masa kudin ko wane. Tana jin sa yabuga waya yake fada. Bayan yayi sallama ya ajiye ya juya wajenta yace “maigida yace shi ga yadda yake saye kuma haka zai saya amma in har zaki sayar”. Tayi mamakin price din da ya ambata saboda abin da zai saya sai da ya ninka kudin kowanne sau uku. Baba Laure ce ta sanya ta ta karba. Ta kuma nuna mata tayi wan nan order kanta ce bata Momi ba. Tun daga ranar kuwa kusan kullum za a zo sayen snack. Kuma kullum tayi ciniki bata samun kasa da ribar dubu ashirin. Ita dai bata san me saye ba. Sai dai saboda kudin da ya kara sai ta kara masa girma da kuma yawan fillings din ciki. Amma duk da haka kudi take caska ba na wasa ba. Sai ta shiga tarasu a wajen mama Hajjo saboda saukar da take burin yi wan nan shekarar. Da kuma tunanin saka kanta a LEGal kamar yadda kawarta tayi. Haka zalika tana burin idan sun yi aure sai ta taimakawa Bala ya kara jari. Shi kuwa Bala mai gwanjo /AL Bashir, shi ke dibga mata wan nan ciniki ba tare da sanin ta ba. Kuma da yazo bata boye masa komai ba na sabon customer da tayi da kuma cinikin da yayi mata. Shi kuwa a bangarensa, idan ya sayi snacks ya kan kaiwa Ummansa da kuma sisters din shi. Kuma ko bai saya ya kai musu ba zasu tambaya, saboda a cewarsu ba su taba cin mai dadin wanda yake sayowa ba. Shi dai bai sanar da su daga ina
Chapter 19 · 0% Book details